*RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA. (Mrs j moon)*35*
Koda ta sauko tuni yabar parlorn. wani sanyi takeji yana sauka mata cikin heart ta runtse idanunta ta daka tsalle ta soma rawa tana d'iban shoky tana juyi cike da nishad'i tana wak'an soyyaya-soyayya.
Sautin dariyan Ummi taji abayanta yasa tayi saurin dakatawa da rawar ta juyo cike dajin kunya sai kuma ta diba da dugu zata fice.
"Auta zo ki tafi mishi da wani abu mana."
Juyowa tayi kanta k'asa ta shige kitchen, tana jera drinks tare da snacks tajiyo Ummi na fad'in "Oh Auta dai k'arfi da yaji taki yaron nan Ubaiyyu, to Allah yasa haka shi ne mafi Alkhairi."
Can k'asa ta amsa"Amin." Sai kuma ta rufe fuska wai taji kunya. Fitowa tayi kanta sunkuye taki kallon inda Ummi take, rankwashi Ummin ta kai mata tana cewa "Kunyar k'arya ba, bacin yanzu kika gama cashewarki har da d'iban shoky hankali kwance."
Da sauri tafice tana dariya itama Ummin dariyan tasa tana furta "Auta hoo ita dai abinjin kunya bayayi mata wuya sam."
'Dauke da sallama ta shiga sitting room d'in, ya amsa mata can k'asa cike da k'asauta. Ta karaso ta d'ora kayan saman table ta tsiyaya mishi mango juice with apple data had'a da hannunta, ta mik'a masa mai makon ya amsa sai ya damk'e hannunta yana son su had'a idanu ita kuma ganin haka ta kara sunkuyar da kai k'asa murmushi ya saki mai sauti ya ce "Kinsan Allah idan har baki d'ago kin kalleni ba sai dai mu kwana a nan."
Tak'i motsawa ya matse hannun da k'arfi ta ritse idanu, lemun dake rik'e hannunta yasoma zubewa sabida rawar da hannunta yasomayi. Jan hannun nata yayi zuwa bakinshi ya kafa kai yana tsotsan juice d'in eyes nasa a kanta, tana jinsa duk abinda yakeyi amma tak'i d'ago kai ta kalleshi haka ta kasa janye hannunta.
Sai da ya shanye tas sannan ya saketa ya koma ya lafe cikin Cushing yana tsotsan lips cike da nishad'i ya ce "Oya Hajiya Rabi'atu sami wuri ki zauna kada k'afafunki yayi tsami."
Mikewa tayi ta zauna nesa dashi still kanta a k'asa tana wasa da bungles dake sanye a hannu ta.
"Uhmm sarkin jin kunya sai kisaki jikinki hakan ko maji dad'in yin hiran yaushe gamo duk da nasan yanzu batani kikeyi ba kinsami handsome d'an balarabawa ya sace miki zuciya."
Da sauri ta d'ago idanu waje ta ce "nji wa?."
"Inji ki."
Ta langabe kai cike da marairaita ta ce "Kai Yaya Ali yaushe mukayi haka da kai?"
Shima langabe kan yayi ya amsa "Ranar da kuka dawo daga saudi a airport kika tabbatarmin da bana gabanki sam yanzu."
"Uhmm Yaya Haydar kenan baka rabo da zolaya."
"Allah ba zolayanki nakeyi ba Rabi'a, ke da kanki kika nunawa duniya bakya yayina tunda ko darajan kallon arziki ban samuba ba daga gareki." Ya karasa zance cikin dacin rai.
Tuni idanunta ya kawo ruwa ta dawo gabanshi ta zauna ta soma magana "Wallahi Allah Yaya Ali abinda kake tunani akai ba haka ba ne kawai kunyar yima magana naji agaban su Abbie amma sosai ranar naji dad'in ganinka."
Ya amsa adak'ile "Uhm naji."
Kallonshi tayi sosai ta ce "Don Allah kayarda dani ba wanda ya sace maka heart d'in Rabi'a, wallahi zuciyar taka ce har abada bata taba son waniba sai kai kuma bazata k'ara son wani ba bayan kai, kayafe min dan girman Allah kaji my life."
Murmushi ya kufce mishi ba shiri ya jijjiga kai ya amsa "Komi ya wuce sweetie. Nima naki ne har a rayuwar k'iyama."
"Thank you habibi. Allah ya amsa.
YOU ARE READING
RABI'ARUL ADDAWIYYA.
PoetryZumunci ne mai ban al'ajabi tsakanin jinsin mutum da Aljan wanda ya rabe tsakanin musulmai da kafiransu.