page 17~18.

868 71 0
                                    

*RABI'ATUL ADDAWIYYA*

*17~18*

Malam Yusuf shine cikakken sunar Abbi? Haifaffen garin Jangab'a ne dake jihar Niger. Mahaifiyarsa tare da k'anninsa uku biyu maza d'aya mace wutane ta yi ajalinsu lokacin shi yana can cikin garken shanu yana gad'insu, wutan ta tashi kokafin akawo agaji wutar ta lashesu sanadin haka Mahaifinshi yakamu da ciwon zuciya shima bai jimaba yace ga garinku nan sakamakon haka sai yataso maraya.

 Ga dukiya da shanu sunbar mishi sosai amma Baffaninsa sukace nasune Mahaifin nasa ke yi musu kiwo kuma bawanda ya musanta hakan a garin sabida haka suka k'wace komi su bar mishi wata tsohuwar saniya wai ladan kiwon da ya yi. Ya sha kuka har yagode Allah kawunshi yayan mahaifiyarshi daya rage mishi shi ne yayi tabashi baki ya nuna mishi wuta sukaci kuma da yardan Allah bazai amfanesu ba.

Haka nan yacigaba da rayuwanshi a gidan kawunshi ya kuma jefa karsanan shi cikin garken kawun duk da shima shanun nasa basu da yawa domin basufi bakwai ba.

Bayan shekaa saiga sanuwa ta haifi 'yan maruk'qa biyu suna isa yaye suka saida uwar suka bar 'ya'yan sabida ta tsufa.
suka sayo wasu mata biyu suma shekara na kewayowa suka haihu 'yan bibiyu.

A bufa yayi albarka sai gashi a cikin' 'yan shekaru shanun Yusufa suntasarma kusan ashirin banda tumaki da raguna ga kaji tare da zabbi.

Ganin haka sai yacewa kawunshi zai shiga duniya neman ilimi sabida ilimi Addin yayi qaranci sosai ayankinsu, bai hanashi ba saima  addu'a daya bishi dashi.

Ya soma isa garin kwantagora a inda yahad'u da wani matashi mai suna Abubakar ya taimakeshi ganin yana tare da k'auyenci, ya kaishi gidansu ya kwana washe gari ya kaishi tasha ya sashi amotar garin Zaria birnin ilimi sabida yasanar mishi cewa ilimin addini yafito nema shine yaga ba inda zai samu mai nagarta irin birnin zazzau.

Ya iso garin Zaria daf da la'asariyya, ranar ya nemi gidan shehin malamin dazai soma karatu, wani mutum yayi mishi jagora zuwa gidan lamamin mai suna Alhaji malam Haruna mai riguna. yanemi iso atake kuma akayi maraba dashi domin gidane na karamci da nagarta, kowa nasune domin irin adalcin mai gidan, yasa ake karrama bak'o kodaga ina yazo sabida yakance shima zuwa yayi gashi har yazama wani abin wanda har ake zuwa wurinshi samun ilmomi.

Anan yusufa yasamu karatun AL-QUR'ANI dawasu littafai na addina sai yakoma gida amma akwantagora ya sauka.
Abokin shi Abubakar yayi ta mamakin ilimin da yasamo.
Washe gari yayi misu bankwana ya nufo qauyensu kafin ya shiga mota yaji wani yana bawa abokinshi labarin ya kosa yakoma kano yacigaba da sana'arshi.
Sai yayi tsam da ranshi atake kuma yaji bazai koma garinsu baida komi ahannumshi ba sai kawai yanufi wurin saurayin nan yayi masa sallama ya fad'a mishi intafiya zaiyi to zai bishi, atake saurayin mai suna gambo ya amince suka shiga motan kano.

Ya shigo garin kano da k'afar dama sabida a sheratu 2 yasami alkhairi mai tarin yawa, fad'i yake lallai garin kano tacika tumbin giwa.

Sai ya shirya yayiwa abokinshi Gambo bankwana ya nufo gida.

Koda kawu ya ganshi bai ganeshi ba sabida yazama magidanci sosai mai tarin natsuwa daka ganshi kaga cikakken mai ilimi, gashi dama farine sai farin yakuma k'aruwa.

Shikuma yayi mamakin irin shanun da kawu yanuna mishi yake nashine domin sunkai garke biyu banda tumakai da kaji tare da zabbi ga kuma kud'in kwan zabbin da yake saidawa insumyi sai ya ajiye mishi, ya tara mishi kud'i masu yawa.

Take yaraba komi biyu yabawa kawu kyauta, dakyar kawun ya amsa, saida yayi tayi mishi magiya sannan ya amsa.

Dangin mahaifinshi hankakinsu yatashi dasuka ganshi da wannan dukiya sabida nasu dasukaci zalin duk sun kare basu ka komi sai wahala, sai suka nemi da ya auri y'a'yansu yanuna shi baitashi yin aure yanzu ba.

RABI'ARUL ADDAWIYYA.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang