BABI NA 'DAYA

1.8K 42 1
                                        

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA,MAI JIN KAI...

Dukkanin godiya ta tabbatar ga Allah(SWA) da ya nufe ni da fara rubuta wannan labarin,ina aduan yadda ya bani ikon fara shi lfy ya sa na gama lfy,tare da isar saƙon da nake son isar wa.

JAWABIN MARUBUCIYA
This is my first novel,ina rokon don Allah duk in da aka yi katari da wani kuskure da nayi ayi ƙokarin sanar da ni tare da min uzuri.

Wannan labari ƙirƙirarrare ne,duk wani suna ko halayya da za a gani ban yi domin na ci zarafin kowa ba sai domin isar da sakon da ke cikin sa.

Daga ƙarshe,zan kara nuna godiya ta ga duk wanda ya ke karanta wannan littafin nan mai suna ƘADDARA TA domin abin alfahari ne a gare ni na ganin yadda kuke bibiyan labarin.

GARGADI
Piracy is not allowed,immediate action will be taken if caught

JAN KUNNE
Ina so nayi gargad'i ,wannan littafin jigon sa ya ginu ne a kan SOYAYYA,da haka nake cewa duk wanda zai karanta littafinan,ya san cewa akwai MATURE CONTENTS, ina da yaƙinin duk wanda zai karanta ba yaro bane,da haka nake roko,dan Allah wanda ya san shekararunsa ba su kai na karanta irin wadannan abubuwan ba,toh don Allah kar a karanta

Read at your own risks

Mallakar
HAFSAH BEE
(UmmuAfreen)

****FARKO****
KADUNA
UNGUWAR DOSA
LEGISLATIVE QUARTERS
3:pm
July,2017

••••••••••
Kwance take tayi matashi da cinyar Momyn ta ranan wata lahadi misalin karfe uku na yamma,a falon su mai matukar girma da daukar ido.A gefe guda kuma wani tafkeken talbijin ne kaman a cinema ke ta faman aiki kamar mutanen ciki za su fito waje.

Kara lafewa tayi jikin yar farar ƙyaƙƙyawar dattijuwar  matar da yanayin hutu da jindadi suka kara boye shekarun ta wuce baxata wuce 45 to 46 years ba,kokarin gyara mata gashin kan ta mai tsawo da cika take da man gashi tare mitar yadda take barin gashin babu kitso

Ɗan turbune fuskar ta yi jin momyn ta dage sai famar mita take yi na rashin kitson da bata yi,ita kuwa in akwai abinda ta tsana toh kitso na daya daga ciki,ita kuma momyn na sha'awar ganin kitso a kan ta,a cewar ta kitso na kara fiddo da kyawun mace.

Ɗago da kan ta tayi ta kalle momyn a shagwaɓe ta ce

"Kai momy ni fah ba na son yin kitso ne na fison na bar gashi
na haka,saboda in nayi sai na yini ciwon kai daga baya kuma kitson ya zo kunce sbd santsin gashi na"

Jin abinda tace ne yasa Hajia Nafisa ta ce
"Sam wannan ba wata hujja bace da zaki ce kin daina kitso kwata-kwata ai gwara ma ki yi din da baki yin ba,amma na san maganin ki daga yau ni zan koma yi miki kitson,ai na iya rashin zama ne yake hanani yi miki amma zan rika kokari ina yi miki in ga ta tsiya"ta karashe fada tana tufke kan ta da tagama gyare shi tsaf sai sheƙi yake yi

Tashi tayi daga ƙwancen da take tana shafa kan tare da faɗin

"Allah kuwa Momy ba bazaki gane bane kitso fa akwai zafi ga wahalar zamn sa"Ta karashe maganan a shagwabe

Momy da ke duban ta da takaicin ta ne ta ce

"Ai dama bazan gane ba tunda ƙyuya da som jiki ke damun ki bakomai ba"

Wasu ƙwalla ne taji suna taruwa a idanun ta ganin yadda momyn takasa fahimtar ta yasata fadin

ƘADDARA TA Where stories live. Discover now