Charpter 1

3.2K 99 5
                                    

💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓




®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*Story and Writing by:*
'''Aysher Aliyu Humaira (INNARO)'''

*Dedicated to:*
'''Zainab Ahmad Shareef'''
           &
'''Hafsat Abbas Babi'''


~🗓october 2019~

'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''


*Page 1↔5*

Yarinya ce ƴar kimanin shekara goma Sha biyu na hango tana sanya da uniform,tana sawa tana jan tsaki har tagama sa uniform ɗinta kalar ruwan siminti da hijab fari bakin guiwa kayan sun mata kyau bakaɗan ba.

Tafito daga bed room zuwa falon wata mata dake zaune a bisa kujerar robber wadda shekarunta ba zasu haura arba'in ba.

Tace, "Ammina na shirya ina Yaya?"

Ammi tace, "ai kinsan halinsa baya wargi da baccin safe dan haka sai kije yana ɗakinshi kitada Shi"

ta turo Baki a gaba kamin tace, "Ammina baki tuna mashi bane yau zanfara zuwa school ba"

tace, "nafaɗamasa Mana mai yuwa ya manta ne Amma je kigani koya tashi"

ta wuce Tana ƴan ƙunƙuni, koda taje bakin ƙofar dakinshi taji kamar alamun ruwa a toilet Sai ta juyo tace,

"Ammina Yama tashi Yana wurin wanka"

tace da ita, "toxo ki karya kamin yafito kinsan halinsa bayason jira karyaxo yahanaki karyawa"

tace, "to Ammina"

ta wuce kitchen ta ɗauko kunun gyaɗa wanda yasha Madara tare da ƙosai tadawo falo ta zauna a bisa kujerar robber kusada Amminta tace,

"Ammina Abii bai tashi bane gashi har zan wuce makaranta?"

tace, "eh baitashi ba tukunna"

daga haka Bata ƙara cewa komai ba tafara Shan kununta.

Tana Fara Sha Yayanta Yana shigowa tai maza ta aje ta taso da gudu ta rungumeshi Tana turo Baki gaba.

Yace, "waya taɓaman LilSis ɗina?"

tace, "ba kaibane yaune zanfara zuwa school amma kaƙi zuwa ka kaini da wuri"

yace, "to suda uwar dumi yanzu saiki sa kaina yayi ciwo, tinda gani nazo ɗauko jakarki mutafi"

Ya juya wurin Ammi ya gaida ita ta amsa cikin fara'a yace,

" Ammi Abii ya Baki takardunta?"

tace, "eh sunanan kan mirror kaje ɗauka"

yace, "tau"

yaje ya ɗauko suka fito a tare tana rataye da jakar makaranta tace,

"Ammina natafi Sai mundawo"

"to Allah ya tsare ayi karatu banda wasa da kula ƙawayen banza"

tace, " to Ammi idan Abiina yatashi Ina gaida shi....."

bata ida zancen ba taji Yayanta na Ƙawalama ta Kira,

"Muwaffaqa kifito mutafi ko natafiyata inada wurin zuwa"

tace, "gani nan Yaya"

ta fita da sauri ta hau mashin yaja suka tafi.


_plsss share,comment and vote._


*INNARO*✍

AISHATUL-MUWAFAQAWhere stories live. Discover now