Chapter 2

960 36 2
                                    

💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*Story and Writing by:*
'''Aysher Aliyu Humaira (INNARO)'''

*Dedicated to:*
'''Zainab Ahmad Shareef'''
           &
'''Hafsat Abbas Babi'''

~🗓october 2019~

'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''

*Page 6↔10*

*__________📖* bakin wani gate da aka rubuta Govt. Girls Day Arabic secondary School sabon birni area sokoto akan wani Allo dake kusa da gate ɗin.

nan sun shiga suna shiga yai parking ta sauko Shima ya sauko Sai ga wani malami yazo wucewa yabashi hannu suka gaisa yace,

"sunana Muhaisin Abdulmumin Umar, ƙanwata na kawo"

Malamin yace, "ok muje na nunamaka office ɗin principal"

yace, "yauwa nagode"

yace, "ba damuwa muje"

suna gaba Muwafaqa na biye dasu har office ɗin principal.

Da sallamarsu suka shiga wata matace zaune a bisa kujera wadda aƙalla shekarunta sun kai hamsin, Sai wani dake zaune abisa kujerar da aka tanada domin masu zuwa, gefe Kuma wasu ɗalibaine su biyu da irin uniform ɗin Muwafaqa.

kusa da ɗaliban taje tai tsaye shikuma Ya Muhaisin ya zauna a kujerar dake facing ɗin wannan mutumin a bisa umarnin principal.

ya miƙa ma mutumin hannu suka gaisa ya gaida principal Muwafaqa ma ta gaidasu.

Muhaisin yace, "wannan ƙanwatace na kawo"

principal tace, " ok bara nagama da wannan"

Sai mutumin yace, "toni zan tafi"

tace," ok Sai munyi waya"

da alama dai ƙaninta ne.
Bayan wannan mutumin ya fice Sai tadawo ga Ya Muhaisin tace,

" inajinka a wace makaranta ta gama?"

ya Miƙa mata takardun da yazo dasu tare da cewa,

" a Islamic collage"

nan dai yamata bayani akayi cike-ciken takardu aka gama tace da Muwafaqa,

"zauna Nan tare da ƴan'uwanki kamin Mallam Abba yazo akai ku class"

"to" ta nemi wuri ta zauna Ya Muhaisin ya miƙe zai fita ya miƙo mata naira ɗari yace,

"ƙarfe nawa ake tashi?"

principal tace, "ƙarfe biyu saura kwata"

yace, "ok" ya wuce Muwafaqa ta bishi abaya yace,

"koma Sai naxo ɗaukarki"

ta koma ciki Shi Kuma yaja mashin yayi gaba.

data koma ta xauna a kusada yaran da bazasufi sa,anninta ba.

Ɗaya tace, "ya sunanki?"

tace, "sunana Aisha Abdulmumin Umar  amma Muwaffaqa akece min"

tace, " wow nice name"

ita kuma tace, " kufa?"

ɗayar tace, "sunan mu ɗaya"

tace, " haba dai ?"

tace, "Allah dagaske nake sunana Aisha Bello Aliyu amma ana cemin Bakariya"

tayi murmushin kan tace, "nice to meet you my name-sake"

tace "mee too"

ta dubi ɗayar tace,
" ke kumafa?"

tace, "sunana Zainab El_mustafah"

Sai Bakariya tace, "Allah kasa a haɗemu a class guda"

mukace, "ameen"

Saiga wani malami ya shigo suka gaisa da principal tace,

"yawwa Malam Abba kaga new student fa ankawo"

yace, " ba akaisu class ɗin Malama Balki ba kuwa?"

tace, "a'a Dan Allah dai ka kaisu class ɗinka"

Tamiƙa Masa sunayen su tare da admission no.

Ya karɓa yace,

"ku biyoni"

suka tashi suka bishi.



_plsss share,comment and vote._

*INNARO*✍

AISHATUL-MUWAFAQATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang