💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*Story and Writing by:*
'''Aysher Aliyu Humaira (INNARO)'''*Dedicated to:*
'''Zainab Ahmad Shareef'''
&
'''Hafsat Abbas Babi'''~🗓october 2019~
'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''
*Page 21↔25*
__________📖Jawo littafan yayi ya fara making kenan, ganin ɗalibai na fitowa daga class alamun an fito break.
Muwafak'a ce ta tashi daga inda take taje wajen Malamin tace masa.
"Malam za muje muyi break".
Be d'ago ya kalleta ba yace mata. "ban baku izinin tafiya ba".
Bata ce masa komai ba, suka cigaba da zama har ya kusa gama marking din book, wani book ya d'ago yace.
"Wacece Aisha Abdulmumin Umar?".
Muwafak'a tace, "Malam nice".
Bai ce komai ba ya fitar da littafin gefe ya cigaba da marking d'in sauran.
Yana gamawa ya mikoma su.
"Malam nawa fa?".
Ita ce tambayar data masa
Kallonta yayi yace. "Kije sai na neme ki".
Mik'ewa sukayi a tare suka fara tafiya.
Muwafak'a ce tace ma Bakareeya.
"Allah Malamin nan ya raina ni da yawa duka-duka fa yau nafara ganin sa,amman bakomai bai sanni bane".Bakariya ce tayi dariya tace.
"Lallai Muwaffaƙa kince wani Abu".
daga haka ba wanda ya k'ara magana a cikin su har suka Isa class.
Duk ba kowa, inba wasu 'yan mata biyu ba suka gaisa suka tambayi sunan su d'ayar tace.
"Sunan ta Safinat Bello Junaidu".
dayar kuma tace. "Sunanta Asma'u Maneer".
Bakareeya tace, "Kuma yau aka kawo ku?".
Amsa suka bada da cewa a'ah sune first a class din nan.
Muwafak'a tace. "A kuce kun san gari kenan, ko zaku rakamu musiyo abin break tunda mu bamu san wuri ba?".
Mik'ewa sukayi suka ce.
"Mi zai hana".
Suka jero a tare suna tafiya suna fira har suka kawo wurin wani malami suka duk'ƙa suka ce.
"Baba Ina kwana".
Ya amsa musu da. "lafiya ƙalau".
Suka wuce Muwafaƙa tace.
"Naji kunce Baba hala Baban ku ne?".
"Aa suka ce mata, sannan suka cigaba da maganar ai duk malaman makarantar nan Baba ake ce musu".