Charpter 8

487 22 0
                                    

💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓
*1441H/2019M*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*STORY AND WRITING:*
*AYSHER AlIYU *HUMAIRA(INNARO)*

*Dedicated to:*
*ZAINAB AHMAD SHAREEF*
           &
*HAFSAT ABBAS BABI*

~🗓December~

'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''

*Page 36↔40*

_____________📖Daga Ɗayan 'bangaren aka ce, "hello Assalamu Alaikum".  Wani ihu Muwaffak'a ta saka tace.




"Ya Ammar ashe baka manta dani ba, shine ko ka kirana ka daina  bari nayi maka fushi".

Gargiza Kansas yayi  yace.




"haba lil sis taya za'ayi na manta da ƙanwata, ai idan na manta dake tamkar na manta da kaina ne" .




Tace "I miss you so much Yaya Ammar".

yace.

"Miss you too ƙanwata".

tace "yaya Ammar na fara zuwa school fa yau".

Magana ya k'ara yi mata da cewa.




"Masha Allah  sweet ƙanwa sai ki mayar da hankali da karatu kinsan dai likita nake so kiza ma ko?".



Kuma  nasan halinki da tara ƙawaye Dan Allah a rage tara su  kinga pramry da secondary ba ɗai ba".





Murmushi tayi tace.

"Insha Allah yaya Ammar zan mayar da hankali,sosai naga na zama abinda make so".



"haka nake so ƙanwata idan har na samu labarin kin mayar da hankali akan karatun ki zan siya maki wani abu, amma  bazan faɗi ko mene ba".

Ya k'arasa maganar yana murmushin jin dad'i.

A haka sukaci gaba da hira har ƙarfe tara  tayi sannan sukayi sallama, ta jawo littafan ta ta cigaba da rubutu har tara da rabi tayi sannan ta gama.


  Yaya Muhaisin yazo ya karɓi waya taje ta watsa ruwa ta saka kayan bacci, sai ga Ammi sun dawo ita da Mubarak da Kausar.





Koda suka dawo Kausar ma tayi bacci tun suna hanya  Mubarak ne kawai yazo ya rungume ta yana murna itama ta rungumeshi tana  murnar dawowar ƙannen nata  saboda tayi missing ɗinsu ba kaɗan ba.






Ammi ce tace

"Muwafaqa ki ɗauki Kausar ki canja mata  kaya zuwa waɗanda take bacci dasu".





"To Ammi".

ta ɗauki Kausar taje ta canza mata kayan bayan  ta canza mata ta  shimfiɗe ta sannan tasa Mubarak ya canza nashi suka fito tare.

Koda suka fito Abii ma ya dawo nan suka zauna suna fira tare da Abii da  Ammi da Yaya Muhaisin
har ƙarfe  sha ɗaya  tayi basu ankara ba.





Sai can Abii yace "kowa ya tashi yaje ya kwanta dare yayi.

suka miƙe suka masu sai da safe.


AISHATUL-MUWAFAQAWhere stories live. Discover now