Charpter 9

1.2K 45 12
                                    

💓💓 💓💓 💓💓
〰〰〰〰〰〰
*AISHATUL MUWAFAQA*
〰〰〰〰〰〰
💓💓 💓💓 💓💓
*1441H/2020M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*STORY AND WRITING:*
*AYSHER ALIYU *HUMAIRA(INNARO)*

*Dedicated to:*
*ZAINAB AHMAD SHAREEF*
           &
*HAFSAT ABBAS BABI*

~🗓 January~

'''Follow & Vote 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.'''

*_INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN, YA ALLAH MUNA ROƘONKA DA SUNAYENKA TSARKAKA, YA ALLAH KA BAYYANA MANA FAREESA CIKIN AMINCINKA, YA ALLAH KA KARETA DA KARIYAR KA A DUK INDA TAKE, YA ALLAH KA TSARE MANA ITA DA TSAREWARKA,YA ALLAH KASA TANA CIKIN YANAYI MAI KYAU KASA TA FAƊA HANNU NA GARI, YA ALLAH KA DAWO DA ITA HANNUN MAHAIFANTA LAFIYA, AMMEEN YA RAHMAN._*

_Ƴan'uwa Muna Baran Adu'arku Akan Ɓatan Ɗiyar Ɗaya Daga Cikin Marubutanmu Wato Rahma Ladingo, Allah Ya Bayyana Mana Yarinyar Cikin Aminsa Yasa Kuma Tana Ƙoshin Lafiya,Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum._


*Page 41-45*

_A gurguje_


*____________*📖 Bayan angama assembly suka koma class Mai English ya shigo ya masu ya fita, a haka a kayi ta masu karatu har aka tashi, Yaya Muhaisin yazo ya ɗauke ta sai gida .

Bayan takoma gida tayi wanka tayi sallah taci abinci ta wuce islamiyyah.

A haka dai rayuwar Muwafaƙa taci gaba da tafiya cikin ƙanƙanin lokaci tayi suna a makarantar su da ita da ƙawar ta Bakareeya, akan ƙoƙarin su duk wani presentation da za'ayi dasu akeyi a yayin da Muwafaƙa take a matsayin monitor Bakareeya kuma assistant.

Sosai suke shiri da Malam Arrida saboda ƙoƙarin su, shi kuma yana son ɗalibai masu ƙoƙari wanda har gidan su Muwafaƙa ansan da Malam Arrida saboda bata da magana da ya wuce Malam Arrida.

Sau da yawa idan Yaya Muhaisin ya kawo ta suna gaisawa da Malam Arrida saboda har extra lesson yake masu.

A ɓangaren Safwan ma kusan hakan ce takasan ce komai na tafiya dai-dai sai abunda ba'a rasa ba, Da kuma damuwar da tasha masa kai ya rasa hanyar da zai bi ya magance ta.

Inda a ɗayan ɓangare kuma mahaifin sa yasha masa kai akan maganar aure dan ɗan'uwan sa kuma abokin sa Fahad saura kwana ki ƙalilan auren sa.

Shirye-shriye ake tayi a kowa ne ɓangare wanda Safwan duk shirye-shiryen da sukeyi ƙarfin hali ne kawai yake yi saboda damuwar dake da munsa.

A ɓangaren Muwafaƙa ma shirye-Shriyen jarabawar canjen aji sukeyi inda duk tabi ta damu kanta sai kace wadda zata rubuta jarabawar shiga jami'a.

Zaune take duk ta barbaza littafai a gaban ta idan ta karanta wannan ta karanta wannan saboda gobe jarabawa huɗu za suyi.

Yaya muhaisin ne ya shigo yace, "Muwafaƙa har yanzu karatun ne akeyi?".

tace, "Eh Yaya kasan jarabawar gobe fa huɗu ne zamuyi".

yace, "To Allah ya taimaka tun ɗazu Yaya Ammar yake takira wai na baki waya ni kuma ina majalisa amma dole ya tasoni".

Ya ƙarashe maganar yana mai miƙo mata waya tace,

"wallahi kamar yasan ina son magana dashi kam".

Ta karɓi wayar shi kuma ya fita bayan ya kira ta ɗauka tace,

"Hello Yaya barka da yini, ya gida aiki?".

yace, "lafiya ƙalau lil Sis, ya makaranta dafatan komai na tafiya dai-dai?".

tace, "komai Lafiya Yaya sai dai kewar ka da mukayi".

yace, "yanzu dai albishirin ki".

Tace, "goro".

yace, "insha'Allah end of this month zan dawo kuma ina son maida kasuwan cina gaba ɗaya a gida".

tace, "dan Allah Yaya da gaske kai amma da naji daɗi wallahi".

yace, "Insha'Allah ki tayani da addu'a kawai, yasu Kausar da Mubarak?".

tace, "Suna nan ƙalau suna can wurin Ammi kasan maƙale matane, duk inda take Suna can".

yace, "Ki gaida su ba dai wani abu da kuke buƙata ko?".

tace, "eh Yaya bama buƙatar komai Yaya Muhaisin Yana Mana Komai".

yace, "Shikenan Haka Akeso Allah ya maku albarka ya karatun naki?".

tace, "Alhamdullilah Yaya Jarabawa ma mukeyi".

yace, "Allah ubangiji ya taimaka ya baku Sa'a bari nabar ki kiyi karatu sai da safe".

tace, "Tau Yaya nagode".

suka kashe wayar ta ajiye Taci gaba da karatu.

*WASHE GARI.*

Koda ta tashi tayi duk abunda tasa ba ta shirya ta wuce makaranta.

Cikin Ikon Allah suka yi jarabawar su lafiya suka gama akayi hutun makaranta Yanzu islamiyyah Kawai take Zuwa sai taya Ammi aikin gida.

A ɓangaren su Fahad ango kuwa shirye-shirye kawai suke yi bukin amarya ya rage saura sati ɗaya a fara Shagalin buki.

Ɓangaren Amarya ma suna nasu shirye-shirye Inda suka shirya ranar laraba a wanke amarya, Alhamis suyi Fulani's day, jumu'a ƙunshi ranar Assabar Da dare suyi dinner wadda hadda ango zai zo Lahadi a ɗaura aure da walima.

Ɓangaren Aunty Bilki shirye-Shiryen bukin ƙaunar mijin ta suke wanda ya rage saura sati ɗaya a fara shagalin buki.

Kuma duk Wani anko da akayi saida ta ɗinka ma Muwafaƙa, Kuma amarya tasha mata kai dan Allah suje gida Suzo da muwafaƙa dan ita gaskiya Tana son yarinyar .

Yau suka shirya da ita da amarya dan tana nan gidan ta duk wani gyaran jiki itace take mata.

Tare suka tafi mijin Aunty Balki ne ya kaisu Bayan ya ajesu yace zaije ya dawo da marec ce ya ɗauke su.

Sosai Ammi taji daɗin ganin ƴar tata sai da Suka gama gaisawa sannan Aunty Balki tace,

"Ammi dama tahowa nayi dan Allah ku aramani Muwafaƙa tunda sunyi Hutu kinga *IKHLAS* Ta matsa dan Allah mutaho mu tahi da ita har a gama buki".

Ammi tace, "Babbar magana sai ku jira Baban ku ya dawo idan zai barta dan kinfi kowa sanin halin sa".

tace, "Hakane Ammi Allah dai kasa ya Barta Dan nasan *IKHLAS* baza taji daɗi ba idan ba'a barta ba".

Ammi Tace, "Haka ne kinga ko yanzu ban san inda Muwafaƙa taja taba tun tahowar ku sunyi gaba, Kuma har da ita *IKHLAS* ɗin ta biye ma Muwafaƙa alhali ba'a so amarya tana yawo".

Aunty Balki tace, "Ya wuce suna gidan Amina dan nasan Muwafaƙa Bata da wurin zuwa da ya wuce can, Kuma ai duk sune dan ba wani girmewa *IKHLAS* ɗin tama Muwafaƙa ba".

Haka dai sukaci gaba da hira har su Muwafaƙa suka dawo aka dasa wata sabuwar fira.

Koda Abii ya dawo bayan sun gaisa Yaje yayi wanka Ammi tace ma Aunty Balki taje ta faɗa masa ta miƙe taje ɗakin sa.


*_Kuyi hakuri da wannan, shima da ƙyayar nayi_.*



*©INNARO•*

Você leu todos os capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Jan 09, 2020 ⏰

Adicione esta história à sua Biblioteca e seja notificado quando novos capítulos chegarem!

AISHATUL-MUWAFAQAOnde histórias criam vida. Descubra agora