♥
♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)(It's all about friendship)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*written *✍
-by-
*Deeja one love*Wattpad 13deeja.
Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.
An ƙarbo daga Abu huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace"Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace: alamomin munafiƙi guda uku ne,idan yayi magana sai yayi ƙarya,idan yayi alƙawari sai ya saɓa,idan aka amince mishi sai yayi ha'inci.
Allah maɗaukakin sarki yana cewa._*ya ku wa'inda kuka yi imani,idan fasiƙi yazo muku da labari to kuyi bincike,domin kada ku zargi mutane da jahilci,sai ku dawo kuna akan abinda kuka aikata kuna nadama*_.
*TSOKACI*.
Yanzu jama'a abinda yake damun mu kenan,bama tsayawa mu duba me ya faru,da zarar an kawo mana magana sai kiga kamar dama abinda muke jira kenan saboda hassada da ƙyashi da yayi mana katutu.Dama laifin ƴan uwan mu muke jira,sai kuma daga baya gaskiya tayi halin ta kaga mun dawo muna jin kunya,ya kamata mu gyara domin rabauta a wajen Allah maɗaukakin sarki,dan Allah mu dinga kyautata zato akan ƴan uwan mu zargi babu kyau.
Da manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yana cewa"na hane ku da yin zato domin shi zato shine mafi ƙaryar zance.Allah kuma yana cewa: yaku wa'inda kuka yi imani ku guji mafi yawan zato domin wani ɓangare na zato zunubi ne,kada ku tsanan ta bincike kada sashen ku da dinga sukar sashi.........
Allah kasa muji tsoron Allah,mu kiyaye wannan hadisan da ayoyin ubangiji Allah ka wanke zuciyoyin mu.
Don idan ya kasance kullum kana munana zato akan ɗan uwan ka to lallai ka fara neman tsari daga sharrin kanka,dan zuciyar ka abin tsoro ce.
Haƙiƙa *fatima batula* kin nuna mini cewa kin haifu kuma naji daɗin wannan abu da kika yi mini dan haka ina godiya
_*29*_Sai da nayi ajiyar zuciya sannan nace"shikenan Allah yasa hakan shi yafi ya kuma shige mana gaba",ta amsa da ameen.
Kasancewar bamu wani saba ba yasa bamu yi fira sosai ba,sai dai jefi jefi haka har biyu ta cika sannan nace musu"to zan shiga lecture yanzu sai anjiman ku".
Zuly ta miƙe tace"to shikenan ƙawata Allah ya bada sa'a amma ƙarfe nawa zaki fito ne",sai da nayi ɗan jim sannan nace"ƙarfe biyar".
"to shikenan nan da biyar zamu dawo muma",ban wani damu ba nace"shikenan sai na ganku",har na fara tafiya tace"am Juwairiyya number ɗin ki mana".
Murmushi nayi sannan na dawo na bata,itama ta bani nata sannan na juya na tafi cikeda kwanciyar hankali koba komai yanzu ina da ƙawaye.
Duk da abin jin shi nake sabo saboda ni ban taɓa ƙawa a waje ba, da farko Khairiyya ce ƙawa ta har muka girma ita da Rufaida,daga baya kuma Khairiyya ta dena kula ni.