30

978 25 0
                                    


    
    ♥ ❤
           
         ♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*written *✍
       -by-
         *Deeja one love*

Wattpad 13deeja.

Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *ONE LOVE* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe,  muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.

Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace"ba'a ɗaukar cuta,babu camfi babu camfi da mujiya,babu camfi da watan safar".

*ABIN NUFI*
 
Cuta bata taɓa tashi daga jikin wani ta dawo jikin ka da kanta idan ba da izinin Allah ba.

Camfi a musulunci babu kyau,Haka kuma kukan mujiya babu abinda yake kashewa ku sani manzon Allah a wani hadisin yace"da ace zaku yi dogaro da Allah matuƙar dogaro da ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu ya wayi gari cikin shi babu komai amma kuma ya kai yammaci cikin shi a ƙoshe".

Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace"wasu mutane zasu shiga aljanna zuciyoyin su kamar zuciyoyin tsuntsu".

   Haƙiƙa manzon Allah yayi gaskiya ka dogara da Allah sai Allah ya isar maka.

  Allah yana cewa a cikin Alqur'anin shi me girma *_domin lallai Allah shine abin dogaron muminai amma kuma kafirai basu da abin dogaro_*.
*muhammad aya ta 11*

Lallai mu duka ƴan *golden pen writers association* muna cewa *_hasbunallah wa ni'imal wakeel*.

*khadeeja z,hajjaju,zainab bala abubakar,meera ta annabi,fatima bala,fatima zahra,Aishatu babay,name khadeeja,khairat aminullah,hafsat nana sa'ad,Rabee'atu Auwal,Aisha,maman fadila,maman annur Habiba,Zainab dauda,maimunatu Abbas nuram da duk wanda ban ambata ba ina godiya sosai da sosai*.

*Zulaihat Isma'il ina jin dadin comments ɗin ki sosai Allah ya bar ƙauna*.

*idris khadija umar na gode da addu'a*

_*30*_.

Buɗe idanun shi yayi wanda ya canza kala daga fari tar zuwa ja,kafe Abba yayi da ido kafin ya buɗe baki yace"Abba nifa ba wai ina son ta bane kawai dai ina shiga farin ciki idan muna tare ne".

Abba ya kuma wani murmushin dai wanda ban san ma'anar shi ba,hannun shi ya riƙe yace"to kada ka kuma kawo ƙorafin Ummi ta hana ka ganin Mama na ɗin".

  Maida idanun shi yayi ya lumshe sannan yace"ai dama Abba ba ƙarar ta na kawo ba amma dai dan Allah ai ya kamata,ta sassauta haka saboda yanzu fa idan muka koma sai biki zamu dawo".

   Abba yace"Allah ya kaimu",buɗe idanu yayi ya kalli Abban ganin kamar be fahimci me yake nufi ba,buɗe baki yayi da nufin yin magana sai kuma ya fasa kawai ameen yace sannan ya miƙe ya fice.

   Baba malam yace"Khalil kenan rigima",Abba yace"ƙyale shi soyayya ta rufe mishi idanu amma ya kasa fahimtar hakan",hirar su suka cigaba wacce ta shafi zumuncin su da sauran su.

K'AREENATEEY Where stories live. Discover now