♥
♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)(It's all about friendship)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*written *✍
-by-
*Deeja one love*Wattpad 13deeja.
Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *ONE LOVE* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.
_*Duk wanda yake aikata aiki mummuna,ko yake zaluntar kan shi(yake shirka),sa'annan ya nemi gafarar Allah,to zai sami Allah me gafara kuma me jin ƙai*_
*_duk wanda ya aika ta aikin zunubi to kan shi yake yiwa,lallai Allah masani ne kuma me hikima ne_*
_*duk wanda ya aikata aiki mara kyau,ko aikin zunubi sa'annan ya jefi wani dashi,haƙiƙa yayi ƙirƙira da zunubi bayananne*_.
_*suratun nisa'i aya ta 110,111,112*_
*One love tana ji daku,group ɗin Ƙareenateey fans club da kuma deeja one love hausa novel*.
*sanaz ke ɗin ta daban ce a wajen one love ina ji dake irin sosai ɗin nan*.
Pls ku saka ni a addu'a sosai nake buƙatar addu'o'in ku.
_*33*_
Ƙara matsowa yayi kusa dani sannan yace"Buddy kece kika zama haka?",nayi fari da idanu ina faɗin"ya san ranka".
Jinjina kai yayi cike da mamaki,lallai abin ya fara bashi tsoro,yace"yanzu ina zuwa haka?",.
Baki na turo gaba nace"bayan daka dawo baka neme ni ba sannan yanzu kace wani wai ina zuwa",ɗan ware idanu yayi yace"Juwairiyya!".
"ba Juwairiyya ba juuuuu...zaka ce wannan ai ya zama out dated(tsohin yayi)",amma dai kin san har makaranta naje neman ki ban same ki ba yanzu ma siyayyar dana tsaya yi taki ce ina so naje gidan ku".
"to amma dai ai ka kira ni ka faɗa mini ko",murmushi yayi yace"yaushe rabon da ki kira ni,nima fa idan na kira ki sai kinga dama kike ɗauka".
Kallo na ya kuma yi ƙasa da sama yace"amma nayi mamaki dana ganki haka,akwai lectures amma baki je ba kuma ji shigar ki".
Kallon kaina nayi daga ƙasa zuwa sama nace"me shiga ta,tayi ne?",kashe ido yayi yace"kin canza ne daga Juwairiyyar dana sani me saka hijab da niƙab zuwa me saka gyale".
"nafa faɗa maka Juuu zaka dinga cewa ba wai Juwairiyya ba,sannan ma ni naje aka hana ni shiga shine na dawo".
"to yanzu muje na sauke ki a gida ko?",ɗan taɓe baki nayi nace"kaga ka bar ni ba'a gida zan kwana ba yau tare da ƙawa ta zamu kwana,ba gida nayi ba".
Cikin mamaki yake kallo na,sannan ya juya ya kalli wacce nake cewa tare zamu kwana da itan.
Fuska ɗoɗar sunan wani mulki namu,idan ka ganta ba zaka ce tayi kala da mutanen arziƙi ba,yatsu biyu ta ɗaga mishi alamar hi.