006-010

790 37 1
                                    


     ♥ ❤
            ♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*

*written *✍
       -by-
         *Deeja one love*

~Dedicated~

      To

     *~Aisha yunus(eesher lurv)~*

Wattpad 13deeja

Deeja1love.blogspot. com

An k'arbo daga abu huraira Allah ya k'ara masa yarda yace:Manzon Allah (SAW) ya hana aske wani yanki na kai a bar wani b'arin.

*YA AR-RAHMAN*

006-010

Ina zaune a daki kanne na suka dawo daga makaranta,abdul'azeez ya shigo da sallama, amsawa nayi, gefen gado ya zauna sannan yace"sweet ya dai naga kamar wani abu na damun ki", girgiza kai nayi nace"babu komai, kaje kitchen abincin ku yana nan", bece komai ba ya mike ya fita.

Ana sallar la'asar na shirya domin tafiya makarantar islamiya, dogon hijab na saka har kasa sannan na fita,a bakin get na tarar da yaya khaleed yana jiran fitowa ta, murmushi yayi mini nima na maida mishi, jerawa mukayi muna tafe muna fira kamar yadda muka saba.

Can bakin fita layin mu muka hangi abdulhafiz da ameer da kayan kwallo daga ganin alamu kwallon zasu tafi,yadda yaya khaleed bece komai ba haka nima ban ce komai ba.

Muna shiga makarantar na wuce nawa ajin shi kuma ya wuce office domin makarantar ta abba ce haka yaya khaleed ya bawa shugabantar makarantar kasancewar be cika zama ba.

Ina shiga ajin daliban ciki suka fara girmamani duk da akwai wa'inda muke sa'a daya kai harda wa'inda suka girmeni sai dai fa a shekaru kawai amma a karatu duk na fisu, karatu mukayi cikin girmama juna har lokacin tashi yayi.

Sai dana jira ya kammala abinda yake yi sannan muka taho,muna zuwa kofar gida mita nayin parking, rufaida ce ta fito daga ciki da alamu bata ma lura damu ba.

Saurayin dake ciki ne ya rike hannun ta yana murmushi,itama murmushin tayi mishi,dago kan da zata yi suka hada ido da yaya khaleed, ganin irin kallon da muke mata ne yasa duk ta tsargu.

Cikin daburcewa ta janye hannun ta, ta fara tafiya har ta shiga get yaya khaleed ya kwala mata kira jikin ta ya hau rawa, karasawa kusa da ita mukayi, kallon tuhuma yayi mata kafin yace"ki sani duk abinda kika yi a wannan lokacin kanki kike yi mawa, sannan duk abinda kikayi watarana zaki yi dana sani dan haka kiji tsoron Allah a duk inda kike", kallo ma yayi have"muje ko", wucewa mukayi muka barta a tsaye jiki a sanyaye.

Mun zana jamb din mu alhamdulillahi ya fto kuma munci baba data Dan duk rashin jin yaran gidan mu akwai kwakwalwa fa.

Yanzu haka yau muke graduating daga secondary, dan mun gama wa'ec da neco, yanzu zaman jiran result muke.

Ina zaune ina yanke farce, khairiyya da rufaida sukayi sallama suka yi,  murmushi nayi nace"sannun ku da zuwa ku karaso kunji,zama suka yi khairiyya ta harareni tace"ke wallahi baki da mutunci ko leke wato saboda yanzu babu makaranta ko", maraicece fuska nayi nace"yi hakuri wallahi ba haka bane kinsan abubuwa sun yi mini yawa ne".

Dariya suka yi suka tafa kafin khairiyya tace"aifa kiji sai kace wata yar kasuwa", dariya muka yi gaba daya. Nan dai muka cigaba da fira har yamma tayi.

K'AREENATEEY Where stories live. Discover now