13

1.9K 113 16
                                    

🌹🌹🌹
           *_DR. HABIBULLAH_*
                        🌹🌹🌹

_writing by_📚✍🏻
       *_🌹 Ameena firstlady🌹_*

*WATTPAD*
@Ameenafirstladyy

*🌈 Kainuwawritersassociation*

https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation

*_(This page is yours my sweet sisters Husaina sunusi ibadan thank you so much I'm so proud of you)_*💓💓

'''I can't forget you my daughter NEESHER JAY'''🌹🌹

13

_________________________

Jiddah saida taci kukanta Sannan ta share hawayenta ta shiga wanka.
Tana fitowa kiran hibban ya shigo ta daga fara'a.
"Yaya hibban ya aiki.."?
"Kalau kanwata, badai wata matsala ko?
"Eh babu" tace.
Murmushin jin dadi yayi sannan yayi mata sallama yaci gaba da aikinsa.

Cikin Wata ash color din atamfa docuwar riga ta shirya, bakaramin kyau tayi ba,, har zata fita kiran Kabir ya shigo wayarta.
A sanyaye ta daga tareda sallama dauke a bakinta.
Amsa mata yayi sannan yace "jiddah waye wannan wanda yazo ɗaukar ki".. ya jeho mata tambayar.
"Yayana mana"
"A'a jiddah bayan wannan fa"?    "Kabir bazan boye maka ba amma kayi hakuri zakaji bayani a daga afnan amma karka ga laifi na dan Allah".
Kabir kasa fahimtar bayananta yayi hakan yasa ya katse kiran kawai dan hankalin shi ya fara tashi..

Jiddah kuwa jagwab ta zauna kan katifar ta tana rintse ido, sam bazata iya misalta yadda takesan Kabir ba shi kadai ta bawa soyayyar ta gashi ƙaddara tasa zata rabu dashi ta auri wanda babu soyayyar shi ko kadan a zuciyarta.
Palour ta fita ta zauna tana jiran a kirawo sallar la'asar sannan ta tashi.

Habib yana gama shan coffeen shi ya sake shiga ya sheka wanka sannan ya fito ya kwanta bisa three sitter dake ɗakin kanshi na kallan silling..
"Meyasa nake damuwa da ganinta da wani danayi,  mezai sa na damu bayan sam babu soyayyar ta a ranshi infact ma shi tsanarta ce a ransa dan Baiga abin so a jikinta ba..."
Tunanin shi ne ya tsaya tunawa da yayi ta amsa zata aure shi cewar mommy, rintse idanuwanshi yayi da sukayi masa zafi da nauyi.
"Zaki gane kuskurenki very soon,," ya faɗa ko bude ido baiyiba.
Jin ana kiran sallah ne yasa ya fice dan zuwa masallaci....

Suna idar da Sallah tareda hibban suka shigo gidan,, tana zaune a palour taji sallamar su sannan ta amsa tana kasa dakanta dan batasan su hada ido da Habib.
"Kanwata" hibban ya kirata cikin fara'a.
Ɗago kanta tayi da murmushi tace "yaya hibban sannu da dawowa"
"Yauwa jiddah, tashi muje ki tayani gyara dakina" ..
Tashi tayi da sauri dan dama a kuntace take a palourn.
Kallon gefen da Habib yake tayi yana zaune cikin wani tsadaddan farin yadi wanda ya amshe shi sosai ya fito da ainihin farar fatar shi saidai fuskar nan a haɗe kamar kullum,,.
Taɓe baki jiddah tayi tace "mutum a cikin gida ma bazaiyi fara'a kamar sauran mutane ba" ta faɗa tana bin bayan Hibban.
Sarai Habib ya ganta wanda tuni zuciyarshi tafara zafi da tafasa saidai bai nuna ba duk da shi kadai ne a palourn lebensa ya ciza sannan ya wani hura baki ya fitar da iska cikeda bacin rai...

Hibban da jiddah kuwa hirar su sukeyi harda dariya "yaya hibban nifa nayi maka mata kawai kai nakeso ka motsa"
"Uhmm wacece fadamin"
"Afnan na baka kuma na yarda da ita sosai.."
Dariya yayi yace "angama kanwata jeki shirya ki raka ni"
Cikeda mamaki ta kalle shi "da gaske kake yaya hibban ka amince"
Kautar da kanshi yayi yana barin wajan zuwa bathroom danyin wanka sannan yace "naki wasa ne yar nan Ni kingama wanka zanyi ke kawai zan jira" ya shige batareda ya kuma cewa komaiba.
Abin ya ba jiddah mamaki sosai, part ɗinsu ta koma lokacin Habib bayanan kai tsaye ɗakinta ta wuce ta dauko mayafinta sannan ta haifa sama wajan mommy.
"Mommy zamu fita nida yaya hibban"
"Ina kuma zakuje sarakan yawo"?
"Da alamar dai yau suruka zamo samo miki" jiddah tace tana dariya.
"Aaa toku je maza a zabo mai kyawawan halaye dai" mommy tace.
Da gudu jiddah tayi hanyar fita tana dariya "aima mommy tanada kyawawan halayen ma" ta faɗa tana ficewa.

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now