31

1.7K 107 10
                                    

🌹🌹🌹
           *_DR. HABIBULLAH_*
                        🌹🌹🌹

вч
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻

*wαttpαd:-ameenafirstladyy*

*🌈K͎a͎i͎n͎u͎w͎a͎ W͎r͎i͎t͎e͎r͎s͎ A͎s͎s͎o͎c͎i͎a͎t͎i͎o͎n͎*🤝🏻

{31}

Sosai mommy taci gaba da bawa jiddah kulawa kuma tana samun sauki sosai,, hibban da Afnan kuwa kullum suna asibitin dan anan yake barin Afnan ya tafi office saiya dawo yake ɗaukanta su tafi gida shima sai mommy tayi ta faɗan suzo su tafi saboda dare..

Kwanan su biyar jiddah ta warware sosai komai nata ya dawo nrml saidai rashin kwarin jiki saboda bata iya cin abinci sosai mommy tayi fadan harta gaji...

Kwana biyu jiddah ta kara taci gaba da zuwa makarantar ta hankali kwance saidai bata sake kula Amra ba Dan haushin ta takeji ganin take kamar ita taja mata koma menene..

Tare da mommy suka cigaba da rainon cikin nata wanda yanzu yafara girma duk da sai Afnan ta riga ta haihuwa, dan ita tuni hibban ya hanata fita ko ina..

tunda Habib ya koma sau biyu kawai sukayi waya da mommy saidai sama sama suke gaisawa ta kashe wayarta, duk da yasan dalilin amma yanaso yaji lafiyar dansa sannan ya sake yiwa jiddah jan kunne akan karta sake yunkurin zubar masa da cikin dan yasan ta da taurin kan tsiya kodan ta bata masa rai zata iya attempt din sake zubarwa..
tsaki yayi kasa ƙasa sannan ya ajiye book ɗin dake hannun sa ya dauki wayar shi yafara neman layin mommy..
mommy dake zaune itada jiddah sakamakon weekend ne, taji karar wayarta..
lokacin wayar na hannun jiddah tana ganin Habib ne ta sauya fuska sannan ta mikawa mommy wayarta tabar palourn Dan batasan ma abinda zai sake hadata da shi..
itama mommy ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar,..
shiru yayi bai sake cewa komaiba, jin haka yasa mommy tace "akwai wani abu ne kuma"?
kamar bayasan maganar yac "a'a babu"!
"shikenan ka kulada kanka" kafin yayi magana mommy ta katse kiran sannan tabi bayan jiddah zuwa dakinta..
a kwance mommy ta samu jiddah tana karatu, saidai kallo daya tayi mata ta gane tunani ne fal zuciyarta,.
kusa da ita ta zauna sannan ta kamo hannun ta tareda kiran sunan ta.
itama jiddan kallan mommy tayi saidai tuni hawaye suka zubo Mata.
"meya faru"! mommy ta Tambaye ta..
cikin kuka jiddah tace "Ina tsoro kar yaya Habib ya mayar da auran mu, dan Allah mommy karki saurare shi dan wlhy kashe ni ne kawai bazaiyi ba muddin naci gaba da zaman aure dashi, nasan nayi kuskure kema bakiji dadin Hakan ba. "
hararan da mommy tayi mata ne yasa tayi saurin yin shiru.
"bana ce karna kara jin wannan Maganar ba tunda ta wuce, kuma saidai idan ke kika so Habib ya mayar dake"..!
kallan mommy tayi tareda taɓe fuska cikin shagwaba tace "Allah mommy bazan so ba, to tayaya ma zanso komawa wajan wanda baya sona.."
murmushi mommy tayi dan ta fahimci har yanzu da yarinta akan jiddah sosai.
"kinsan Habib bayasan raini bayasan wargi da taurin kai saboda haka ko mezai hadaki dashi saiki kiyaye ko kiranki yayi karki dagawa dan yanzu ya gano bakyasan zama dashi ne da zarar kinyi masa wani abu magana daya kawai zaiyi ya mayar dake kuma shikenan kinjawa kanki saboda saiki kiyaye"... mommy tace tana saukowa daga saman bed din sannan tace "kinji dai abinda ne idan kika jawa kanki babu ruwana".ta fice tabar jiddah a ɗakin..

maganganun mommy sun shigeta saidai har zuciyarta ta kudurta bazata taɓa daukan wulakanci daga Habib ba a yanzu saidai koma menene ya faru amma bazata dauki wulakanci ba ita kam..

Habib kuwa yakai makura wajan ɓacin rai sai faman tsaki yake shi kadai da tunanin jiddah a ranshi"muddin ta zubar masa da ciki to tabbas matakin da zai dauka bazaiwa kowa daɗi ba tunda ya fahimci har yanzu batayi hankali ba,..
jin ana masa nocking ne ya katse masa tunanin sa sannan yabda iznin shigowa duk yasan Sultan...
a hankali Sultan ya shigo saidai kallo daya yayiwa Habib ya gano ransa a bace yake, murmushi yayi sannan ya zauna yana daga kiran da Angelina tayi masa..
sun dade suna waya kamar karsu rabu sannan suka ajiye wayar yana maida kallanshi kan Habib wanda fuskar kamar hadari babu alamun fara'a ko kadan a kanta..
murmushi Sultan ya sakeyi sannan yace "ya akayi ne abban unborn"!
dan sassauta fuskan nashi yayi saidai baice komai ba.
"look habib fadamin Matsalar rike damuwa bashida wani amfani"!
saida ya dauki dan lokaci kamar bazaiyi magana ba sannan yace "Sultan kasan maganata bata wuce ta waccan yarinyar"
"wacce yarinyar kenan!?" Sultan ya tambaya cikin rashin fahimta.
tsaki Habib yayi sannan yayi banza dashi dan gani yake Sultan ya gane raina masa hankali yake..
"ohhh! jiddah kake nufi wai"?
"yahh! ita" Habib yace sannan ya faɗa komai har sakin da yayi mata sannan ya baro ƙasar..
sauke numfashi Sultan ya kalli Habib yace "gaskiya kayi kuskure Habib".
harara Habib yabi shi dashi sannan yace "danayi me"?
"jiddah tanada hakuri meyasa zakaga laifin ta bayan kaine mai laifi duk fa macen da nunawa kiyayya to zata iya abinda yafi wannan tunda itama ba sanka takeba, tana ganin kamar dan cikin kake santa duk ranar da babu zataga wulakanci to dole tayi yunkurin zubar dashi, kuma kaga har yanzu jiddah she's youn so saina lallaɓata sannan zata fahimce ka"!
wani kallo Habib yakewa Sultan harya gama, murmushi yayi dan maganar Sultan ɗin ta karshe dariya ma tabashi wai kamar jiddah zai lallaba..
"yanzu me kake nufi"
"ina nufin ka mayar da ita tunda har saita haihu sannan ta gama iddarta"
"na mayar da ita,"! Habib ya tambaya cikeda mamakin kalmar.
"eh mana haka nake nufi"
tsaki Habib yayi yace "never, tayaya kake tunanin Ni zan cigaba da zama da wannan yarinyar"!
mamaki ne ya kama Sultan dan shi sai yau ya dada tabbatar da cewa Habib baisan menene so ba..
duk yadda yaso ya fahimtar da Habib yaki fuskantar shi dole ya kyale shi suka rabu a haka tun kafin ya sauya mishi Yanzu...

Habib ya dade yana juya maganar Sultan a ranshi saidai shi sam baya jin zai iya sakewa harya mayar da auran nasu dan yanajin zafin abinda tayi har yanzu...

yau kwana biyu Kenan da Habib ya kira mommy saidai bai sake tunanin sake kiran nata ba duk da yanaso ya samu yaji lafiyar dansa saidai babu yadda zaiyi sai hibban ya kira yace ya dinga kaita duk inda zataje..
"to yaya".
"karka kara sakacin barinta zuwa wani wajan ita kadai"!
"Amma yaya akwai lokacin da nake tsaka da aiki mezai hana a samo mata driv.."
da kakkausar murya Habib ya kira sunan shi sannan yace "kafi kowa sanin banasan gaddama, ko"!
"I'm sorry Yaya"
tsaki kawai yayi ya kashe wayar, har zai ajiye sai kuma ya yafara neman layin jiddah,cikin fushi ya kara wayan a kunnen shi saidai tun kafin ta daga yaji kamar ya katse dan baisan me zaice mata ba...
cikin tsananin mamaki jiddah take bin wayar da kallo, maganganun mommy ta tuna yasa tayi saurin dagawa saidai Muryar a cunkushe..
"waye"? ta Tambaya cikeda rainin hankali..
wani bugu yaji zuciyarshi tayi cikin mamaki da takaici ya yanke kiran kawai yana huci..
ya dade yana juya abin a ranshi da kyar ya dauki wayar tashi ya tura mata da sako..
"karki sake fita batareda izinina ba, sannan hibban zai dinga kaiki duk inda zaki.."! Yana ganawa yayi sendind sannan ya shiga bathroom..

tsaki jiddah tayi ganin sakon nashi dan abin ma haushi ya bata wai karta sake fita waya faɗa masa yanzu zataji maganar shi bayan sakin dake tsakanin su, cikin takaici itama tayi masa reply..
"ohh Yaya Habib I'm sorry, saidai idan fita ta kamani zan fita kawai tunda baka nan, sannan ka kyale yaya hibban shima abubuwa sunyi masa yawa so zan dinga hawa na haya kawai, kuma ka rage isa yanzu akwai saki tsakanin mu watanni ya rage nayi iddah..."

fitowar shi kenan yaji karar shigowar sako, saida ya gama shiryawa sannan ya buɗe sakon saidai kafin ya gama karantawa kanshi yafara wani mugun sara masa babu shiri ya saurin zama kan bed ɗinsa Dan yadda yaji wata juwa na daukan shi ga wani zufa dake karyo masa tako ina kamar ba daga wanka ya fito ba...

✍️✍️✍️✍️

DR. HABIBULLAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora