33

1.6K 117 10
                                    

🌹🌹🌹
            *_DR. HABIBULLAH_*
                           🌹🌹🌹

ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻

*wαttpαd:Ameenafirstladyy*

________________________
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motives the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________

{33}

Suna zuwa kuwa mommy tafara yi masa faɗa akan meyasa ya bari takai rana haka..
Saurin tarewa jiddah tayi da cewa "mommy kinsan idan na hadu da Afnan bamasan rabuwa" hararan ta mommy tayi tace aina sani dama daga yau dai bazaki sake fita ba saidai awo ko school" tana gama fadan haka ta wuce sama ta barsu..
Hibban bai wani zauna ba yayi mata sallama ya tafi dan yanada aiki a gida.

Kwanaki sun ja kamar yadda cikin jiddah yanzu yakai 7month, yanzu kam tanajin nauyin kanta sosai, saidai hakan bai hanata zuwa makarantar taba sannan komai tanayinsa yadda Yakamata dan sosai ta mayar da hankalinta kan karatun nata..
Sam yanzu babu abinda ya sake hadata da Habib dan ko mommy yanzu ba sosai take samun shi a waya ba shiyasa take komai hankalin ta a kwance sannan take saurin manta wa dashi a matsayin matsalar ta, sai shirin exam kawai takeyi yanzu, bakaramin murna takeyi ba yadda abin yazo mata cikin sauki zata haihu batareda wani tunanin makaranta ba..

Yau da sassafe ta fito cikin shirin ta tana sauri sauri zata fice daga tsaye take breakfast din cikin sauri..
Mommy ce ta sauko palourn taga yadda jiddan ke sauri taki zama taci abincin cikin nutsuwa..
"Saurin duk tafiya school ɗinne"?
"Eh mommy karna makara shiyasa"
Kyaleta mommy tayi sannan ta wuce kitchen dan haɗa coffee.
Hibban na shigowa ta ajiye cup din hannunta tana fadin "yauwa yayana dama kai nake jira"
Dan kallanta yayi sannan yace "ai saki bari na gaisa da mommy ko" ya faɗa ya nufa kitchen din.
Tare suka fito da mommy sannan sukayi sallama suka fice daga gidan..

Cikin ikon Allah jidda ta fara exam hankali kwance duk da cikinta yayi girma sosai amma haka take kokari takeyi batareda wata damuwa ba, kullum hibban ke kaita kuma ya dauko ta shima kuma ba karamin tausayin ta yake jiba..

Da asuba mommy ta tashi jiddah tace zata tafi asibiti Afnan ce zata haihu, cikeda murna jiddah tace zata bi mommyn amma tace babu inda zata bita tunda yau ma tana da exam..

Jiddah na cikin shiri taji karar wayarta, sunan mommy ne yasa tayi saurin picking,, wani dan karamin ihu tayi na murna jin afnan ta haihu.
Mommy kuwa kashe wayarta tayi dan tasan halin jiddah yanzu saita fara yi mata shirme...
Jiddah sai ita kadai ta tafi dan hibban bai samu kaita ba, har aka tashi suka fito, tayi mamakin ganin hibban yazo ɗaukar ta da murmushi ta karasa jikin motar tana tsokanar shi..
"Yaya hibban yau an ka zama baba" ta faɗa tana dan taɓe baki.
Dariya yayi yace "saura ke zaki zama mama, wai wayaga jiddah da baby" shima ya faɗa yana mata gwalo..
Haɗe fuska tayi tace "wlhy kasan nikam zanyi kyau da baby ba Kamar kai ba".!
"Ni dama nace zanyi kyau ne, saidai ke mu jira muga irin kyaun da zakiyi ai"
Sarai tasan magana ya faɗa mata dan tsokana amma saita fuske ta shige motar yaja suka bar school ɗin..

Kai tsaye gidan shi tace ya kaita, acan ta samu mommy tana shiga ta fara murna tana daukan baby girl din tareda zuba mata ido kamar ta hadeyi ta..
Sai yamma itada mommy suka bar gidan,..
"Amma Afnan tasha wahala sosai ko mommy"?
"A'a bata sha wata wahala sosaiba"
"Amma naga ko magana batayi sosai" ta sake tambayar mommy..
Mommy dake driven kuwa dariya jiddan ta kusa bata amma sai make tace "nima dai bansan Dalili ba"..
Sai tambayoyi jiddan ke mata tana bata amsa sannan tace "mommy mu wuce shopping pls"
Batareda mommyn tace komaiba ta juya kan motar suka wuce shopping mall dan tasan idan ma bataje ba ta shiga Uku da shagwaban jiddah..
Sosai ta jidi kaya kamar hauka mommy kuwa duk siyayyar kayan babies tayi dan yanzu tana sane cikin jiddah ya shiga wata na tara, ba kananun kudi mommy ta kashe a lokacin ba ita kuwa jiddah batasan ma mommy nayi ba  hankalinta yana kan kayan makulashe..

Yau su jiddah suka gama exam suka samu hutu bakaramin daɗi taji ba dan sunan Afnan zatayi shi hankali kwance gobe sai faman shiri sukeyi gidan..

Tun asuba ta tafi gidan hibban, acan ta shirya akaci suna aka zubar da dukiya dan hibban yayi bajinta ya zubar da kudi ba kananu ba,,..

Tunda Afnan ta tafi gida wanka badan hibban yaso ba ya barta dole ya dawo part ɗinsa Dan yace bazai iya zama gidan shi kadai babu matar sa ba duk sanda ta dawo ya saiya koma shima, jiddah tayi masa dariya da tsokana sosai saidai shi bai kulata ba saidai yayi dariya kawai...
Dakin mommy jiddah ta koma da kwana dan dole mommy ta tilasta Tata ta koma dan kar haihuwar tazo ba kowa kusa da ita..




_pls kuyi manage da wannan_👈

coммenт and voтe 🤝🏻

*ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ*✍🏻

Not edited

DR. HABIBULLAHWo Geschichten leben. Entdecke jetzt