47

1.8K 110 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
         *_DR. HABIBULLAH_*
                                 🌹🌹🌹🌹

вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч🌹*

                 *wαttpαd*
              Ameenafirstladyy

{47}

.... Tunda ta dawo mommy ta hanata fita daga daki sai ɗaki dan ko palour bata fita koda yaushe suna daki ana mata gyaran jiki ko shan magunguna kala kala harta fara gajiya.
Habib tun yana nacin da faɗa harya gaji ya kyaleta kawai yaci gaba da shirye-shiryen taron da zasuyi..
saidai koda yaushe suna maƙale ta waya ba dare ba rana..

kwana huɗu ya rage yau mommy ta shirya kamu na Musamman, anyi kamu angama lafiya gida duk ya tara jama'a..
washe gari da yamma aka dunguma zuwa walima cikin wani babban hall da aka kayata shi abin sha'awa.
yaso mommy tace yazo ya kaisu danya ga jiddah amma tace bata yarda ba saidai yayi nashi zuwan daban shida abokansa tunda walimar harda shi aka tsara.
tare yaje dasu Sultan da Dr Ahmad daman sune manyan abokan nashi da yake dasu, saida kowa ya hallara sannan su mommy suka zo wajan tana rike da hannun jiddah wanda yasha bakin lalle da ja.
kanta na kasa rufe har mommy ta kaita kusa dashi ta zaunar da ita sannan ta dan matsa kusa dashi daya kafe su da idanuwa Kamar ya lashe..
"saura kayiwa mutane rashin kunya a wajan walima"
murmushi shima yayi ya matso da kanshi kusa da mommy yace "amma ai ta buɗe fuskar tata ko mommy"!
dukan wasa takai masa ya farayin dariya, basu wani daɗe da zuwa ba malaman da aka gayyato suka fara nasiha da wa'azi duk hall ɗin yayi tsit da alamu maganganun suna shigar su..
har aka gama ba wani hayaniya shiyasa Habib bai damu ba shida bayasan hayaniya ko kadan, lokaci zuwa lokaci yake kai kallanshi kanta amma sam har aka tashi bata ɗago ba kanta na ƙasa cikin wani mayafi mai shegen kyau..

a matuƙar gajiye suka koma gida, shi dai Habib duk takaici ya gama kama shi na hanashi ganin amarya shi da akayi, yanzu ma dayake driving zaikai Dr Ahmad gida da Sultan tare da matan su sai surutu sukeyi shidai yayi shiru kawai..
"wai Habib yadai duk ka wani shiru kamar ba shagalin ka akeyi ba"
tsaki ya ɗanyi sannan yace "Sultan kyale ni kawai ina bukatar matata amma ko ganinta ya faskara"!
su duka sukayi masa dariya har Angelina da take ɗan jin Hausa yanzu.
"kaida zaka tafi da ita gaba daya kubar gidan ma meye na wani jin haushi"
shiru yayi kawai bai ba Dr amsa ba dan yasan bazasu fahimci irin abinda yake ji gameda matar tashi ba..

dare nayi ya shigo palourn su, mutane sai tsokanar shi sukeyi amma bai saurare suba, yanaji suna masa tsiya wai dama wannan ɗan kurman ba kula ku zaiyi ba wannan jiddah ta shiga Uku kafin ma ta koya masa magana aiki ne balle akai ga su saba..
sosai maganar tasu tabashi dariya har ya shiga dakin mommy yana murmushi.
"kalau kuwa ka shigo kana faman murmushi kai kaɗai"?
"babu"
"to me ya kawo ka dakina na"!?
"ohh! momma coffee nakeso kisa jiddah ta haɗa min"...
kallan shi tayi kamar tanasan cewa wani abu sai kuma yaji tace "shikenan zata kawo maka"!
bai ja maganar tasu ba ya fice yana godiya kawai tun kafin ta sauya shawara..

dakin jiddan ta shiga tana zaune da wasu ƴaƴan makwabtan su na ƙauye da aka zo dasu suna ta hira mommy ta shigo tace ta shirya taje ta haɗa masa coffee yace takai masa part ɗinsa.
amsawa tayi sannan ta shiga kitchen ta haɗa masa hot coffee ta ɗauko mayafinta ta wuce kai masa..

tunda ta shigo dakin ya kafe ta da idanuwanshi ko ƙiftawa bayayi harta karaso ta ajiye masa kan table tace "ga coffeen Nan na kawo"!
murmushi yayi sannan ya taso ya riƙo hannun ta yace "aiba yanzu zan sha ba"
ɗago dara daran idanuwan ta tayi zatayi Magana taji yace "mata ta naso gani dama, ko nayi laifi"!?
"a'a bakayi laifi ba amma haɗa zance babu kyau ai"
wani lallausan murmushi yayi har kyawawan fararan haƙoransa suka bayyana reras dasu.
"haɗa zance ma kamawa takeyi ai, anayin tane dan asamu hanyar bullewa.."
dariya itama tayi tana ƙasa da kanta..
"zan koma kar mommy ta dawo taji ban dawo ba"
"to menene aita san kina nan wajan mijinki"
"amma.."!
"shhht! ki saki jikin ki babu abinda zata ce nima kuma babu abinda zanyi miki kawai zaki ɗan tayani hira ne before you leave"!

saida ya gama shan coffeen sannan yace ta taimaka ta dafa masa noddle Dan yunwa yake ji..
bata tafi ba saida ta dafa masa sannan ya zaunar da ita yace tare zasu ci danya fahimci bataci komai ba itama..
dakyar ta samu ya rako ta ta dawo sannan ya koma cikeda kewar matarsa..

ranar dinner party kuwa sai yamma sannan aka fara shirya jiddah, tana dakin su inna marka can aka kai makeover tafara tsantsara Mata kwalliyar ban mamaki..
"wannan kwalliya kamar baza a goge taba kai jama'a ƴan birni kuna abinda kuka ga dama a bi a narka kuɗi akan wannan aikin banzan" inna marka take ta faman tsiya kamar wacce da kuɗin ta zata biya.
"inna idan kinaso kema ki zauna ayi miki idan bahaka ba ko hall ɗin baza a barki ki shiga ba".
"yo Kar a bari mana dama nace muku zanje ne irin wannan wajan saika ga wata kamar aljana haka kawai nakai kaina na dawo a razane"
dariya sukayi tayi mata har aka gama mommy ta kawo mata kayan ta.
wata haɗaɗɗiyar  dinner gown ce sky blue har Ƙasa take ja cikin kankanin lokaci aka cakara mata head tie ɗinta ta fito kamar ba ita ba..

tuni motocin kawayen ta suka tafi, dama Habib ya dame su da kira tayi sauri ta fito lokaci yana kurewa..
Sultan ne yaja su har hall din suna zuwa suka wuce wajan da aka tanadar musu sannan aka fara gudanar da taro sun zama taurari a wajan kashewa kowa ido sukeyi da kyaun su..
duk wani motsin su tare da yaron su sukeyi wanda shima aka ƙure masa wanka kamar ba yaro ba yana tsakiyar su abin gwanin sha'awa...

(wannan shine ake kira da ƙara'i😂😂😂😂)

a matuƙar gajiye suka dawo daga wajan dinner saidai duk takasa cin abinci duk da tana jin yunwar, mommy harta gaji da lallashinta ta fice tace ai cikin tane..

Habib na shigowa palourn mommy ta fito daga ɗakin jiddan tana mita.
"yauwa tunda kai tanajin tsoron ka har Yanzu saikaje kasa ta taci abinci tunda ni bazataji tawa ba, ayi yarinya da shegiyar kafiya" ta faɗa tana barin palourn..
kai tsaye dakin ya shiga, kawayen nata na ganin shi fuskar nan a haɗe suka fice, da sauri ta tashi tsaye tana rarrabe idanuwa kamar munafuka.
jin saukar hannuwanshi tayi a ƙugunta tago kai tana kallan shi..
"meyasa ƙika ƙi cin abinci"!?
"na koshi ne..."!
ji tayi ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya fara yi mata wani salo na musamman saida ya tabbatar ta nutsu sannan ya sake kallanta da idanunshi da suka yi wani iri yace.
"kinaso ki jamin matsala ne, kinsan fa ba'a so mace ta zauna da yunwa kota dinga ci fiye da ƙima duk suna haifar illa.."!
zata sakeyin magana ya kuma haɗe bakin nasu, wannan karan kam saida tafara kokarin kwantar kanta sannan ya sake ta yana murmushi.
"muje kici abinci, ko kuma.." yayi shiru yana ɗan cizan lips ɗinshi haɗe da cigaba da kallan ta da rikitattun eyes ɗinsa...


✍✍

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now