22

1.8K 109 11
                                    

🌹🌹🌹
             *_DR. HABIBULLAH_*
                             🌹🌹🌹

    nα
*🌹ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ*🌹

ⓒ ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ

    
          *wɑttpɑɗ*
     @ᴀᴍᴇᴇɴᴀғɪʀsᴛʟᴀᴅʏʏ

____________________________
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
____________________________

( *_Kuyimin afwa kwana biyu zaku jini shiru hakan ya faru ne dalilin uzuri danake dashi zanci gabada typing da zarar komai ya kammala na gode da kulawarku sosai_*)

22

...... jiddah kuwa sai yamma ta tashi duk da har lokacin jikinta babu kwari amma taji dadin jikin sosai.
Mommy ce ta haɗa mata tea mai kauri kamar yadda Dr Ahmad yace da kyar aka samu tasha kaɗan dan bakinta babu taste sosai,,,, hibban da Afnan ma sai yamma mommy tace ya kamata su tafi kar dare yayi suma zuwa safiya za'a sallame su.
Haka suka tafi cikeda tausayinta "gaskiya dear Yaya Habib baiyiwa jiddah adalci ba sam"
Hararan wasa hibban yayiwa Afnan yace "to ba matarsa bace koma me yayi mata ai babu wani abu"
"Duk da haka dai yayi rashin tausayi".
Murmushi kawai hibban yayi dan shima yasan gaskiya ta faɗa yaya Habib baiyi mata adalci ba gashi nan yanzu yaja mata kwanciya a asibiti.

Jiddah kuwa tunda ta farka tasha tea Bata sake magana ba dan batajin zata iya surutu a yanayin da take ciki., Lokaci zuwa lokaci dai takanyi hawayen baƙin ciki sai mommy ce kawai ke bata hakuri, a haka Dr Ahmad ya shigo dakin.
"Mommy zan wuce gida akwai wani abinda kuke buƙata"?
"A'a Ahmad mungode sosai"
Shiru yayi yana maida kansa kan jiddah dake kwance "ki lura wajan motsi da tashi saboda gudun matsala"
Daga kai kawai tayi dan haushi ma ya bata da maganar tasa.
Mommy ce tace shikenan zata kula ai.
Sallama yayi musu sannan ya tafi dan sai zuwa gobe zai sallame su.

Ko kaka jiddah tayi kyakkyawan motsi saita yi kuka sosai mommy kaɗai ke lallashin ta, har dare bata sake cin komaiba.



ʀᴜssɪᴀ:- ᴍᴏsᴄᴏᴡ ᴄɪᴛʏ

Azimut hotel. Fitowar shi Kenan daga hadaddan bathroom ɗinsa Yana tsane ruwan daya kwanta jikin kyakkyawar fatar shi, tsaki yayi yana matsawa jikin wani dan karamin table na glass, tafkekiyar wayarshi ya dauka tareda karawa a kunnen shi.
"Sultan ina san contact din shugaban makarantar yanzu"
Daga can ɓangaran Sultan yace "shikenan zan Turo maka amma kafara duba makarantar idan tayi maka"
"Ok" Kawai yace yana kashe wayarshi.
Kai tsaye wardrobe ya nufa ya shirya cikin ƙananan kaya wanda suka amshe shi tsaff ya feshe jikinsa da turare mai sanyin ƙamshi.
Laptop ɗinsa ya janyo ya yafara binciken makarantar babu bata lokaci yayi apply a RUDN University of Moscow.
Bai tashi ba saida ya kammala komai sannan ya tashi ya kira Sultan yace ya gama komai baya bukatar imel address din.
"Shikenan dama nasan zata birge ka ai, saika dage nima yanzu na dauki hutu ne saboda Angelina batada lafiya"
Habib kashe wayarshi yayi danya gaji dajin fadi ba'a tambaye kaba irin na Sultan.

Kwanciya yayi a saman bed ɗinsa yana lumshe ido, ya dauki lokaci kafin ya saki wani kayataccen murmushi yana tashi tareda lalubo wayarshi.
Wayar mommy ya Kira saida ta kusa katsewa sannan ta daga Muryar ta babu yabo ba fallasa.

Lokacin jiddah na zaune ta jingina da pillow,, tunda taga mommy ta daga waya babu fara'a ta mayar da hankalnta kan mommy.

"Mommy barka da dare" Habib yace.
"Ka sauka lafiya ko"? Mommy bta Tambaye shi.
"Eh mommy alhammdlilh"
"Masha Allah, saika dage da abinda kaje yi"

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now