39

2K 112 13
                                    

🌹🌹🌹
        *_DR. HABIBULLAH_*


ŋą
ąɱɛɛŋą ɱųʂą✍
*🌹ʄıγʂɬ ιąɖყ🌹*

*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*

*{fírѕt lαdч'n kαínuwα}*

{39}


Jinta tayi a jikin bango hakan yasa ta buɗe idanuwanta da sauri, saidai a tsaye ta ganshi ya kafe ta da mayatattun idanuwan shi masu rikita ta...
Saurin yin kasa da kanta tayi jin wani abu na taso mata game dashi..
"Ɗago idanuwanki ki kalle ni sannan ki sake maimaita kalmar bakya san sake zama dani"! Ya katse mata tunanin ta..
Da sauri ta ɗago kanta saidai takasa kallan kwayar idanuwan shi hakan yasa ta kalli gefe..
Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice cikin sassarfa..

Ajiyar zuciya tayi sannan ta zauna a gefen gadon ta hawaye na zubo mata wanda batasan kona menene ba, tabbas tasan karya takeyi tace batasan Habib dan shi ne mutum na farko da zuciyarta ta tsumu da tunanin shi tun kafin idanuwanta su ganshi tana san Habib irin soyayyar da bazata iya fasalta shiba saidai bazata juri irin wulakancin dayake yi mataba dole ta nemawa kanta yanci koda hakan zai sa ta sallama farin cikin ta to amma tayaya zata jure rabuwa dashi ɗin anya kuwa zuciyarta zata iya karbar wannan hukuncin".. rashin samun amsar tane yasa ta rufe idanuwanta tana hasko Habib a zuciyarta..

Habibullah kuwa daran yau gaba daya sam bacci baiyi nasarar sace shiba, gaba daya tunanin jiddah yau yayi "tayaya zai iya rabuwa da ita, meyasa yakejin zuciyarshi bazata iya rabuwa da itaba, meyasa yake jinta a jinin jikin sa"..! Da wannan tunanin sai sallar asuba yaji ana kira, baiyi mamaki ba danshi dama ƙaguwa yayi safiyar tayi..
Alwala yayi sannan yayi nafila ya dade a zaune kan mat sannan ya fice masallaci jin ana kiran sallar shiga....

Wanka yayi ya shirya cikin kyakkyawar shiga ya nufi wajan mommy, a palour ya same su itada Abdul yana shiga Abdul yayo kanshi da gudu..
"My boy harka tashi"! Ya faɗa yana kama hannun shi suka koma wajan mommyn..
"Good morning momma"!
"Morning too, har zaka fita'.
"Eh" ya bata amsa a takaice..
"Ka wuce da jiddah dan Yakamata hibban ya huta haka"!
Shiru yayi sannan ya nemi waje ya zauna kawai, fitowar jiddan ne yasa ya dan daga kai ya kalle ta sannan ya yaci gaba da danna wayarsa..
Tana ganin shi tayi saurin nutsuwa sannan ta gaida mommy ta juya ta gaida shi..
Lafiya" kawai yace sannan ya fice yana faɗin "ki sameni a mota"!

da mamaki ta kalli mommy "mommy shine zai kaini"?
"Eh nice nace ya kaiki"
Handbag ɗinta ta dauka sannan ta fice dan tasan bayasan jira..
A zaune ta same shi cikin motar ita kawai yake jira, tana shiga ya tayar  da motar suka fice..
A wani shopping na saida drinks ya tsaya, bai wani dade ba ya fito rike da wata ƙatuwar leda, kallo daya tayi masa ta waigar da kanta gefe, shima baiyi wata magana ba yaci gaba da driving ɗinsa batareda ya kalli inda take ba..
Har sukaje makarantar babu wanda yayi magana sai picking call kawai da yayi..
Yana gama Parking ta buɗe motar ta fice taku daya tayi taji yace "Wait"..!
Tsayawa tayi sannan ta juyo tana kallanshi, zagayo wa yayi rike leda a hannun shi da alamar wacce ya tsaya yayi shopping ce..
Miko mata yayi batare da yayi magana sai kafe ta da ido yayi yana kallanta alamar ta karba..
Amsa tayi cikeda da mamaki a ranta dan bata taɓa tunanin ita ya tsaya siyawa ba..
"Nawa ne"? Ta tambaya tana san gasgatawa..
"Eh, yayi sanyi da yawa ki bari yadan huce sannan kisha" ya faɗa yana juyawa zai tafi..
"Amma..naga kaima bakaci komaiba".
Cak ya tsaya jin Maganar tata saidai bai jiyoba, baiyi tunanin ta damu dashi haka ba, wani murmushi yayi wanda har saida ya fitar da sauti sannan ya juyo yana kallan ta.
"Eh banci ba, kin damu da hakan ne"!?
"A'a ban wani damu ba saidai Yakamata ka nemi wani abu kaci kaima"
Dan tsuke fuska yayi dan yaji haushin amsar Tata sannan yace "I'm full" ya faɗa yana juyawa..
Harya kama handle din motar ya rike saidai jin Maganar ta yasa ya sake tsayawa cikeda tsananin mamaki...
"Mene"! Ya tambaye ta yana sake kafe ta da wani irin kallo wanda ke sake rikita ta.
"Eh nace nima bazan ciba idan bazakaci ba"! Ga mamakin ta saita ga yana murmushi tare da kallan gefe yana wani motsa baki zaiyi Magana..
Takowa yayi har kusa da ita sannan ya zura hannuwanshi cikin aljihu ya kalle fuskarta..
"Shikenan saiki zubar tunda bazaki ci ba".. yana faɗa ya juya ya shiga Mota ya barta a wajan tsaye..

Cikeda jin haushin kanta tace "to maye nawa a ciki dana nuna na damu dashi karma yaci mana, gashi nan ya wulakanta Ni a Banza".! Tayi tsaki tabar wajan saidai har zuciyarta taji dadin hakan..

Tuki yake yi fuskar nan ba yabo ba fallasa, saidai kallo daya zakayi masa ka gane yana cikin farin ciki..
"Ashe ta damu dani" ya tambayi kanshi yana lumshe idanuwan shi..
Sam ya kasa yarda da abubuwan dayake tunanin dan wannan abun daya shiga tsakaninsu daga daran jiya zuwa yau yakasa yadda dashi ji yakeyi kamar bashi ba zafin kanshi duk ya ragu..

Gaba ɗaya yau jinshi kanshi yakeyi kamar bashi ba, har mutanan wajan aikinsa sun fahimci hakan har tsokanar shi Ameenu yayi amma bai kula shiba sai haɗe fuska yayi yace "shut up and get out"
Sum sum Ameenu ya fice ganin ya dawo Dr Habibullah dinshi lokaci guda..
Lokaci zuwa lokaci yake kallan Watch ɗinsa, Sam bayaso ya makara wajan dauko ta..
Message ya tura akan ta jira shi zaizo ɗaukan ta idan sun tashi..

Lokacin tana zaune a capteria duk da ba abinci take ci ba tunani ne fal zuciyarta akan Habib..
Tana cikin tunanin ne taji karar shigowar message, ganin sakon yasa ta saki wani kayataccen murmushi tabbas yanzu ta yarda da soyayyar Habib ta gama rike mata zuciya kamar yadda ta lura shima ya fara canzawa..




*hαppч nєw чєαr*❣

1/1/2020
{wєdnєѕdαч }

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now