43

1.8K 131 25
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

    🌹🌹🌹🌹
       *_DR. HABIBULLAH_*
                            🌹🌹🌹🌹

вч
ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*

              *wαttpαd*
      Ameenafirstladyy

{43}

...... mommy har zata kai masa da kanta sai kuma ta nufi ɗakin jiddah..
a kwance ta sameta idanuwanta a rufe, jin an buɗe dakin tane yasa ta buɗe idanuwanta ta ɗago kanta.
"jiddah lafiya kike kuwa"!?
"eh mommy na gaji ne kawai"
"to tashi ki kawai Habib coffee saiki bashi magungunan shi daga nan, Ni zanje na gyara dakina"!
dan sauya fuska tayi tace"wlhy mommy bazan iya da masifar wannan mutumin ba"
dariya mommy tayi tace "babu abinda zai miki wanda bashida lafiya ina yaga ta faɗa"!
kamar zata sakeyin magana sai kuma ta amsa ta fice daga ɗakin..

a hankali ta shiga palourn tana bin ko ina da kallo, ganin baya palourn ne yasa ta wuce ɗakinshi saidai kasa shiga tayi tana dan tsorace dan har yanzu da sauran tsoran shi da take ji Musamman data san itace silar accident din nashi.
kasa ƙasa tayi sallama dan ta tabbatar bazaiji sallamar Tata ba, a kwance ta hange shi ya dafe kai da lafiyayyan hannun shi, ɗan ɗaga murya tayi ta sakeyin sallamar..

ƙasa ƙasa shima ya amsa sannan ya tashi yana kallanta duk da tayi kasa da kanta, har tazo kan Centre table ɗin kusa da bed ɗinsa ta ajiye sannan ta ɗago kai suka haɗa yayi saurin kawar da kanshi gefe yana ɗan tsuke fuska.
"gashi mommy tace kasha sannan na baka magungunan ka"!
banza yayi mata kamar baisan akwai mutum a kusa dashi ba.
ganin haka yasa jiddah ta kwantar da murya tace "dan Allah yaya Habib kayi hakuri, nasan nayi laifi amma wlhy ba abinda na faɗa maka bane a zuciyata kawai a hanya muka haɗu ya rage min hanya amma babu wata soyayya tsakani na dashi"
saida ta gama sannan taji ya sauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanuwanshi baice komaiba ya fara sipping coffee ɗinshi harya gama sannan ta dauko magungunan tana bashi yana sha harya gama tas. sannan ta tashi zata tafi, ji tayi ya riko hannunta ta baya, jiyowa tayi tana kallanshi tareda daga masa gira tana kallan hannun nasu.
kamar mai koyon magana yace ta zauna.
batayi masa musu ba tazauna tana cigaba da kallan shi.
"wannan kallan fa, na mene"!
"nasan sanin dalilin hanani tafiya mana"
taɓe baki taga yayi sannan yace "a bayanai da kikayi na fahimci kema kina sona wani dalilin ki mara amfani shine ya hanaki faɗa wa mommy matsayi na a wajan ki ko"? ya tambaye ta yana kallan kwayar idanta.
"ni banida wani dalili, kuma ai bakaji nace ina sanka da bakina ba ko"! ta karasa tana haɗe fuska tare da kawar da kanta.
murmushi yayi har saida taji sautin fitar shi, kamar bazaiyi magana ba taji yace "amma nasan kema kina bukatar wani a tare dake, shiyasa har kika kasa hakuri kike so na sake ki ki auri wani, koba haka bane "? ya sake jefa mata tambayar yana wani shu'umin murmushi..

da sauri tace "banajin wani abu ni, dan zan iya karasa rayuwa ta ba tareda na nemi wani da namiji ba..."

maƙale kafaɗa yayi yace "shikenan tunda haka kikace bari na tabbatar da gaskiya kika faɗa.."!
tashi tayi zata gudu taji ya fizgo da ƙarfi, mutsu mutsu ta shiga yi dan kwatar kanta amma ko gezau hannunsa baiyi ba, kamar jira yake yake ta buɗe baki zatayi Magana saiji tayi ya haɗe bakin su waje ɗaya..
wani zazzafan kiss yake yi mata kamar zai cinye bakin gaba daya, duk yadda taso ya sake ki yayi, tun tana kokarin kwantar kanta har saida ta gaji ta hakura.

Habib kuwa tuni ya fara nisa, dayake Gwarzo ne wajan iya abin tuni ta fara mayar masa da martani suka cigaba da aikawa da juna sakwanni..
sunyi nisa sosai harya fara zarce wa da romancing yaji karar wayar shi.
zare jikin shi yayi daga nata yana maida numfashi idanuwan shi duk sunyi ja, jiddah kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin kunyar biye mai da tayi.
cikin husky voice taji yace "yanzu na gano gaskiyar"!.. jin an sake kiranshi ne yasa ya matsa yana daga wayar ganin mommy ce.
dakyar ya iya saita kanshi ya daga wayar.
"Habib ina jiddah ne tun ɗazu bata dawo ba.."!
"gata nan tana dan dafa min ruwan zafi ne, zan gasa jikina saboda ko motsi nakasa yi"
"ok tayi hanzari ta dawo to"!
"ok Mom" yayi saurin ajiye wayar jin tana ta kokarin fizge hannun ta.
"an faɗa miki nidin rago ne da zaki iya kwace wa a hannun na"
"dan Allah yaya Habibullah ka sakemin hannu na tafi"
murmushi yayi yace "yau ai anan zaki kwana, better for you kawai ki nutsu ma yarinya"
ganin da gaske yake bazai barta tafi ba tace "shikenan naji amma kasan me zaka fadawa mommy da safe"!
kallan fuskarta yayi ya danyi murmushi yace "naji,"
"to sakemin hannu nayo wanka"
sam bai kawo guduwa zatayi ba yana sakinta tayi hanyar fita da gudu, sannan ya leko yanayi masa gwalo yana daga Kafa ta sa gudu tabar ɗakin yana jiyo rufe palourn shi datayi.
dariya ta bashi ganin yadda take cin uban gudu kamar zata tashi sama, saida ya gama murmushin shi sannan ya tashi ya shiga wanka cikeda farin ciki..

a firgice ta shiga palour, mommy na ganinta tace "keda waye kike gudu haka, "mommy kin sanni da tsoro"
"shine kike wannan gudun, ta faɗa tana dan nazarin jiddan"
"eh wlhy, ji nake kamar an biyo NI"! tana faɗa ta wuce ɗakin ta dan ta lura da irin kallan da mommy keyi mata..

sai wajan 8:00am jiddah ta tashi, dan sosai yau bacci yaki sakin ta, da sauri sauri take shirya wa tana gamawa ta dauko jakarta ta fito palour.
kai tsaye dining room ta shiga, yana zaune cikin wani ligt blue na yadi mai shegen taushi gaba daya dakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, cak ta tsaya takasa ƙarasawa kusa dashi, bai kula da ita ba saida ya ɗago ya ganta takasa karasowa.
harya buɗe baki zaiyi magana mommy ta shigo, "ya kika tsaya anan, lokaci fa ya kure zakiyi asarar lecture ta farko"!

"umm kyaleta mommy, may be wani abu take tunawa take tsoron kar a maimaita" yayi maganar shi hankali kwance.
"wanne abu Kenan" mommy ta tambaye shi.
"ina nufin may be tana tunani kar tayi  asarar text ɗin da zatayi irin na wancan satin"!
"ok to kinji saikiyi saurin kammalawa ki wuce".
Habib yagama ba jiddah mamaki, saiya yanko magana ta wayance dayin karya, sam yanzu yagama sauyawa halayen sa sun canja sosai ba kamar da ba mommy kuwa saurin yadda takeyi dan tasan Habib bai iya tsara zance ba.
kuma abinda yafi bata mamaki ko alamun sakin fuska babu a tare dashi fuskan nashi a haɗe ta yadda dole mommy ta yadda da maganar shi.
zama tayi kawai tafara cin abincin, kasa ƙasa yayi da kanshi saitin kunnen ta yace "kin gama gudun yanzu kuma gamu tare" yana faɗa ya tashi ya fice palour.

*Kuyimin afwa readers rashin yin typing dina inada babban dalilin shiyasa amma yanzu komai yayi dai dai, na dawo da hot ɗina😀😛😛*

Maman hajiya
shamsiyya mamman
Maman hmy
fathema abdull dnj
firdausi daughter
Kuna Raina a kowanne lokaci 🌹🌹

*First lady*

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now