25

1.7K 115 11
                                    

🌹🌹🌹
              *_DR. HABIBULLAH_*
                             🌹🌹🌹

вч
*🌹fírѕt lαdч🌹*

*ⓒ* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ

             *wαttpαd*
      @Ameenafirstladyy

25

.....Zaune take gaban doctor bayan ya gama koro mata bayanin yanayin yadda abin yake, sannan ta nisa tana kallan dan dattijon wanda jin dadi ya ratsa shi da alamu..
"Pls nidai doctor koma yane ina so a cire shi"!
"Gaskiya hajiya akwai haɗari babba saboda cikin ya fara kwari za'a iya samun matsala babba inaga kawai ki hakura" ya karasa maganar yana kallan face ɗinta.
Cikin yanayin damuwa tace "Yanzu babu yadda za'a yi kenan"!
Make kafada docton yayi sannan yace "akwai mana idan kikace kinaso ayi kin amince zaki dauki kowanne irin matsala idan ta biyo baya"!
Da sauri tace eh doctor ayi inshallah babu wata matsala da za'a samu by God grace..
"Shikenan ki dawo next week zanyi Miki allura tareda magani wanda zaki sha"
"Ok thank you doctor" tace tana tashi bayan ya faɗa mata payment din...

Jiddah cikeda farin ciki ta koma gida hankali kwance babu wanda ta faɗawa saidai mommy ta lura ta dan rage damuwa kwana biyu..

*Russia*

Sultan ne dake gefe a zaune cikeda mamaki yake kallan Habib wanda yake hada kaya cikin nutsuwa fuskar tashi wasai,, "wai man da gaske kake yi tafiya zakayi"!
Ɗago eye ball dinsa yayi ya kalli Sultan batareda yace komai ba, saida ya gama abinda yake tsaf sannan ya zauna ya fuskanci Sultan ɗin da mamaki ya gama kamashi..
"Sultan bazaka gane yadda nake ji a zuciya taba, Saboda haka dole na koma na nawa matata da yarona kulawa ta.."
"Amma karatun naka fa"
Kallan Sultan ya sakeyi na tsawon wasu sakanni kamar mai tuna wani abu, sannan yayi ajiyar zuciya yace "nima bansani ba"
"Kamar ya baka sani ba kana nufin bazaka dawo ba"?
Cikin ƙosawa da tambayoyin da Sultan yake masa ya danyi tsaki yace "banida tabbacin zan dawo ko a'a, koda na dawo ma zan karasa makaranta ta kamar yadda na fara"
Jinjina kai Sultan yayi dan yasan tsarin makarantar da Habib keyi ba irin sauran Makarantun gida Nigeria bane shiyasa yakesan ya tafi dan yasan bashida wata matsala ta ɓangaran karatun nashi..
"Shikenan yaushe zakayi tafiyar"?
"Next week inshallah"
"Amma shine ka hada kaya tun yau" Sultan ya faɗa yana dariya tsokana.
Shiru Habib yayi dan ya gaji da ba Sultan amsa kuma yasan ko zasu kwana bazai gaji da tambayar shi abubuwa ba.
Sultan ne yaci gaba da surutun shi saidai sam Habib ba kula shi yake ba, cikin jin haushi Sultan ya tashi yana faɗin "nifa kaga abin dayake hadani dakai, kaga nina tafi wajan matata muyi hirar" Sultan ya faɗa yana ficewa..
"Mata"? Habib ya maimaita kamar baisan me kalmar take nufi ba,,,
Wani murmushi yayi tareda lumshe sexy eyes ɗinsa Sannan ya lashi lips ɗinsa. "Ohhh next week come quickly"!!! Ya faɗa yana daɗa lumshe ido,,,,,,

"Jiddah lunch is ready, tashi muje kici abinci" mommy ta faɗa tana kallan jiddah dake cin biscuit tun ɗazu.
Yamitsa fuska ta ɗanyi "a'a mommy I'm full"
"Da kika ci me"? Mommy ta Tambaye cikin nuna kulawa.
"Biscuit"
"Banasan shashanci tashi ki wuce muje kar ranki ya ɓaci"
Dariya jiddah tayi tana tashi da sauri ta nufi dining room.
"Waike jiddah ko nauyin jikin ki bakyaji ne, bana hanaki irin wannan tashin ba.."!
Jiddah da har takai bakin shiga ta tsaya tana langabe kai "sorry momma bazan sake ba"
"Kima sake mana"..

Tare suka zauna saidai jiddah takasa taba komai a wajan sai mommy ce tayi saving ɗinta cikeda kulawa sannan ta Turo mata plate din abinci"
Jiddah kamar tayi kuka dan tasan kotaci ma ba zama zaiyi ba,, kallanta mommy tayi tace "eat Mana"
"Allah mommy zuciyata ma harta fara tashi sam banasan wannan abincin"
"Shikenan me kikeso sai a dafa miki"
"A'a mommy bari na gwada cin wannan ɗin""
A hankali ta fara ci saidai loman ta uku ta tashi da dan gudunta ta nufi bathroom din wajan,,
Cikeda tausayinta mommy suka koma palour, dan itama mommyn har abincin ya fita a kanta saboda bakaramin so mommy kewa jiddah ba shiyasa ko zazzaɓi jiddah keyi hankali mommy tashi yake sosai ballantana yanzu da ko abincin kirki bata iya ci duk ta dan rame..
Hawaye ne suka zubowa jiddah masu zafi da tuna irin tsanar da Habib yayi mata harta kai yabi mata ta karfi amma sai gashi dalilin hakan tana dauke da cikin shi,..
Ɗagota daga kan cinyarta mommy tayi tana share mata hawayen, "jiddah banaso naga kina kuka kin sani, yanzu kuma kukan na mene bayan kinsan kowacce mai ciki hakuri takeyi ko kinaso hankalina ya tashi ne"
Girgiza kai tayi tana dada zubar da hawaye,, "a'a mommy banaso hankalin ki ya tashi, saidai ina tsoron yaya Habib mommy baya Sona tayaya zai so abinda ke cikina ki duba fa irin abubuwan da tayimin kafin barinshi kasar nan, nasan kashe nine kawai bazaiyi ba idan yaji wannan maganar"
Da sauri mommy ta girgiza mata kai "a'a waya faɗa miki Habib yaji dadin Wannan maganar sosai ma kuwa saidai yace ranki zai ɓaci idan bakyacin wani abin kirki"!
Dan murmushi tayi kawai danta nunawa mommy ta yarda amma har zuciyarta tasan mommy kawai faɗa tayi dan karta tayar mata da hankali.
Tayaya ma zata yarda bayan tasan waye Habibullah mutum mai san zuciyarshi da mugunta da wulakanci iri iri...
Suna nan zaune har bacci ya dauke jiddah sannan mommy ta gyara mata kwanciyarta..

Yanzu jiddah tagama Shirin komai kuma ko mommy Bata faɗawa ba, school kuwa yanzu ko fashi batayi kullum saita je,..
Habib da Afnan kuwa sai tattalin nasu cikin sukeyi Gwanin sha'awa haka rayuwar su take tafiya,,.

Next week

Jibi ne takama jiddah zata koma hospital Kamar yadda doctor yace mata shiyasa tun yau ta tsarawa kanta yadda zataje batareda kowa ya sani ba danta kudurta a ranta dole ma ta rabu da cikin ko zata rasa Rayuwar ta saita zubar data fuskanci wulakancin Habib..

.........      ........

Habib kuwa ya gama shirin tafiyar shi tsaff yau, sai dare sannan ya kira mommy Wanda yake da tabbacin bata tareda jiddah saboda yasan Nigeria yanzu dare ne sosai..
Cikin alamun bacci Mommy ta daga Kiran ganin Habib ne batayi wani mamaki ba tunda tasan halin shi,, shi juyayyan mutum ne..
"Lafiya kuwa Habib"? Mommy ta jefa masa tambaya bayan ta amsa sallamar shi.
"I'm sorry momma, gobe zan dawo inshallah that's why I called you"
"Cikin mamaki mommy tace gobe kuma Habib"?
"Yes mommy pls don't no"
"Shikenan wanne lokaci zaka sauka"
"By 6pm Flight dinmu zai sauka"
"Shikenan Allah ya kaimu"
Ameen yace tareda katse wayar tashi..
Suna gama wayar mommy taci gaba da baccin ta, koda safe har jiddah ta fita school mommy Bata fito ba shiyasa jiddah batasan zancan ba,..

Mommy na saukowa down stairs ta Kira Hibban ta sanar masa da dawowar Habib saboda haka ya kawo masu gyara gidan tunda ka'idar Habib dole sai an sauya komai na part ɗinsa kafin ya dawo..

Ba bata lokaci hibban yazo da ma'aikata suka fara aikin su cikin kankanin lokaci...

Sai 3pm jiddah ta dawo duk a gajiye, Bata kula da masu aikin ba ta shiga ga palour tana cire mayafinta.
"Wash mommy I'm tired"
"Sannu da hanya"
Kallan mommy tayi da mamaki ganin an sauya musu tsarin palourn nasu.
"Mommy badai kece kikayi wannan aikin ba"
Murmushi mommy tayi sannan tace "baki kula da masu aiki bane, yau da yamma  Flight dinsu Habib zai sauka kinsan halin shi da tsafta bayasan ya dawo ya samu komai yadda ya barshi"
Tunda mommy tafara Magana gaban jiddah yayi mummunan faduwa cikinta ya hatsina shikenan tashiga uku gashi gobe ne sukayi da doctor zataje Yaya kenan..
"Yadai jiddah, na faɗa miki wlhy wannan shegen tsoron naki shine yasa Habib yake dada ganin kamar bakida gaskiya akan komai"
Murmushi jiddah ta ƙaƙalo sannan tace "to momma zan kiyaye barina shiga na watsa ruwa" bata jira amsar mommy ba ta wuce ciki da sauri..
Tana rufi kofar dakin nata ta jingina tareda sakin wani ajiyar zuciya, "bazan taɓa fasa abinda nayi niyya ba" ta faɗa tana karasawa jikin bed ɗinta..

ғᴏʟʟᴏᴡ  ᴏɴ ᴡᴀᴛᴛᴘᴀᴅ ᴘʟs

ᴍᴏʀᴇ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ᴍᴏʀᴇ ᴛʏᴘɪɴɢ✍🏻

ᴛᴀᴋᴜ ᴄᴇ
*ᶠᴵᴿˢᵀ ᴸᴬᴰᵞ*🌹✍🏻

DR. HABIBULLAHWhere stories live. Discover now