👸👸QUEEN FARHA👸matar sarki👸👸

3.3K 128 8
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzah*

www.fauzahtasiu41@gmail.com



🅿1⃣1⃣


Sannu² lkc yake tafiya cike da abubuwa kala² na dadi da sabanin haka lamarin Farha da mijinta sai son barka inda bangarenta da abokiyar zamanta abin baa cewa komai kullum cikin bala'i suke duk yanda Farha takai da kawaicinta dason ganin batayi abinda zai zama bacin ran Mijin nasu ba abin yaci tura ita Farha tunda suka dawo batada gurin zuwa tana part dinta saboda jikinta da yayi mata nauyi saidai qannan mijin nata su shigo mata, sunsha bikin Aminiyarta da yan uwanta duk wani abu da akayi a wajen bikin itace tayi Mai martaba shine yayi mawa yan uwanta duk wani abu da uba yakeyiwa yaya wannan abu ba qaramin martaba da qaunarsa ya qara a zuciyar Farha ba.

Lkcn da cikinta ya shiga watan haihuwa ya hanata fita ko ina a gdan sarautar komai da ake buqata ya siya wani siyayyar harda ta shirme abinda ya qara tunzura Amnah da uwarta Sogiji a gefe guda kuma Waziri Iliyasu shima hankalinsa ba qaramin tashi yayi ba lkcn da yaji labarin samuwar cikin na matar Sarki Hafeez nan fah kowa ya baje qullin mugun nufinsa akan Farha da abinda ke cikinta.

Yau da sassafe Amnah ta tashi kasancewar a bangarenta yake ta shirya cikin kwalliyar data dade batayi irinta ba ta nufi dakinsa yana kwance yana chart da sahibarsa Farha ta shigo ta jima tsaye a kansa kafin ya ankara ya dago ya kalleta taji ciwon ganinsa yana abinda ta tsana amma dake tatace ta kawota sai tayi ajiyar zuciya tace “dama nazo na fada maka zanje taaziyya gdansu qawata Zahra ne” haka kawai yaji gabansa ya fadi ya ajiye wayar ya kafeta da ido yanason gano gskyrta kafin yace “amma baki fadamin ba sai yanzu” ajiyar zuciya tayi tace “ka manta kawai Mai martaba abunne yazomin bakatatan don Allah karka cemin aa” tabe baki yayi yace “shikenan saikin dawo hanu ta miqa masa yasan me take nufi don haka ya nuna mata inda kudin suke dama hakan takeso ta wucce gurin ta bude ta dauki raffers ta dubu dubu guda uku ta jefa a jaka ta fice tana wani murmushi na mugunta daganan bangaran Hajiya Sogiji ta nufa ta tarar da ita ta shirya tsaf suka dauki hanya zuwa wani qauyen Bauchi gurin surquqine sosai dole sai parking sukayi suka nufi cikin jejin a qafa, suna zuwa gurin gaban Amnah ya fadi suka kutsa suka shiga wani mutum ne yana zaune tumbur babu komai a jikinsa sai wani dan kamfai suka zauna ya dubesu yana wani murmushi yace “musan da zuwanku dama an sanar damu mugun nufinku  matsala ce akan kishiyarki da take dauke da ciki haihuwa ko yau ko gobe to mun duba mun gano cewa tabbas gobe zata haihu zata haifi da namiji babu makawa dannan saiya taka doron qasa”

Dagowa Gimbiya Amnah tayi tace “na shiga uku na boka ka taimakeni wlh idan yarinyar nan ta haihu a gdannan na kadai ni ko kasheta ma ya kama ayi ita da tsinannan cikin dake jikinta” Hajiya Sogiji ce ta cafe da cewa “boka ko nawane zamu biyaka a lalata rayuwar Sarki Hafeez da shegiyar matarnan tasa a kashe dan da yake kumbura kai zai samu kowa ya huta”
daga mata hanu yayi ya shiga surkullensa dagowa ya kumayi yace “zamu batar da ita a zuwa safiya duk rintsi bazata haihu a cikin gdannan ba” wata laya ya dauko yayi surkullensa ya miqawa Amnah yace “kisan duk yanda zakiyi ki binne wannan a inda kikasan Mijinku zai tsallaka  wannan kuma garin mantau ne ki batashi ta kowacce hanya taci duk wani abu daya shafi garin Bauchi zai goge a kwakwalwar ta sauran bayanin zaki gani da idanunki” yana gama yi musu bayani suka sauke masa damman nairori a matsayin tukuicin aikinsa suka tafi shikuma ya duqufa nasa aikin.

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now