👸👸 QUEEN FARH👸👸👸Matar Sarki 👸

3.8K 163 9
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzah*


🅿2⃣

Dariya sosai takeyi har suka gifta qofar fadar sannan suka rabu kowacce ta nufi gdansu da sallamarta ta shiga gdan tana qwalawa iyayenta Kira fadi take “Ummah Mamah albishirinku yaudai banyi tsokana ba nifa dama na fada muku yarannan Rahmah da Rahina su daina bina sune karfofi idan muka fita dasu sai sunsa na raba hali a titi amma kuma sheg...” hadiye mgnr tayi muqut saboda ganin fitowar  mutumin da suka rabu dazu dashi a qofar makarantarsu da Baffanta daga turakar Baffan tsugunawa tayi tana gaida Baffa ya amsa da cewa “ uwata sarkin rikici duniyama tsoronki take ya karatun ” sosa hancinta tayi tana harararsa tace“to qlau amma wlh dukan da Yaya Anass yayimin jiya ya shigeni kuma bazan yafe...” sake hadiye mgnr tayi saboda kallon da taga Baffa yana watsa mata ta miqe tana dariya tace.

“Kayy Baffa irin wannan harara haka muje na rakaka ka raka baqon naka amma Allah Baffa ya fiye shisshigi da shiga sharo ba shanu nidai garama mutum ya fita daga rayuwata idan ba hakaba nidai kowa yasan ni aljana ce ehee” ba Baffa hatta Mai martaba HAFEEZ saida ya dara duka Baffan yakai mata yace “kajimin ja'irar yarinya wato dole sai kin qarasa shirmenki ko zaki bacemin daganan kosai na canza miki kamanni” daki ta shige tana turo baki binta yayi da ido harta shige dakin yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinya qarama amma tana neman hana zuciyarsa kwanciyar hankali.

Suna fita sukayi sallama daidai lkcn driven sa da excourt dinsa suka iso suka buda masa ya shiga suka tafi. Juyawa Baffa yayi ya shiga gdan ya fara dokawa matansa kira fitowa sukayi da sauri suka isa inda mijin nasu yake, kujera yaja yar tsuguno ya zauna yana sharce gumi yace “akwai matsala Hajara da Inno tabbas akwai matsala FARHANAH ta debo ruwan dafa kanta da babu mai hanashi dafata sai Allah Mai martaba sarki Hafeez yazomin da wani rikitaccen al'amari wai auran FARHA yake nema kuma cikin sati daya tak” dagowa sukayi dukkansu sukace “Farha fah kace Baffan yara wannan shashashar yarinyar zaice yanason aure haba Baffa to kai kuma me kace masa?” qara share zufa yayi yace “to me kuke tunanin zance mawa wannan taqadirin isasshen sarkin namu ya fahimce ni na fada masa Farha yarinya ce qarama kuma quruciyarta da gyara tanada rawar kai yace shi yaji yagani kuma yanaso shima rainonta zaiyi harta hada hankalinta duk da haka na kuma nuna masa rashin amincewata qarshe sai yacemin nayi hqr kawai auransa da Farha rubutaccen Al'amari ne saboda haka nayi fatan alkhairi kawai”

Shiru gurin ya dauka cike da mamaki a fuskar kowanne Ummah ce tace “nidai gsky wannan lamari ban amince dashi ba dama Rahmah yace ko Rahina sunfi wannan dukan taran hankali amma ace wai Farha ce matar sarki Hafeez gsky akwai matsala babba saboda ni nafi tunanin auran ma na manufa ne badon Allah zaayishi ba” Mama ce ta cafe da cewa “ to yanzu maye mafita kunsan dai tunda ya tako qafa da qafa yazo gdannan bai dauki abin da wasa ba kuma babu abinda zai fasar da aurannan sabida haka inaga mafita ya kamata mu naima" Baffa ne ya dago yace “to wacce mafita Inno ai kawai haquri zamuyi mu zubawa sarautar Allah ido tunda bamu isa mu kaucewa umarnin sarki ba kodan tsira da mutuncin mu ba abune me wahala a gurinsa ba ya tozarta mutum shiyasa tun mutuwar mahaifinsa Sarki Hambali na ajiye rawani na na shugaban malaman fada saboda shi amma duk da haka ban tsira daga kaidinsa ba saida mulkinsa da ikonsa ya ratso ta gdana bisa jagorancin fitinanniyar yarinyar nan, na tabbata da bata taboshi ba bazai san da zamana ba ni bammasan tsautsayin daya hadasu ba nasan Farhanah ta zama gawa ta gama”

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now