👸👸 QUEEN FARHA👸matar sarki👸👸

2.9K 124 7
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzah*

www.fauzahtasiu41@gmail.com



🅿1⃣2⃣


Matsowa Momy tayi ta shafa kanta tana zubar da kwallah tace “danki ne  baiwar Allah ki godewa Allah daya saukeki lfy Allah ya raya manashi yayi masa albarka yanzu inane yake miki ciwo?"
Dago idonta tayi ta kalleta har yanzu ruwa ne yake zuba a idonta ta kada kai alamar babu komai ajiyar numfashi sukayi Daddy yace “ alhmdllh tunda babu abinda yake miki ciwo Momy bata abinci taci saita bamu labarinta saboda mu samu ku mayar da ita inda ta fito” kallonsa takeyi kamar wadda ta warke daga ciwon makanta har Momy ta zubo mata abincin ta hado mata tea me kauri Maryam ta karba ta zauna a kusa da ita ta rinqa bata tanasha saida ta shanye tea din tsaf sannan taci faten doyar kadan tace ta qoshi.

Kyaleta Maryam din tayi ta kalleta tace “ya sunanki Aunty?” dago idonta tayi cikin hawaye tace “nidai kamar sunana Farhanah amma bani da tabbas akai?" Kallon Momy Maryam tayi ta share hawayen daya zubo mata tace “anya Momy ba daga Sarcartry ta gudo ba kinji fah sunanta ma bata bambamcewa” girgiza mata kai tayi tace “bari kawai auta lamarinta akwai daure kai kinga fah sarqar wuyanta itace irin wacce muka gani lkcn da mukaje Dubai akace 5  million na fasa siya Maryam wannan ba matar qaramin mutum bace dole akwai wani boyayyen abu ba fitowar lfy bace tashi ki hada mana kaya mu tafi gida mayi mgnr acan”
Miqewa Maryam tayi ta shiga diban kayan tana fita dasu har ta kwashe komai ta karbi babyn ta fita ita kuma Momy ta kama Farha suka fita a hankali har suka isa inda motar take suka shiga suka nufi gda suna zuwa  Momy ta kaita dakinta ta dora ruwan wanka a gas sannan suka shiga gyara mata wani daki wanda yake komai akwai a ciki ba wani babba bane sosai gadone by six sai wadroop ta bango qarama sai tv plasma da qaramin fridge.
Momy ce ta shigo tace “taso yata na gasa miki jikinki kinji haihuwar fari sai an kula sosai” batayi mata musu ba ta tashi tabita toilet din dake wajan gidan babbane sosai tasata ta cire komai na jikinta sai pant kawai ta zaunar da ita saman kujera ta fara gasa mata jikin da ruwan  zafin towel ne babba take mammatsa mata tun tanajin zafin ruwan har ta daina bayan ta gama mata ta zuba mata wani ruwan tace ta shiga ciki a shiga ruwanne sukayi artabu da qyar ta zauna a ciki damma ta hadu da Momyn qaqqarfar gaske da bazata shiga ba.

***      ***      ***      ***   

Sai yamma liqis King Hafeez ya dawo gda kasancewar fitace ta gaggawa sukayi da governor zuwa wata ziyarar aiki tun a gurin yaji gabansa ya tsananta faduwa yana zuwa gdan bangaren Farha ya nufa harda gudu gudunsa yake hadawa ya shiga ya tambayi baiwar dake mata aikin ciki Ina take sunkuyawa tayi tace “wai dama ba tare kuka fita ba ranka ya dade tunda ta karya ban sake ganinta ba tun dazu jiran fitowarta nakeyi" bai jira qarasa mgnrta ba ya nufi daya parlourn yana qwala mata Kira “Queen! Queen!! Kina inane gani na dawo fito kiji jarabawarki ta fito tayi kyau sosai ina tayaki farin ciki dole nayi gifting nak.....” daukewa numfashinsa yayi lkcn daya bude dakin yaga kayanta kaca² tare da akwatunanta duk a wargatse, shiga yayi da sauri yana dube² yana cewa “fito mana matata banason wannan wasan don Allah fito na tayaki gyara kayan nasan duk shirin haihuwa akeyi babyna ya kusa zuwa duniya” zama yayi yana kulle akwatinan yana maidasu inda suke saida ya gama tsaf sannan ya nufi toilet a bushe ya tarar da bathroom din babu alamun an shigeshi nan kusa.
A gigice ya fita ya nufi part din Amnah yana qwala mata Kira “Amnah ke Amnah ina Queen ne ina tace miki ta tafi fadamin” yana mgnr yana banka qofar, a zaune ya ganta tana taunar Chingum shaqota yayi kamar zai kasheta cikin qufula yace “Kina jina ina tambayar ki ina Queen take ne?" Yatsina fuska tayi tace “bansani ba ajiya ka bani ita kome da zakazo kanamin ihun ina wata banzar matarka”

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now