👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸matar sarki👸

3.7K 142 1
                                    

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers.)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzah*

www.fauzahtasiu41@gmail.com


🅿4⃣

02:00pm aka daura auran  3:30pm jerin gwanon motocin daukan amaryar sukazo tare da kawo kayan lefe kayane na gani a fada babu qarya an zuba naira cikin lefen Farha iyakar ganin me kallo bazai iya qididdige adadin kayan dake cikin akwatunan lefen ba sarqoqi kawai da aka zuba mata na gold sunkai bakwai hakanan badan an gama ganiba aka fito da ita sanye cikin  Alqabba milk colour tayi kyau matuqa kamar dama ahlin abun kanta qasa tanata sharbar kukanta wanda ta yini aikinsa Ummah ce ta riqe hannunta har turakar Baffanta ta tsuguna daidai qafarsa tana qarawa kukanta sauti wai don yaji tausayinta yace yafasa aurar da ita, dago kanta yayi da hanunsa yana girgiza mata kai yace.

“Kiyi hqr Farhanah bawai don bama sonki zamu bayar dake a tafi dake ba aa saidon babu yanda zamuyi haka Allah ya tsara mana tun farko kece zaki riga yan uwanki tafiya dakin mijinki Farha banason jayayya da lamarin ubangiji shiyasa na yarda da aurannan naki amma nasan akwai manufa a cikinsa duk da manufarsa ba haramtacciyar manufa bace amma naso ace ba kece wacce kika zama sirrin manufarsa ba kiyi hqr kiyiwa mijinki biyayya kuma ki zauna da kowa lfy kinga dai yanda Allah yayi dake kin taso gdanku daga ke sai yan uwanki da baku zarta shidda ba gaba daya gdanku mutum tara ne yanzu kuma zaki koma babban gda da yake dauke da mutane sama da dari kuma kowanne da halinsa kowanne da iyayensa saboda haka dole ki nutsu ki gyara takunki karkice zaki tafi da shirman nan naki gdan sarauta zakisha wahalar rayuwar cikinsa kuma karkice zaki dauki girman kai da izza irinta makusanta Sarauta zakiyi baqin jini kuma zaki fuskanci wulaqanci da gori ki tsaya iyakar huruminki na mata babu ruwanki da duk wani abu daya shafi sarauta idan kikayi haka zaki zauna lfy da kowa”

Numfashi yaja tare da sakin kanta yace “tashi kije suna jiranki Allah yayi miki albarka ba kareki daga sharri da makircin gdan sarautar garinnan” kama hanunta Ummah ta kumayi ta fita da ita har tsakar gdan ta damqata hanun Jakadiyyah kamo hanun Rahmah tayi ta rungume ta suka fita dukkansu suna kuka, baa dauki wasu mutane da yawaba mutun shidda ne manya sai yan uwanta guda biyu da qawarta Binta suka shiga motocin suka nufi gidan sarautar tun kafin su qarasa ta fara jiyo bushe² da kade² sake lafewa tayi a jikin Rahmah tanaci gaba da rera kukanta Jakadiyyar da tausayin uwar dakin nata ya cikata ta rinqa bata hqr tana lallashinta har suka qarasa batayi shiru ba.

Motocin ne sukayi parking a harabar gdan da yake gari guda kowa ya fito sannan aka bude mata qofar suka fito ita ce qarshen fitowa tana fitowar aka dora saman wata farar godiya sunata kide² su da waqoqinsu har suka isa wata babbar qofa aka bude musu suna shiga bayi da barori sukayita zubewa suna kwasar gaisuwa har suka isa wata qofar nanma aka bude suka shiga sauketa akayi daga kan godiyar  Jakadiyyar ta sake riqe hanunta suka shiga parlourn tare da sallamarsu parlourn cike yake da mutane aka farayi mata marhabin wata mata ce ta taso ta riqo hanun Farhan tanayi mata sannu da zuwa bata gane komai itadai taji anyi qasa da ita ta russuna sai kuma taji an dafa kanta muryar dattijuwa taji tace “barkanki da zuwa gdan nan matsayi matar Mai martaba Hafeez Farhanah Allah yayi muku albarka ki saki jikinki nan gdanku ne ki daukeni kamar mahaifiyarki kiyi duk abinda zakiyi a gdanku nanma gdane kinji, Hajjah ku kaita sauran bangarorin ta gaishesu”

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now