*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻
Writing
And
Story*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH**Wattpad👉🏻* *realfauzah*
www.fauzahtasiu41@gmail.com
🅿1⃣3⃣
Kullum idan ya kalli yaron saiya tunads Prince Hafeez wanda a lkcn suna karatu bashi da abokin daya wucceshi dawowarsu gda 9ja ne yasa abotar tasu tayi baya saboda kowa ya kama abinda yake ganin zai fishsheshi amma duk da haka suna gaisawa sosai cikin yan shekarun nan ne komai yaja musu baya.
Ajiyar numfashi yayi ya kamo Sarki ya dora a cinyarsa tare da jaririyar da aka haifah masa yayi musu hotuna sannan yayiwa sarki shi daya ya turawa Prince Hafeez ta Email dinsa, kiransa yayi a waya ya daga suka gaisa yace “ranka ya dade ka manta damu mulki dadi har yasa ka manta da abokin amana” ajiyar zuciya akayi a daya bangaren yace “ kayi hqr My Nass wlh na rasa nutsuwa ta samada shekara uku ni kaina bansan ya ake wasu abubuwan suke faruwa dani ba ka tayani da addu'a kawai” a gaggauce yace “ya Salam nifa naji shirun tayi yawa yanzu meye dai yake faruwa ne?” jan numfashi yayi yace “yarinyar da nake baka lbrnta samada shekara ashirin ina mafarkin naganta a masarauta ta har munyi aure amma mutu Nasir an tabbatar min ranar da tabar gda motar Jos tahau kuma motar da tahau tayi hatsari babu wanda ya fita a cikinta ciki harda rayuwata Nima saboda wlh itace rayuwata Nima yanzu zaman jiran ajalina nakeyi saboda banida wani amfani a rayuwarnan"Cikin tsananin tausayin abokin nasa yace “Allahu akbar na tausaya maka Hafeez amma babu komai kayi tawakkali ka rungumi qaddararka insha Allah komai zai wucce kasan ita qaddara babu Mai gogeta ita kuma Allah ya gafarta mata yasa matarka ce a aljanna” Shiru ce tadan ratsa kafin Nasir ya kawar da shirun da cewa “akwai wani yaro dan qanwar Momy da yakemin tsananin kama dakai Hafeez wlh duk sanda na kalli yaron saina tunaka yanzu ma ka ganshi a jikina dake anyimin haihuwa ya gudo yabaro gdan Momy ya dawo gdana shima kamar kai yarone qarami da bai wucce shekara uku ba amma shegen son yarane dashi wlh da ace nasan kana neman mata babu abinda zai hana nace kaine uban yaron nan to amma nasan bakayi Allah ne kawai ya sanyaku iri daya” murmushi yayi yace “dama hakane ai turomin hotonsa naganshi don Allah” dariya yayi yace “na tura maka ta Email dazun kana hawa zaka ganshi” haka sukayi sallama suka ajiye wayar.
Yau ta kama rana ta farin ciki kuma Mai muhimmanci a rayuwar Farha ta yanzu saboda yaune ta gama digiri dinta na farko kuma da samu good points hakanne yasa bayan zamansu jiran result ta fara fafutukar ci gaba da kara ita kuwa Maryam tace aa batason wani karatu aure zatayi a lkcn da results dinta ya fito ta samu scholarship a Open University Oxford yan gdansu sunyi murna sosai suka hada mata party me kyau akaci akasha kowa ya watse babu wani bata lkc ta fara karatunta akan matsalar zuciya kuma a wannan lkcn ne aka bude wani babban Asibiti a cikin garin Kaduna me suna ( QUEEN FARHA CONSULTANCY HOSPITAL ) wanda yake mallakin abokin Yaya Nasir Prince Hafeez shiba mazaunin garin Kaduna bane wannan dalilin yasa ya damqa ragamar asibitin a hanun Nasir hakanne yasa aka dauki Farha wadda ta koma Hanah Usman a yanzu a matsayin ma'aikaciyar asibitin ita da Maryam Usman ita Hanah tana bangaren matsalolin zuciya ita kuma Maryam tana bangaren matsalolin mata.
Tana karatunta tana aikinta albashinta me tsoka sosai ganin tana daukan albashi me kyau yasa taso daukewa Daddy wasu daga cikin dawainiyarta data Sarki amma fir yaqi dole ta hqr take serving salery dinta babu abinda takeyi dashi saidan abinda baa rasa ba data tuntubi Yaya Nasir da mgnr tanason daukan nauyin karatun Sarki da kanta sai yake gaya masa ai Suma basu suke dauka ba Abokinsa Prince Hafeez da ne yake daukan nauyin komai na karatunshi, lkcn daya ambaci sunan Hafeez saida taji gabanta ya fadi haka kawai batasan dalili ba.