👸👸 QUEEN FARHA👸matar sarki👸👸

2.8K 113 4
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzah*

www.fauzahtasiu41@gmail.com



🅿2⃣1⃣

Ajiyar numfashi tayi tare da murmushi me nuna farin cikin ta shima murmushin yayi ya sake ruqo hannunta yace “yanzu inane yake miki ciwo me kikeso kici?" Girgiza masa kai tayi alamun babu komai ya sake matsawa jikinta yace “ ok tashi muje ciki na sama miki abinda zakici" bai ida rufe bakinsa ba ya dagota suka fita yana riqe da ita har cikin parlourn ta ya kwantar da ita saman kujera ya nufi kitchen dauko mata cake da youghut ya dawo ya rinqa bata tanaci har taci ya isheta sannan ya dauketa suka shiga bathroom sukayi wanka ita ta kwanta shikuma ya dauki wayarsa ya fita dakinsa.

Tashin farko Abdallah ya kira ya fesa masa ya bawa Momyn sa ajiyar qaninsa ya kuwa saki ihun murna yace “kayimin daidai Dad Ina Momyn take?” murmushi yayi yace tana dakinta tana bacci sai da safe kwa gaisa” sunayin sallama ya kira mutanen Kaduna ya fesa musu suma sunyi murna sosai Maryam tace zatazo taga Farha da ciki itama ta rama tsiyar data rinqa yi mata,
Sunayin sallama ya nufi dakinta lkcn har tayi nisa a baccinta ya haye gadon ya janyota jikinsa ya rinqa shafata har saida yaji alamun ta tashi sannan ya fara aika mata saqonsa tureshi ta farayi tana qunquni yayi saurin hade bakinsu babu yanda ta iya hakanan ta saki jikinta ya samu gamsuwa sosai sannan ya kyaleta sukayi wanka suka koma suka kwanta.

Sannu a hankali cikin Farha ya rinqa girma baya bata wuya amma
Bacci harda na hauka watan cikinta takwas wata ranar lahadi suka wayi gari da mutuwar Hajiya Sogiji duk da ba wata alaqa ce tsakanin Farha da ita ba amma taji mutuwarta sosai shikuwa gogan ko a jikinsa yana dakinsa aka kirashi aka fada masa budar bakinsa cewa yayi “ai gara hakan sun rage mugun iri a family dinsu" kallonsa Farha tayi tace “Haba Mai martaba baa haka fah duk wanda ya riga ya mutu addu'a kawai yake buqata balle ma Hajiya kafin mutuwarta tayi nadama dagani har kai babu wanda bata nema ta roqi ya yafe mata ba kayi mata addu'a shine yafi alkhairi fiye da komai” shafa kanta yayi yace “naji sarkin yafiya nidai ban yafe ba wlh badan darajar yan uwana ba Hasheem da Umaima da bazanje jana'azarta ba meye matarnan batayi min ba tun ina qarami nakeshan wahalar....”

Rufe masa baki tayi tace “naji don Allah muje ni kai wlh ka fiye qorafi to yanzun meye ribarka idan baka yafe mata ba haba Abban Sarki kada kabani kunya don Allah ita guga ko bata tsira dan komai ba ta tsira don igiya tunda bazaka yafe mata don kanta ba ka yafe mata saboda darajar yan uwannaka zasuji dadi sosai kuma kasan ko a lahira wani nacin arzikin wani wlh nidai na yafewa Hajiya duniya da lahira saboda nasan duk abinda ya faru nufi ne na ubangiji kuma qaddarar mu ce sudai kawai sila sukayi”

Tana fadin haka ta juya ta nufi cikin gdan daqyar take daga qafarta saboda nauyin cikin jikinta tana shiga Umaima ta nufota ta rungume ta tana kuka tace “Aunty Farha Hajiya da sunanki ta cika a bakinta tana cewa a kiraki ta qara neman gafararki don Allah ki yafe mata Aunty pl...” rufe mata baki tayi itama tana hawaye ta qarasa gaban gawar ta tsugunna ta ruqo hannunta tana hawaye tana yi mata addu'a a haka King Hafeez yazo ya isheta ya girgiza kai cike da mamakin irin zuciyar Farha me saurin yafiya da mantawa da abubuwan sharri tana tashi aka dauki gawar aka fita da ita nan gdan ya rude da koke² itadai gefe ta koma ta zauna tana sharar kwallah ba komai take tunawa ba sai nasu qarshen a zuciyarta tace “Allah yasa muyi kyakkyawan qarshe wanda zamu mutu ana tuna alkhairin mu tananan zaune har wajen la'asar Hasheem ya shigo yace taje inji Mai martaba daqyar ta miqe wasu mata dake shigowa yanzu suka zuba mata ido suna kallonta itama dayar da tafi kowa lalacewa take kallo wadda take tafiya a shagide hanunta a karkace tason tuna inda ta santa amma ta kasa da haka ta fice ta nufi part dinta tana shiga ta tarar dashi a tsaye a parlourn tana shigowa ya nufota ya hadeta da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya yace.

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now