chapter one

1.8K 47 3
                                    

Tsarin Allah

Na

Aisha Abu turab

A zaune take tana dudduba wasu takardun makarantar ta,aiki take so ta fara nema.zaman nan ya fara isarta kullun banda tunani babu abinda Hindu take.shekarar ta 5 da gama jamia kenan kullun sai zaman shiru da kadaici. Hindu mace ce 'yar shekara 34,gaba daya ita haihur kano ce kuma tashin kano.A kullum ji take kamar ta dawo da hannun agogo baya zuwa wasu shekaru da suka wuce...hmmm ta nisa,yanzu neman aiki da kanshi yake zaune idan ba kafa ce da kai ba.Sallama da Shigowar danta mai shekara tara shi ya dawo da ita daga tunin da take..waalai kumus salam ta amsa masa.Kun taso kenan Ahmad ta fada tana mayar da takardun cikin leda. Eh mama,da akwai abinci ya tambaya eh akwai yi maza ka cire kayan ka dan watsa ruwa sai kaci.A'a dan Allah na dai fara ci tukunna sai nayi wankan To kawai tace masa ya shiga kitchen,bari na zuba maka,kaje ka wanke hannun ka da hand wash.. Ya shiga kitchen ya fara wanke hannun yana bata labari da fara'assa mama kinsan abinda malam yace mu tambayo agida ni kadai na amsa daidai?sai ka godewa Allah tace tana dariya badan Alhaji babba ba da baka Ciba tunda dagani har Abba bamu sani ba.karbi tace tana mika masa abincin kayi maza yamma na kuma yi,yanzu idan ka zauna sai kaji an fara kiran sallar magriba.Haka nan suka zauna su biyu yana cin abinci yana mata 'yan tambayoyi tana eh ko a'a.Duk lokacin da ta kalli Ahmad sai taji dadi aranta tana kuma godewa Allah da ya bata shi.Ahmad bai kasance irin yarannan mara sa fitina ba kuma bai zama mai rigima ba amma akwai zance da tambayoyi.Har kullum addu'a take Allah Ya sashi cikin 'ya'ya nagari masu kishin addinin su.Gani take kamar bata iya tarbiya ba ko kuwa bata isa tayi wa wani tarbiya ba duba da irin abubuwan da tayi shekarun da suka wuce.Allah ka wuce mana gaba tace afili,amin Ahmad ya fada,mama me kike tunani?ba komai kawai tace masa. Da Allah bai sa ta haifi Ahmad ba bata San kuma mai zai faru ba.amma yanzu ko banza tafi karfin a kira ta da juya yadda wasu mara sa ilimi keyi kamar kai kake bawa kanka.Ahmad yana gama cin abinci ya shiga wanka ta ci gaba da 'yan aika ce aika cen ta kafin a kira salla wanda baifi Minti talatin ba. Kamar karfe goma na dare abban Ahmad ya shigo tana ta gyan-gyadi wanda ta fara tun sanda tayi wanka.Karar bude gate din da taji shi ya tashe ta...Da sauri ta mike ta shiga daki don son ta dan kara kintsa wa kafin ya shigo,ta dauki cingam mai dan mint tasa abaki...Yasa key yana kokarin bude kofar sa ta dawo Palo...assalamu alaikummm ya fada yana jan sallamar daga karshe da murmushin sa a fuska.Hindu ta amsa masa tana mai karasa wa gurin sa,ya bude hannun sa ya bata wani babban hug.Ta shige jikinsa da murnan ta tace masa sannu da zuwa yace yauwa maman Ahmad.Har yayi bacci kenan?ya tambaya,tun dazu ma kuwa wai da jiran ka zaiyi amma bacci ya dauke shi anan daker na samu ya kwanta...aiko banji dadi ba,naso tun dazu na dawo wlh ibrahim ya tsayar dani...where is my kiss ya tambaya ta juya ta bashi peck a kumatu yace wannan ai rinto ne kiss nace ba peck ba.Ya samu kujera ya zauna ya jata ta zauna akan cinyar sa ya kara hugging dinta kamar sun dade basu hadu ba sannan yace ya gidan? tace Alhamdulillah bari na kawo maka abinci,A'a bazan samu cin abincinnan ba kinga dare yayi in naci na kwanta bazan ji dadin ciki na ba kiyi hakuri,ba komai kawai tace amma ba taji dadi ba.Bari to na hade abincin nasa a fridge ta fada tana kokarin tashi Ni kuma kafin ki gama bari na shiga na watsa ruwa. Kiran sallan asuba na farko shi ya tashi Farouq mijin Hindu,yayi adduar tashi daga bacci ya kalli gefensa inda matarsa take...yasan bai isa ya tashe ta ba azauna lafiya shi dai azuciyar sa, ya so ace Hindu ta kasance acikin mata masu himma sosai gurin ibada amma sai ya same ta akasin haka, rashin tashin ta sallar asuba acikin halayen Hindu yafi komai damunsa.Ya tuna lokutan da yake tashin ta abaya sai tace ita bai iya tashinta ba firgita ta yake idan ya kira sunan ta da karfi, babu abunda bata fada duk don ya kyaleta haka yana ji sai dai in asuba tayi ya wuce masallaci saboda zaman lafiya kar ransa ya baci tun asuba amma nan bada dade wa ba ya keson yayi maganin abun.Hindu itace mace ta farko daya fara gani yaji ya naso ta zama matarsa wacce zai rinka farka wa kullum yana ganin ta agefen sa... Yayi murmushi da ya tuna lokacin daya ya fara ganin ya;'yar yarinya kyakykyawa fara,ga mayan idanuwa duk da hancin ta ba wani mai tsaho bane amma tana da lips mai kyau.CUTE! Itace kalmar da ya fada lokacin da ya ganta a bikin kanwar sa.Tana ta shan rawa sa'ilin da aka kira kawayen amarya da ganin ta kasan bata da damu wa...duk da ya tsaya a gabanta ya barnatar da kudi gurin lika mata kudi bata ko kalleshi ba balle tasan ya nayi, wannan halin nata shi ya kara jansa gurin son ya santa sosai.Jira kawai yake a tashi yayi wa wannan yarinyat mai kyau magana amma koda aka tashi,sama ko kasa ya neme ta ya rasa...a haka ya koma gida yana tunanin yadda zai kara ganin ta gashi yau an gama biki don kuwa ita kanta amarya daga gidanta tafito dinar..Ya shafi fuskar Hindu da hannunsa ya tashi ya shiga alwala...Karar kofar toilet da ya rufe shi ya tashe ta,ta juya ta kalli inda ya tashi sannan ta juyo tasa hannu bedside drawer ta dau wayar ta taga biyar saura.Alhamdulillah tace azuciyar ta yau dai ta tashi don wallahi ba'a son ranta take sallah da safe ba,ga kuma wani kallo da Farouq yake mata duk lokacin da ta makara.Bari ta jira fitowar sa itama ta shiga,mintuna kadan bacci ya sace ta....

"I'm not perfect"
Username AishaAbuTurab

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now