chapter 6

309 14 1
                                    

**TSARIN ALLAH**

               NA

AISHA ABU TURAB

wattpad AishaAbuTurab

*wannan littafi kirkiranshi akayi,ba'a yishi don kwaikwayo rayuwar wani ko wata ba....

Ban yarda a cenzamin komai ba acikin rubutuna ta ko wacce hanya....

Bismillahir Rahmanir rahim.

A gurin Hindu ta daskare kamar iced fish,tabbas Farouq ya raina ta,wato ita bata da darajar da zai kyautata mata kenan? Baza ta daina tambayar kanta wannan tambayar ba**wai shin Farouq yana sonta kuwa?**

Hirarsu kawai suke da tsohuwar budurwar sa,tace ta gama diploma yanzu business take yi,wane business kike yi? ya tambayeta..pineapple juice take da zobo kuma alhamdulillah tana ciniki,sai yace mata shima zai bada gudumowa,tace a'a ya barshi,irin dai abinnan....Yayi mata transfer na 150k,tana yi masa godiya sannan tace kudin yayi yawa,yace wannan ba komai bane kuma duk lokacin da zata kara shiga wani business din ko za tayi expanding shi zai bata jari.....

Hawaye ne yake ta zuba a idon Hindu wanda ta kasa control dinsa.ita fa wallahi duk kishinta,idan Farouq  zaiyi aure baza ta daga masa hankali ba,amma ya dauki kudi ya bawa budurwa matarsa kuma idan ya bata 1k sai tayi lissafin mai ta siya da kudin?

Yau da ba cikakkiyar budurwa aka kawo ta gidan Farouq ba da sai tace ga dalilin da yasa yake mata haka,kuma dai shi kansa ya tabbata iyayenta dattijen kirki ne don shi dakansa yana yabon su.Basa shigar masa harkar aurensa sannan babu mai kiransa ya sashi yayi abunda baya sonyi kawai don yana auren 'yarsu.ko kuwa hakan da basa yine yasa yake tunanin kamar batada gata?

Duk abunda Hindu za tayi tunani na dalilin halin Farouq tayi amma sam bata gane komai ba,ita dai tasan jajir cewarta gurin ibada ya ragune bayan ta haifi Ahmad,kuma dai kullum akan wannan yake mita,itama so take ta gyara saboda dakan kanta abin yana damun ta...shin wannan dalilin zai hana ya kyautata mata? Sai kusheta da yake yi,komai tayi yace bata iya ba...

Hannu tasa ta goge hawayen da yake ta zuba a idonta,ta cigaba da tunanin daliluka kala-kala wadanda zasu sa Farouq ya mayar da ita shirgi.Idan wayewa ne tana da wayewa tunda tana zama cikin mata masu hali dabam dabam,kuma tasan tana kokari sosai gurin gyara jikinta da muhallin ta....

Tana wadannan tunanin aka kira sallar magrib,ta goge hawayen ta nufi hanyar toilet don yin alwala,duk wasan Hindu,sallah bata wuce ta.

Bayan ta idar ta cigaba da zama akan sallayar,ba wai azkar take ba,dama ba kullum take azkar dinta ba balle yau da tunani yayi mata yawa..har aka kira sallar isha'i tana zaune,tashi tayi ta kabbara sallar kukan ya dawo mata,haka tayi ta sheshsheka har ta idar....kirjinta taji nonon ta yana kara cika irin yadda ake cewa yana nuna alamar danka yana kuka,yau ta manta da Ahmad....ta yanke shawara baza ta zauna da Farouq ba,tun dansu daya kowa ya kama gabansa,shi yaje ya auri wacce yake gani ta kai matsayin ya aureta,itama taje ta auri daidai ita wanda zai ga darajar ta da kima..

Tana wannan kukan taji ana knocking kofa,kamar karta tashi amma saboda tasan duhu ne ko waye ba zaiga fuskarta ba,balle a  gane wane hali take,sai kawai ta mike,ji tayi kanta ya sara,dama dai tasan dole kanta yayi ciwo wannan kuka da tasha haka...

"Waye?"  ta tambaya kafin ta bude.

"Nine". Shine ansar da Farouq ya bata..

Zuciyarta taji ta fara dudubniya a kirjinta,muryarda takeso amma yau bakin cikin saura ranta take.Bude kofar tayi ta juya ta shigewar ta palonta,ta dauki wayarta ta kunno fb,bata da hakurin jiran ya huta kafin suyi maganar,to wane hutu,tunda shima bai bari ta huta ba.Biyota yayi babu walwala a tattare da shi,kullum fargabarta kenan idan ya fita,da wane yanayi zai dawo,amma yau daidai take da koma me yake ji....

" Ya naji gidan shiru?,baki dauko Ahmad ba?" Ya tambaye ta yana haske ta da fitilar wayar sa daya kunna tun shigowar sa,mamaki ne ya kama shi da yaga idonta yayi jazur sannan ga wani hawayen yana bin kuncinta.

"Lafiya naga kina kuka?" ya tamabaye ta hankalinsa atashe.kallanshi tayi akaikaice,da baiyi mata wannan abin ba da ta yarda damuwa ta gani a idonsa amma yanzu babu  abinda yazo mata zuciya sai "munafiki".. Mika masa wayar tayi bayan ta bude chat din nasu...

"Allah Ya isa tsakani na da kai Farouq,ka cuce ni,kuma wallahi bazan yafe maka ba". Jikinshi ne yayi sanyi, idonsa ya kada da yaga chat din..

" Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"shine kawai abinda yake ta maimaita wa...

Hindu ko sauraran sa ba tayi, taci gaba da cewa "yanzu kanuna na mata bani da wani daraja kuma baka sona,tunda tasan kayi aure amma gashi ka koma gurinta babu dadewa,don Allah yau gaya min Farouq,mai yasa ka aure ni?,don Allah ka taba sona kuwa?" muryar ta har ta fara dashe wa,hawaye kuwa wani yana bin wani,ga ido duk ya kumbura..Ya kalleta,zuciyarsa a raunane,kafin yace mata...

"Bana sonki na aure ki Hindu?, kema fa kinsan ina sonki"

Cikin daga murya Hindu tace "ba wani sona da kake wallahi,duk wulakancin ka akaina yake karewa,ka dauki kudi mai wannan yawan ka bawa wata karuwa"

Launin idon farouq ne ya kara cenza wa "kema kinsan wallahi bana neman mata,banyi ba kafin aure,kuma bazanyi ba bayan nayi aure,ki tsaya nayi miki bayani"...

" ba wani bayani da za kayi min na gane,bazan kara yadda da kai ba,kuma naji ba ka neman mata amma me tayi maka har kaji dadi ka dauki kudi ka bata,ai sai tace matar ka ta gida banza ce,to bari kaji na gaya maka,nagaji kuma bazan zauna da kai ba,sai dai mu hakura da auren na koma gida inyaso ka auro ta taci gaba dayi maka zobo da pineapple juice"..

Kalanta yayi ranshi a bace "bari na gaya miki Hindu,ko zaki mutu bazan rabu dake ba,kuma damuna tayi shi yasa na kulata" Ya fada yana kauda kai wurin fadin maganarsa ta karshe..

Ta kalleshi ido cikin ido tace" i'm disappointed in you,ya zakayi min irin wannan karya kana babba? ka bani kunya"

Wai damunsa tayi,ita daya bata wannan excuse din gwanda ya fada mata gaskiya.Bata da lokacin kara tsayawa taji rainin wayo irin wannan,gashi kanta kamar ya fashe don ciwo,bazata iya tsayuwar jin wani abunba...

A daddafe ta tashi ta shige dakinta ta banko kofar tasa lock,ita kanta karar buga kofar da tayi sai da taji ya kara mata ciwon kai...

Yana tsaye ya rasa me yake masa dadi,bakin kofar yaje ya murda yaji ta rufe,ya kira sunanta amma a banza,ko kulashi bata yi ba,hakuri yake bata,yasan tana ji amma tayi shiru...da yunwa ya shigo but ya nemeta ya rasa,wai me yasa ya kula yarinyar nan har ya tura mata kudi?ya tambayi kansa,yarinyar da Hindu ta fita ta kowane bangare....Ya dauki wayarta da ta bari a gurin ya goge fb,sannan ya bude tashi wayar,shima ya goge fb din,Insha Allahu,babu shi ba wani fb gashi basu kai ko shekara uku ba amma auren su ya fara tangal-tangal.Yasan Allah ya bawa Hindu hakuri,dolensa ya lallaba akoma zaman lafiya.Bakin kofar dakin nata ya koma yana cemata ga wayarta nan yasan a duhu take don Allah ta fito ta dauka,beji tayi magana ba yaja kafarsa  yayi hanyar nashi palon,kafin ya shiga palonsa ya jiyo kanshin abinci daga kitchen,anya kuwa tana wannan fushin tayi girki?ko dai sai da ta gama shaidan ya shigo masa gida?cikinsa ne yaji ya bada wata kara kuuui....Ta palon ya wuce dining yaga ta jere masa abinci..

"Ya Allah ka kore mana shaidan din da ya shigo mana gida".ya fada a fili,shifa gaskiya yana son matarsa amma ta fiya tsari da iyayi,kullum ita sai ta rinka nunawa komai ta iya,yasan tana da himma wajen koyar abubuwa da karance karance da kuma son neman ilmi.....da wannan tunanin zucin ya gama abinda yake ya shige dakin sa,yayi duk abinda ya saba kafin barci ya kwanta yana tunanin yau ce rana ta farko a rayuwar aurensu da Hindu ta gujewa dakin sa...

**STAY  FOOT**

AishaAbuTurab

Comment and press ⭐ please..

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now