chapter two

565 38 1
                                    

Hindu Usman sunan ta,itace 'ya ta shida tsakanin Alhaji Usman da Hajiya Fatima.'Ya'yansu goma maza shida mata hudu,Abdur Rahman shine na farko sai Aliyu, Hadiza,umar,Tariq,Hindu,Bara'atu,mariya,Sadiq sai dan autansu Mahmood.Hindu nada shekara 15 Abdur Rahman babban wansu ya rasu lokacin yana final year dinsa a university,wannan rasuwar ba karamin taba ta tayi ba duba da irin shakuwa da sukayi dama kuma Hindu irin yaran nan ne wadan da suke very sensitive,abu ko kankani ne damun ta yake balle rashin dan uwa.                                                          Alhaji Usman ya kance a cikin 'ya'yansa Hindu itace bata da kwarin zuciya ko kadan,idan abu ya dameta a zuci take barin sa babu wanda za tayi kokarin sanar wa.Yasha kama ta tana kuka ita kadai amma juyin duniya baza tayi magana ba....dalilin haka ya ke yawan yi mata kyautar littattafai kala-kala na addini.Duk wai don ta samu ta rinka dan debe  kewa...Ita kanta Hindu gwanar karatu ce tun tana yarinya har ta kai teens dinta.                                                      Tsarin gidan su Hindu ne kowa sai yayi karatu zuwa higher institution,Yayan su Aliyu da ya karanci chemistry yanzu haka yana aiki a federal ministry of health a Katsina da matar sa aunty zara wacce cousin dinsu ce da 'ya'yansu biyu,sai aunty Hadiza mai aure a Abuja da 'ya'yanta shida ita hausa ta karanta.Umar ma a Abuja yake yana aiki da firs da matarsa daya da 'ya'ya uku,Tariq kuwa a kano yake kuma architect ne yana shirin aure.Hindu da sisters dinta duk suma a kano suke,Bara'atu business admin tayi kuma 'ya'yanta biyu ga cikin na uku tana aiki a admin department na akth,sai Mariya mai 'ya'ya biyu ita english edu tayi tana teaching a wata makarantar gwamnati.Sai Sadiq da Mahmood inda Sadiq yake Alkalam a Katsina,Mahmood kuwa yake Maitama Sule university dake Kano.Gidan su abin sha'awa ne saboda yanda suke son junan su da kuma irin kulawar da iyayen ke nuna musu.Alhaji Usman ba wani mai kudi bane sai rufin asiri amma bai kasa bawa yaransa tarbiya mai inganci ba,kuma yana kokari sosai ganin 'ya'yansa sun sami ilimin addini da na boko.Sai dai fa duk abinnan ance hali zanen dutse,dan kuwa kowa da irin halinshi a 'ya'yan nasa duk da dai Alhamdulillah amma Hindu akwai taurin kai,kafiya da rashin son sabo da jama'a wanda yasa mutane ke mata kallan mai girman kai...fatanshi kullum Allah Ya basu abokan zama na gari musamman Hindu mai baudedden hali,a kullum gani take ta iya kuma yadda take so ayi shine daidai....wannan kenan.
            Hindu geography ta karanta a Buk don tayi karatu har zuwa masters amma Farouq ya kafe akan baza tayi aiki ba.Amma kwanannan ya fara canza ra'ayi akan aikin nata don shima yaga yanda take zaune shiru ko da yaushe a gida kuma zaman tunin Hindu baya mai dadi duk da dama ba wasu kawayene  da ita ba amma bature yace an ideal mind is the devil's workshop kullun da sabon salo take zuwa masa idan shaidan ya gama hure mata kunne.Gashi kuma ta tashi a wani yana yi na tsara wa kanta rayuwa saboda rashin fadar matsalar ta....kafin aurenta da duk abunda zata yi sai tayi istikara hatta course din da za tayi a university sai da taita addua...Shi yasa ta tabbata zaben Farouq da tayi kuma Allah ya ba ta shi a matsayin miji shine zabi na farko da ta tabayi mai kyau a rayuwar ta.Ba ta manta ranar da Farouq ya fara zuwa gidan su lokacin tana remedials a Buk ta dawo gida agajiye ga kuma yunwa saboda ranar monday ne,tayi azumi,yaron makotansu Sani ya shigo aunty Hindu wai ana sallama da ke a waje yace mata..waye?ta tambaya,wai yayan su Billy ne.Billy kuma?ta tambayi kanta,Billy daya ta sani kuma jiyan nan sunday suka kaita gidan ta banda ita ba ta san wata mai irin sunan ba.Ka ce ina nan?ta tambayi Sani eh mana ba ga kinan ba,kai! Ba haka na tambayeka ba,shidin da yake waje ka fada masa ina nan?...eh mana ina kofar shagon hassan na ga dawowar ki.Amma Sani baka kyautamin ba,yanzun ko hutawa banyi ba har ka rakito min wata matsalar ta fada tana fita zuwa gurin hajiyan su,shi kuwa Sani ya fita yana dariya yaje yace tana zuwa da tasan be ce tana nan ba da baza ta fita ba sai dai ta tura shi yayi karyar bata nan.Hindu tana shiga dakin Hajiya ta tadda ita akan sallaya don ka'idar ta ne idan tayi sallar magriba ba ta tashi sai bayan isha'i...ta danyi jimm kadan sannan tace ya akayi ne Hindu?wai Sani ne yace ana sallama dani.Yanzu haka?ta tambaya saura kadan fa akira isha'i,maza to ki leka amma karki dade ni bana son irin haka.A haka ta fita ko gyara fuskar ta bata yi ba saboda bata da lokacin bata wa a wajen,a kofar gidansu ta tadda maza guda biyu,ta dai gane daya daga cikin su,da shi su billy suka zo kawo ma ta iv.Dayan kuwa gaskiya bata san shi ba,sallama tayi suka amsa atare sanna suka gaisa,Hindu tayi shiru ta kalli wanda ta gane din acikin su don ko zata san dalilin zuwan su...wanda bata sani din ba shi ya fara magana,sunana Farouq brother din Bilkisu friend dinki da aka gama biki jiya,okay tace masa,sannan ya ci gaba Wannan kuma friend dina ne yace sau biyu yana kawo su Bilkisu gidan nan.Hindu tace na dai gane shi sun kawo min iv shida su Billy ko? ta tambayi abokin,eh  2weeks ma da suka wuce kunyi bikin wata friend din taku kuma mu da su Billy muka kawo ki gida..Kwarai Hindu ta tuna da su suka kawo ta gida lokacin bikin Maryam amma bata gane shiba sai zuwan su na biyu aiko ya fiya surutu,..ta gyada kanta alamar ta eh ta tuna sannan yace suna na Nasiruddeen kuma Farouq shine dalilin dawowar mu gidan nan amma naga kamar sauri kike ki koma gida..kuyi hakuri,ban dade da dawo wa ba gida ne daga makaran ta shiya sa.Farouq dinne yayi maza ya ce babu komai sai dai kawai tunda mun ga gidan ki bamu lambar wayarki sai muyi magana a waya,har zataa bayar ba daidai ba taga rashin amfanin yin hakan tunda sun san gidan nasu  zasu kara dawo,kawai ta bayar,yace ya sunan?ta kalleshi tace Hindu....

*i'm not perfect*
*wannan littafin kirkiranshi akayi*
             *Stay foot*
And don Allah arinka danna ⭐

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now