chapter seven

293 15 2
                                    

Washe gari da ciyon kai ta tashi,ga ido yayi luhu luhu,abinda ya faru jiya shi ya dawo mata taji idonta ya circiko,kokari tayi ta tsayar da kukan,saboda tayi alkawari Farouq ya de na sata kuka,kirjinta duk ya kara cikowa yana mata ciwo,jiya tun 11 na safe Ahmad be sha ba..Tana tashi taji amai ya taho mata,da gudunta ta shige toilet ta fara kakari amma ba ko mai acikin,sai wani green din abu take fitarwa,cikinne ya kara murdawa yayi kara alamar tana jin yunwa....aiko kamar kanshi taji,halan makota ne kanshin girkinsu yake shigowa haka...

Ruwan zafi ta samu tayi wanka tayi alwala,yau ma ta makara amma ta alakantashi da baccin da batayi ba da wuri.Tana fitowa ta goge jikinta ta dauko zani da hijab tayi sallarta,yau kam ta zauna zaman addu'a..A gaban kayan kwalliyarta ta zauna ta dauki mai ta shafa,ta dakko turarenta da ta saba amfani dashi taji yayi mata wani irin wari...kar dai abinda take tunani shine ya faru da ita,wata drawer ta bude ta dauko pt strip ta koma toilet...

Gwajin farko Hindu taga tana da ciki,kuka ne ya kwace mata,ko Ahmad bata yaye ba,ga makaranta sannan gashi ita yanzu bata son kara haihuwa da Farouq don bata ga gurin zama ba a gidansa,haka ta fito daga toilet tana hawaye,ta gama shiryawa ta bude kofa ta fito,duk irin abinda ke damunta,bazai hana ta dora musu abincin safe ba,hanyar kitchen ta nufa,kafin ta karasa take jiyo kara kamar abu ake soyawa,ga kanshi nan yana tashi,aiko Farouq ta gani dumu dumu yana suyar dankali,dama lokaci lokaci yana irin wannan,ko da cikin Ahmad haka yake mata,yau kam yana da dalilinsa,yauce rana ta farko tun aurensu da ya taba kokarin masalaha bayan sunyi fada,duk lokacin da sukai fada ita take bada hakuri ko ita aka cuta don kawai azauna lafiya..

Tana shiga ya taho gurinta yana murmushi yayi hugging dinta,ta kauda kanta ta tsaya kamar dutse...

"İna kwana yace mata"? abin yaso ya bata dariya duk da dinbin damuwar dake ranta,wai yau ita Farouq yake gaida wa,duk don an cuceta ana kuma so a nadeta don acigaba da cutar ta...kauda kanta ta kumayi,ya danja da baya ya rike kafadunta da hannayensa,so yake su hada ido amma taki

" don Allah ki kalleni" yace mata yayi wani kalar tausayi,ita kuwa yau wannan zuciyar tata ta zama dutse,gani yayi bata da niyar magana kawai ya jata zuwa dining,ya zaunar da ita yana gaya mata ta zauna ta huta yanzu zai kawo abinci,Hindu kuwa duk wannan cikin na jikinta shi ya dameta,tana nan zaune taji wayarsa tana kara,alamar ana kiransa,dauka taji yayi da ladabi,bayan gaisuwa taji yana cewa "A'a wallahi hajiya,ba yayeshi akayi ba,to,insha Allah ina gama cin abinci zanzo sai in taho dashi" suka cigaba da maganarsu amma Hindu ta daina saurare...

Ya zama dole ta yaye Ahmad tunda dama yanzu ya wuce wata goma sha biyar,dama tana da niyar hakan,ba tun yau take jin alamar ciki ba hada hadar school ta hana ta maida hankali ta tsaya tayi calculating period dinta,shi yasa ta suyo pt strip din,Allah baisa za tayi amfani dashi ba sai yau...

Zaman da yayi ne a gefenta ya katse mata tunanin ta,ya riko hannunta,yana kokarin zama a kujerar dake gefenta,kokarin kwace hannun take,ya tsaurara rikon

"Don Allah kiyi hakuri,nasan ban kyauta ba,don Allah ki yafe min"... Juyo da kanta tayi,ta kalleshi ido cikin ido taga dagaske yake amma shaidan ya riga ya tunzura ta

"Na hakura,amma zamana da kai ya kare tun muna da daya"tayi shiru kafin ta cigaba " gashi yanzu cikine dani,kuma mai hali baya cenza halinshi,in Allah ya yarda daga wannan bazan kara haihuwa dakai ba" ta karashe hawaye na gangarowa zuwa kuncinta..

Zuba mata ido yayi,yaji farin cikin samun cikinta sosai amma zancenta na karshe shi ya daga masa hankali,addu'a kawai yake a zuciyar sa don kar ya bude bakinsa ya biye mata,yau Hinduce take addu'ar kar ta kara haihuwa dashi? Tana nufin su rabu kenan? Wannan kuwa bazai taba yiwuwa ba,tukukin bakin ciki ne yasa yayo magana

Cen kasa yayi da muryarsa kafin ya tambayeta"Kina nufin wannan cikin na jikinki da baki sameshi ba da haka kika fi so?" ya tambayeta yana kokarin kwantar da zuciyarsa "kuma kina tunanin zan rabu dake,me kike so nayi Hindu?, nima ina dana sanin laifin dana yi miki kuma a kullum zan baki hakuri,kada ki bari zuciya da shaidan susa kizo kina da nasani"

Yana rufe baki tace "ba wani dana sani dazanyi,yanzun ma dana sanin aurenka nake,wannan cikin da badan tsoron Allah ba wallahi da zubar dashi zanyi,bakasan kowa ba sai kanka,baka taba damuwa da damuwa ta ba" ta karashe tana kuka..

Tashi kawai yayi daga zaune,ya kura mata ido sanan yace mata "Allah ya baki hakuri"ya juya ya shige,key din motarsa ya dauka yafice daga gidan,zuciyarsa tana tafasa,se kace cikin shege,wai da ta zubar,lallai shaidan yaga baraka a gidansa,anya Hindu tana karatun Qur'ani kuwa idan ya fita? Hanyar gidansu ya dauka,har yakai yana tunani.

Yana shiga bangaren hajiyansa yayi,a zaune take a palonta wanda yake dan madaidaici,duk da ta manyanta,tasha kwalli da farar powder,ga lalle hannu da kafa,sallama yayi ta amsa da fara'arta kafin ya nemi guri ya zauna..Gaisawa suka karayi kafin yace "yana ganki ke kadai anan hajiya,ina su Fiddausi?" Duk suna ciki tace masa,itama ciwon gwiwa ne ya dameta ta fito daga dakin don ta mike kafar

"Ko dai maganin ya karene?"

"A'a duk biyun babu wanda ya kare,kaga da safen nan ma bayan nasha nashan,sau biyu Fatima ta shafa min na shafawar"ta fada tana dan juya kafar

" inaga to kawai gurin likitan za'a koma,ko nan da yamma sai nazo na kaiki"

Tace Allah Ya kaimu,kamar karfe biyar sai na shirya,kafin lokacin na ma Alhaji bayani ma..

Muryar fiddausi suka jiyo dai dai kofar daki tana "hajiya kinga yaron nan duk sonshi da wasan ruwa dakyar ya tsaya nayi masa wanka saboda yajiyo muryar abbansa" dariya sukayi duk kansu,nan ta nadoshi a tawul ta rungumoshi,tana zuwa ta dorashi kan cinyar Farouq "Allah raka taki gona,yaya ina kwana"

"Lafiya kalau fido,tintin tana daki kamar amarya ko?" dariya kawai tayi,shi kuwa Ahmad yana ganin abbansa ya fara murna yana gwarancinsa na murna,hajiya ce ta kalli dan da uban tace "oh jimin yaro,wai shima yasan babansa,don Allah karasa ladan ki,ki shiryashi"

Don kuwa sauri nake,akwai wanda nake son gani zuwa 11" da sauri aka shiryashi suka fito, hanyar gidansu Hindu ya dauka,cen zai kai Ahmad a yayeshi....

Farouq yana fita Hindu taci gaba da kukanta..Ji tayi kamar ta kira babban wansu Ya Aliyu,sai taga kila bazai gane ba,shima namiji ne,ko kuwa ta kira Bara'tu,a'a,Bara'atu hakuri zata bata,tace kawai tayi ta addu'a,duk da dai acikinsu babu wanda ta taba daukan matsalar gidanta ta fadawa,tasan halayensu sarai......

Tana zaune tana wa abincin gabanta kallan magani zainab
kawarta ta kira wayarta,zancen wata lecture dinsu sukayi suka gama,dama ita bata jin karfin fita yau.....

Wai shin Hindu tana zubar da cikin ko kuwa??? 

Stay foot

AishaAbuTurab


Tsarin AllahWhere stories live. Discover now