chapter eight

290 29 2
                                    

  Tunda wannan matsalar ta faru tsakanin su,Farouq ya kasa gane kan Hindu...za tayi komai na hakkinsa,bata tauye masa,amma inya kalli idonta yasan akwai wani daci acikin zuciyar ta,gashi tun daren da abin ya faru taki yadda su kara maganar balle yai mata bayani  ya kuma nemi yafiyarta,walwalarta agidan ta ragu da kashi saba'in,in kaga tana fara'a to lallai da Ahmad ne,wannan abu ba karamin daga wa Farouq hankali yake ba,yaso ace ta bude bakinta ta fadi duk abinda taga dama da tayi masa wannan shirun....

An kusa azumi da wata biyu ya biya musu Umra duk don ta kara kwantar da hankalinta kamar da..

Anata bangaren kuwa Hindu bata son ta kara yadda dashi....in kuma aure zeyi,ga guri nan,indae rikon da yake mata ze yiwa matar...koda ya gaya mata ya biya musu Umra,ba karamin jin dadi tayi ba,don zata samu damar yin ibada sosai,gashi tun kafin a fara azumi zasu tafi har sai bayan sallah da kwana goma zasu dawo.....

Bayan wata biyun kuwa tabi duk 'yan uwa tayi musu sallama wadanda kuma bazata iya zuwa ba, sukayi sallama a waya....

Tunda suka sauka a kasa mai tsarki Hindu ta samu wata nutsuwa a tattare da ita,duk da bataji azuciyar ta ta yafewa Farouq ba amma ta saki jiki dashi tun zuwansu saboda dole akwai abinda sai ta tambayeshi,haka akayi azumi suna ta ibada aka gama,aka kuma yi sallah. ....

Acikin kwanakin da yawan mutane ya ragune Farouq ya rakata don tace tana so ranar ta taba ka'aba...Ranar da baza ta taba mantawa ba kenan,ranar da ta jingina kanta a Ka'aba tayiwa kanta addu'a,ko kuwa alokacin tunaninta,Farouq tayi wa wannan addu'ar "Ya Allah ka cenza min halin  Farouq,idan bazai cenza ba,Allah kasa bazan kara haihuwa da shi ba"

(Sub hanAllah)

Haka tayi ta adduointa har ta gama,duk da tun kafin ta daga kanta,zuciyarta ke gaya mata ba dai dai take ba,daya barin na zuciyarta da shaidan ya gama ribata tana gaya mata dai dai tayi,tana juyowa suka hada ido da Farouq,yadda ya kalleta,sai taga kamar ya san addu'ar da tayi

"Kin gama"? Shine tambayar da yayi mata,ta gyada kai don ji tayi kamar an daure mata harshe,dana sani take a zuciyarta amma wani abu yazo ya danne mata zuciyar balle ta fara istigfari tun alokacin,ya riko hannunta saboda mutane

" muje na rakaki gida,ki dan huta,ga kafarki nan kamar ta kumbura,sai na dawo"

Banda zaman tunani ba abinda take,ga zuciyar ta tana ta gargadinta kan rashin dacewar abinda tayi...Haka suka dawo tana ta rainon cikin da Allah ya dora mata so,da kuma burin Allah Yasa ta haifi mace...

Shikam Farouq dawowarsu yaga cenji sosai tattare da matar tasa,duk da sau dayawa sai yaga kamar tana da wata damuwar banda wadda ya sani,idan kuma ya tambeyeta sai dae tayi murmushi tace babu komai ko tace gajiya ne kawai

*****
Kwanci tashi cikinta yayi wata tara har ya dan gota,tasha wuya sosai don kamar ba tayi rai ba,haka likitoci sukai shawarar kawai ayi mata aiki acire babyn don sunga alamar bazata haihu da kanta ba,kuma za'a iya rasa ta ko a rasa abinda zata haifa ko ma duka...Aikin akayi kuwa,sai dae babyn tazo babu rai.

Haka 'yan uwa da abokan arziki sukaita lallabata,da gaisuwa da kuma adduar Allah Ya kawo wasu masu albarka. ...zuciyar Hindu tayi nauyi,itada Farouq sai kallon kallo,ta hakane suke bawa junansu hakurin rashin baby girl din da sukayi,kwanan ta shida a asibiti aka sallamota,lokacin rashin babynta ya dawo mata sabo,ta kalli kanta a full-length mirror taga ba ciki,kuma ba baby,sai a lokacin kukan da ta kasayi a asibiti yazo mata....cikin da take ikirarin zata zubar,ashe zai girma har yazo duniya ta ganshi da idonta amma Allah baiyi ze rayu a duniyar ba,haka Allah Ya tsara,yinin ranar haka tayishi tana kuka,tun ana bata hakuri har ta fara bawa masu raunin zuciya tausayi suma suna taya ta....

Bayan satanni ta warware sarai,don harta koma school suna dinal exams dinsu,dake cs akayi mata,duk da batayi tsarin tazarar haihuwa ba,tana kokarin karta samu ciki har sai tayi wata shida kamar yadda suka gaya mata a asibiti.

Rayuwa ta cenza sosai itada Farouq amma haihuwa shiru,tun tana zaman jira har suka fara tunanin zuwa asibiti don duba lafiyarsu..zuwansu na farko akayi musu tambayoyi sannan aka basu gwaje gwaje da za suyi,amma na Hindu yafi yawa..Bayan sun hada duk sakamakon ko wane gwaji ne suka kaiwa likitan nasu,inda yaga Farouq yana da matsalar rashin yawan kwayoyin haihuwa sanna ita kanta Hindu,kunnuwan mahaifarta duk biyun a toshe suke...

Tun daga lokacin ta shiga wani tashin hankali wanda ita kanta bata san ana irinsa ba,babu abinda ke mata yawo azuciya kamar addu'ar nan da tayi...

Sunje gurin likitoci da yawa amma duk magana guda daya ce,karshe ma wani likita cewa yayi sai dai a sa mata (ivf),wai tunda yanzu Allah Ya kawo saukin abin,kuma suna yi a  asibitin,haka Farouq ya fara biyan kudin gwaje gwaje da akeyi kafin ayi dashen,tunda da kudin gwaje gwajen da kudin dashen daban ake biya banda murna Hindu bata komai,sai ranar da zasu biya kudin dashen sannan ayi fixing musu ranar dashen Farouq yace ya fasa,wai bazai biya kudin abinda Allah Yake badawa kyauta ba....

Ranar Hindu tasha kuka tayi tur da bakin da ya yanka wuya,tayi adduar da gashi ba'aje ko ina ba ta dawo kanta,kuma duk da hali irinna Farouq na rashin sanin darajar abu,son da take masa,ta tabbatarwa kanta baza ta iya rabuwa da shi ba

Haka suka cigaba da rayuwa,sai dai duk inda taji zance magani ta siya ta gwada har kawo iyanzu da shekarar ta bakwai rabonta da haihuwa
(Back to labarin)

Stay foot🌸

🌼🌸🌸🌼🌸🌼🌸

@AishaAbuTurab

Star dinda kuke dannawa itace take kara mana karfin gwiwa

Please comment and press ⭐

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now