chapter four

361 25 2
                                    

**Tsarin Allah**

**Na Aisha Abu Turab**
            @fantafar
                         💖

Farouq shine da na goma-sha hudu a gidansu,na takwas a gurin mahaifiyar su,cikin yayanta goma-sha daya kuma dan autan ta a maza.Mahaifinsu babban dan kasuwa ne wanda ya shahara gurin kasuwanci,matansa hudu,'yayansa talatin da shida,Hajiyan Farouq,hajiya Zulaiha itace matarsa ta farko,suna ce mata hajiya,sai hajiya Bintu matarsa ta biyu mai 'yaya tara,suna cemata Mama,matarsa ta uku kuwa,hajiya Murja wato aunty,'yayanta goma,sai Aunty amarya wato hajiya Sauda me 'yaya shida.Alhaji Muktar wato Alhaji babba yanda jikokinsa suke kiransa ya rike gidansa sosai ya kuma hada kan matansa da 'yayansa...kishi kam a tsakanin matansa sai dai abunda ba'a rasa ba,tunda kowa da irin halinta kuma kowacce tarbiyar da ta taho da ita,ita take bawa 'ya'yanta duk da Alhaji Babba a tsaye yake amma akwai abunda sai da addu'a.Farouq yana da yayye manya-manya maza da mata kuma ya biyo mata,mata kuma suna binsa...Ya zauna acikin mata sosai har yana tunani irin nasu,sau da yawa Hindu takan kalleshi tace ya mai da ita kamar wata kishiryarsa saboda in tace dama sai yace hagu ko kuma tace,bata da dangin miji masu kusheta kamar sa....Duk wata karamar magana irinta mata Farouq ya iya..farkon shekarun su da Hindu kullun korafin halayen sa take amma da shekaru suka jaa sai taga ba amfani,ta zuba ido tayi addu'a ta zaunda da halin nasa a haka tunda tana sonshi,.shi yafiye mata.

          Ta gama hada musu abinci ta kuma fara kintsa kitchen din kenan taga wulgawar bera,ta saki dostar dake hannun ta,ta dare kan wata kujera mai kafa hudu ta roba tana karkarwa.....a rayuwa ta tsani bera,kai duk wani abu mai kama dashi bata so,zata iya suma daa beran wajen kafarta ya yiyo,gashi bata son mage,bawai don tana tsoron ta ba amma bata son tana taba ta.haka ta tsaya tadan dade kafin ta hakura ta zauna akan kujerar tana raba ido taga ko zai sake fitowa kuma in zai fito ta ina,dan ta shirya,a haka bata san lokaci ya dan jaa ba sai jin kara tayi,ta kara tashi da sauri ta dare kujera,Farouq ne ya shigo,ya rufe kofar,ya shiga kitchen din,tayi ajiyar zuciya.

"Ashe kai ne".. Yayi murmushi yace " tsaka kika gani ko bera na ganki kan kujera?" don yasan waddan nan biyun suke tada hankalin matar nan tasa..

Ta kalleshi tace "wallahi bera ne." yace "bera da safiyar nan,ina maganin da na kawo?" Ta kalli sama ta nuna kantar kitchen din tace "gashi cen sama", " to ya baki sa ba"shine tambayar da yayi ma ta.Hindu ta gyara tsayuwar ta akan kujerar sannan tace "manta wa nake amma insha Allah yau bazan manta ba.....

Ta langabar da kai da shagwaba tace masa" sauko dani kajii" Ya kalle ta yayi dariya yace "kedin buhun shikafa biyu a ya zan iya daukanki".ta bata rai tana kokarin sauko wa yace "bari na dan baki hannu na dai ki rike ki sakko". Hindu tace "a'a sai dai ka juyo na hau bayan ka".Ya juya yace ta hau,amma tana hawa yayi kasa luuu kamar zasu fadi,ya cigaba da dariya..Nan Hindu ta fara " sauke ni don Allah,karfa na fado"..Yayi banza da ita ya fara hajijiya yana dariya,ita kam Hindu rufe ido tayi ta cigaba da ihu..da ya gaji yace mata "sauko zaki fasa min kunne" Aiko yana aje ta tai maza ta zauna kan kujerar tayi shiru tana maida numfashi kamar ita ta dauke shi ba shi ya dauke ta ba....

Yana tsaye yana kallon ta da murmushi a fuskarsa,ta dago ta kalle shi tace "yau ka dawo da wuri".." Ai kinga yau mun fita da wuri yadda kike so,ba cunkoson abin hawa kamar ko wace safiya idan munyi latti" Ya fada yana mika mata hannu,ya janyota ta tashi daga kujerar,ya ruko kugunta ya danyi dariya yace "wannan kyau fa?"  Ta taba fuskar ta,ita dai tasan ba tayi wata kwalliya ba saboda tana ta sauri,sannan ta daura hannayen ta a kafardar sa tace "duk taka ce"

Murmushi yayi kawai alamar yaji dadin maganar ta yayi ma ta peck a goshi kan nan yace "maman Ahmad rigima"

Tayi dariya  ta harare shi tace ahaka kake sona"

Dariya yayi mai sauti kafin yace "kwarai kuwa,a haka nake son matata...."

Haka suka zauna zaman cin abinci suna hira suna rahaa,abinda yake kara wa zaman nasu dadi kenan,basa fushi da juna,in daya yayi fushi sai dayan yayi kokarin ganin ya kore wannan fushin.Acikin zance ne Farouq yake cemata "ina littafin nan kuwa wanda nake rubuta bashi aciki"?." Yana daki,in dauko maka ne"..."Bari mu gama tukunna,Abdallah ne yake nema yayi mun wasa da kudi,kinsan na ranta masa kusan dubu dari biyu,munyi komai a rubuce wannan satin da ya wuce ya kamata ya kawo,amma  kinga shiru,idan an kira kuma baya dauka,sai jiya yakira ni wai baya gari ne, kawai shiru nayi masa don raina a bace yake"..."Allah Ya kyauta Ya kuma bashi ikon biya,sai ka rinka yi masa addu'ar wanda ake binshi bashi ko Allah zai sa ya biya"shine abinda Hindu ta fada.wannan irin labarin ba bakonta bane,yau ya bawa wancen bashi kudi bai dawo ba gobe ya bawa wancen rabin kudi sun fito,wataran kuwa kaya yake bayarwa aki kawo masa kudin sai da  kyar,bata mantawa akwai wani wanda ya karbi kayansa a Kaduna mai yawa don kuwa kudin da taji Farouq yana  ambata suna  da yawa,sai kotu ce ta raba su da mutumin,dake ba'a bari a kwashe dai-dai,zirga zirga da daukan lauya shi kansa sai da ya kwashi kudi...

Farouq ya kalle ta yace "amin Hinduwa ta"......Dama Hindun sa ya bawa wannan kudin da ba haka ba 🤔,kuma da yabi shawarar ta daya rage kudin kada ya bada duka,saboda shi kanshi Abdallan wai kudi ake binshi,an kuma dame shi,kuma kudin da yake tsammanin zai samu bai samu ba amma tunda ga Farouq,sai ya ranta a gunsa daga baya sa warware....

Ta kalle shi tana murmushi,za tayi magana taga kuma alamar tunani yake" tunanin me kake kuma"ta tambaye shi.."Ba komai"kawai yace.

Sun gama cin abinci ta hada masa ruwan wanka ya shiga toilet ita kuma ta fara zabo masa kayan da zai sa...duk da tasan karshe sai sunyi rigima gurin zaben kayan.maza da yawa suna son mace ta fito musu da kayan sawa amma banda Farouq sai dai idan yasa kayansa ya tambayeta ko yayi kyau..wani lokacin ko shirin kayansa in an kawo guga sai yace shi baya gane wa jeren ta....

Yana fitowa wayan shi tayi kara yace da Hindu "duba min waye?" Ta duba tace masa "Aminu plumber"..." Sai yanzu zai kira ni,shi da nace yazo kamar karfe 9,kafin na fita ya gama duk aikin da zai yi,dauki ki mikon" ta danna ta mika masa wayar ya karba suka gama magana...

Ta dan nisa tace "dama ina son inyi maka maganar wani magani da nake so in siya" "kingama shan wancen ne?" Ya tambaye ta

"Na gama kusan wata daya da ya wuce har munyi maganar da kai, manta wa kayi,masha Allah na ji dadin sa,ai shi yasa nace ko inje a kara yi min Hsg dinne?"

"Kibi a hankali,in na dawo sai muyi maganar". Ya fada yana miko mata hannunsa da links don tasa masa.ya shirya tsaf ta kalle shi tace "baka yi sallar walha ba" yace "yanzu zanyi".yana jin dadi idan Hindu tayi masa tunin ibada,amma fa ita ba tayi....

Ya tada sallah ita kuwa ta shiga kintsa dakin,har ta gama ta zauna bakin gado ta fara shafa jan farce kafin ya idar,yayi adduo'in sa sannan ya tashi yana shirin fita.." Yanzu duk wannan kyau a kasuwa zai kare?"tace masa,tana hura iskar bakinta akan faratan ko sa bushe da wuri,Ya juyo yace mata "to ko na fasa zuwa kasuwar na zauna ki ta kallo na,don sai dai kallon"ya fada mata..duk lokacin da yaga ta rage kwalliya kuma ga jan farce a hannun ta ya san da dalili..

Ya fice palon sa tana biye dashi tana dariya har bakin kofar palon da zai fitar da shi daga cikin gida,ya bude ya juyo yayi hugging dinta yace "sai na dawo,ki kula da kanki"

"Adawo lafiya,Allah Ya bada sa'a.." "Ameen".......



*i'm not perfect*

Please share, comment and press that star ⭐

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now