chapter five

341 18 0
                                    

**Tsarin Allah**

       **Na Aisha Abu Turab**

Username dina ya zama @AishaAbuTurab

Banyarda wani ko wata ya canza min rubutu ba,ko a rage ko a kara wani abun......

Wannan littafin kirkiransa a kayi,ba'a yishi don kwaikwayon rayuwar wani ko wata ba...

Bismillahir Rahmanir Rahim

Shekarar Hindu daya da wata biyu Allah Ya azurta ta da haihuwar Ahmad,yaro kyakykyawa mai farin Hindu da kamar Farouq.

Farouq ba karamin farin ciki yayi ba,don tun a asibiti yake kyautar kudi,dake bayan haihuwa jinin ta ya danyi sama,kwanan Hindu hudu a asibiti kafin a sallame su...

Gidanta ta koma saboda Farouq baya son taje gida suma kuma dama yan gidan su basa wankan gida,kishiyar kakarta ita ta zauna da ita da mariya kanwar ta don ayyukan gida,an hanata wanka a asibiti sai dan abunda ba'a rasa ba,haka kakarta tayi ta mita wai ace yarinya tasa abu azuciya har jini yai sama an hanata yin wankan da ba karamin amfani zaiyi mata ba....itakam tasan babu abinda tasa a azuciyar ta banda tsoron haihuwar ita kanta.

Ranar da Hindu ta dawo gida tasha mamaki,farouq ya gyare  matashi,ta lelleka ko ina gurin tsaf,ita dai wannan haihuwar tazo mata da alheri..

Angon karni kuwa ya rasa inda zai sa kanshi balle inda zai sata,yayi nan yayi nan,tana cewa wash zai ce sannu,nan-nan sosai yake da ita,don kakarta har tsokanar ta suka rinkayi.Kowa yazo  barka sai  ya tafi da zancen mijin Hindu wanda baya jin kunya agaban kowa kulawa ya ke nuna wa Hindunsa.

Ba suna za'ayi ba amma Farouq sai da yayi mata dinke-dinke,daya ke su Bara'atu ne suka kai dinkin kuma su suka fada masa kudin dinkin,haka ya dauki kudin ya basu.Hindu kam tana ganin ikon Allah,mutumin da duk tsada da yawan kayan lefen ta in zata kai dinki sai yace bashi da kudi ko kuma sai yace ta kai in an fadi kudin dinkin,yace yayi mishi tsada,tasha kai dinki gurin wata tela wacce ko kafin tayi aure ba ta bata dinki saboda bata kware ba,amma haka zata kai mata dinkin tunda kudin dinkin baifi dubu daya ba...kuma ita ba abun ta karfi kudi a wajen hajiya ba.....

Yadda Farouq ya rinka azarbabi yasa Hindu ta rinka godewa Allah babu wanda take fadawa matsalarta...tab to da wama zai yadda da ita?,gashi yafi ta magana kuma gashi da sabo,kana zama dashi zaka ga kirkinsa kuma zai shiga ranka.....

Dama tunda cen Farouq  store yake cika wa da kayan abinci,aiko ya kara cika shi harda su lemon kwali,na roba,ruwan roba kai harda lemon yara saboda in baki sunzo da yara 🤔...ga nama kala-kala,Hindu har gajiya tayi da mamaki,sai godewa Allah take da Yasa Farouq ya rufa mata asiri.Tana kuma addu'ar Allah Ya sa ya dore da hakan...

Da kwarin gwiwar ta take saukan baki,da har gulmar ta facaloli suke yi wai dan rowa in sunje sai  ta dakko pure wata ko sanyi babu ta basu,ko kuma suce ta basu abinci,amma duk ta tsame naman cikin miyar.Tasan basu kadai suke wannan gulmar ba saboda babu wanda zai shiga gida irin na Hindu yayi tunanin za'a rasa irin kayan jin dadi haka...wasu ma arzikin yayyan suke duba wa suyi tunanin shima arzikinshi ya kai haka amma Hindu ta san duk yayyenshi sun fishi samu.Gida kam duk wanda zai yi aure mahaifinsu ne yake bashi da kudin hada lefe....

Haka akayi ta hada-hada har Hindu tayi wata uku da haihuwa suna taci albarkacin baki,daga lokacin da kafa ta dauke suka koma gidan jiya,duk baya damunta amma fa idan ta kawo abinci sai dai ya tsakura,ba nama ba dan salad,yayi ta wani iri da fuska duk da dai zai cinye,amma da gani kasan ba haka yaso ba....Dan kudin barka da ta samu ta fara tsakura tana amfani dashi,aiko in ya dawo gida hatta hirar sa sai ta cenza idan yaga yadda ta hada masa mai kyau yaci sannan yasha mai dadi....

Duk kudin da Hindu zata samu idan tayi amfani da shi agidan bai taba damun ta ba..Farouq kuma baya tambayar ta a ina ta samu kudi,shi in baza ta tambaye shi ba shikenan zata zauna lafiya....

Matsalar Hindu da Farouq ta zama babbab lokacin Ahmad yana shekara daya,Farouq ya dau wayar Hindu ya shiga facebook account dinshi,lokacin ita ba wani social network da take da account dashi,tunda in yana yi a wayarsa  babu abinda ke damun ta amma sai ta samu kanta da shiga facebook din wayar ta don taga ya abun yake kafin ta bude nata account din,tana ta duddubawa don abin ya burge ta,Shi Farouq din ma ba wani post yake ba sai comment da like,ta gama kallon ta zata fita kenan gurin messages ya dauki hankalinta,tana ta duba wa,duk maza ne masu message din sai mata guda biyu,aiko sai ta bude ta fara karantawa,da alama tasanshi tunda dadewa,sunsha hirarsu kafin ya tambaye ta yayarta wacce tace tana nan lafiya kuma zata ji dadi in taji sunyi magana,aiko shima yaji dadi amma da wane suna take amfani dan ya neme ta da kanshi? Haka suka yi dan hirar su bayan ta bashi full sunan da yayar take amfani dashi a face book...Hindu ta fita daga message din wannan din sannan ta fita daga account din nashi ta ajiye wayar....

Aiko da ya dawo gida take gaya masa ai ta shiga account dinsa,baice komai ba amma da tace masa harda wasu mata su biyu sai taga yanayin sa ya dan chanza..sai taji kishi ya kama ta... take ce masa kai kuwa ina ruwanka da tambayar wata yaya,ko kanwar ma da baka kula ta ba,wai ai shi kanwar ce ta masa frnd request kuma bazai iya yi mata wulakanci ba....

Haka ya tsara wa Hindu zance duk da taji kishi amma tayi kokarin kawar da shi don azauna lafiya tunda duk namiji mijin mace hudu ne.....

Abun bai damu Hindu ba sai a makaranta,lecture dinsu ta karshe tunanin maganarsu da Farouq ta dawo mata.. Kawai sai taji akwai abunda yake boye mata,kuma tana son tasan meye shi.wannan lecture'n dai batasan mai akayi ba sai da malamin ya fita,ta dauko wayar ta da niyar ta shiga fb,ashe bata da kudi,hakura tayi ta tafi gida,ta bude gidan ta shiga ta dan fara aikace aikacen ta,Ahmad yana gidan kakanninsa,ita kadai ce a gida.Tun tana zaune tana jira ko yaran mokota wani zai kwankwaso mata tayi aika har ta gaji tasa hijab ta fita...a bakin gate ta hadu da Shafeeq ta bashi kudi tace ya siyo mata kati....wannan katin da Hindu tasa shi ya juya mata rayuwar aurenta,ya cire mata zaman lafiyarta...Tun daga lokacin ta dena yadda da mijin nata...ta shiga bacin ran da yasa tayi wa kanta addu'ar da take tunanin ita take bibiyar ta har yanzu.....

Shin wai wace addu'a Hindu tayi wa kanta???

Bazan rika post ranar asabar da lahadi ba

I'm not perfect

Username is @AishaAbuTurab

Follow, comment and press ⭐

Stay foot!!!

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now