chapter three

390 29 0
                                    

*Tsarin Allah*
           *Na Aisha Abu Turab*
                 *@fantafar*

Firgigit Hindu ta tashi da salati abakin ta,ta juya ta dubi Farouq dake jin wa'azin malam Lawan a radio wanda an kusan gama wa ma,bai kalle ta ba,tayi adduar tashi daga bacci azuciyar ta,ta tashi ta shiga toilet don yin alwala amma me?sai taga period dinta yazo.Yanzu idan ta fara sallah sai ta rama wannan sallar kenan hmm!ta nisa,sallar asubar da ta rasa saboda lattin yin salla suna da yawa,kila da ta tashi da wuri da har sai tayi sallarta kafin period dinta,koma dai meye wannan sallar sai ta rama.Wanka kawai tayi ta fito,tayi maza ta kimtsa ta fita don azatonta,Farouq yayi bacci don  idan ta juyo ta kalleshi,sai ta ga idonsa a rufe,shi kuwa Farouq ikon Allah Yake gani,yau ko sallar bai ga alamar zata yi ba ko kuwa bayan fitarsa tayi? 😅 abunda Farouq ya tsaya tunani kenan.shi ya san Hindu nada kirki,ga kyauta don bai taba cewa zai yi kyauta ta hana ba,sai dai tace a kara,kuma ya sani yayi kura-kurai da yawa farkon auren su da yanzu yake tunanin son da Hindu take masa ya ragu,kuma duk da haka yasan son da suke wa juna ba kadan bane,amma meke faruwa da ita haka?banda matsalar ibadar Hindu,ya san gani take kamar baya son kyautata ma ta,amma shi barnar kudi ne damuwar sa,kar ya saba mata da bata kudi kuma ranar da babu ta dame shi....yana wannan tunanin ya jiyo hayaniyar ta da Ahmad,"Dan uban ka kayi sauri an makara!tun dazu mai kake a toilet?karka bari raina ya baci".....Zuciyar sa ce taji ba dadi,shi wallahi da Hindu ba ita ta haifi Ahmad ba da sai yace ta tsani dannan nasa,duk safiya sai anyi wannan,ranshi yana baci kullum idan yaga yadda take wa wannan dan nashi kwaya daya,wataran sai yaga kamar danta bata masa rai take yi,shi ya kasa gane irin wannan abu haka, komai so take ayi da sauri,yadda take so,kuma ta tsara,don Ahmad kafin ya shiga toilet duk safiyar duniya sai ance kaza zaka fara yi sai kaza....ko shima haka take masa gurin zaben kaya ko hular da zai sa,kai hatta magana idan yayi wataran sai Hindu tace ba haka ya kamata yayi ba.Wannan abun ma yana damun sa,Ya tabbata tsari da hadin Allah sannan da son da suke wa juna shine yasa suke zaune inuwa daya....Ya sakko daga kan gado ya fita daga dakin nasu ya shiga palonsa ya bulle kitchen inda ya jiyo motsin ta,yana shiga ta juyo tace ina kwana?yace lafiya,ko kinsan ko ina anajin hayanir ki kuwa?Don Allah ki rinka tausasa maganar ki akan Ahmad,kefa uwace,a kullum magana mai kyau ake son ki rinka furta masa....ta kalli Farouq rai a bace tace kai dai ka kusheni kullum shine burin ka,daga cewa ki gyara mai ya kawo zancen kushe acikin wannan,Hindu tayi masa shiru ta ci gaba da aikin ta,Farouq ya jijjiga kai ya fice zuwa dakin Hindu inda nan ne Ahmad din ke kwana....Ya shige palon ta sannan ya shiga dakin,amma bai ga Ahmad ba, Ahmad!ya kira sunan da dan karfi kadan "uhmm" Ahmad ya fada alamar ya na toilet,kana jina,kayi sauri ka fito ka ji,saboda karka makara,kaga jiya saura kadan arufe gate muka karasa,Farouq ya fada yana kasa da murya alamar lallaba wa.....ita dai Hindu tana kitchen tana jiyo su,ita ta kasa gane dalilin da ya sa Farouq banda kushe ta baya komai sai kace shima abun duk da ya kamata yayi a matsayin shi na miji yana yi.
                Shekarar su goma da aure har yanzu basa fahimtar juna,shekara goma mai dadi kuma mai wahala,Hindu dai kam bata da wata matsala da Farouq sai maganar kudi sai kuma yawon kusheta da yake yi komai tayi sai ya samu dalilin kushe wa,aganin ta wannan matsalar sa ce babu mai hanata abin da taga dama idan har bai saba sharia ba.Amma kam tunda sukai aure Farouq maganar kudi itace ke sawa suyi fada,lokacin tana amarya dake ba'a dade da bikin su ba aka fara azumin watan ramadan kullum sai sunyi rigima gurin ba da kudin cefane,ba dan komai Hindu ke damuwar ya bada ayi cefane ba illa fita kunyar bakin da kullum sai ansha ruwa da su,yau abokan diploma,gobe na secondary,jibi na kasuwa,wataran kuwa na university,kullum mutum sun kusa goma,da Hindu ta gaji sai kawai tasa sadakin ta agaba tarinka zara tana musu dabge, sadakin da Hajiya tace taje ta karbi wani kudin a wajenta ta cika ta sayi awarwaro na gwal ta ajiye.....ranar da Hindu kudi ya yanke mata,rannan taga tsiya sabo da ranar cousins dinsa ne zasu zo,aiko yace bakin ciki take don bata son 'yan uwansa shi yasa tace ba kudi a hannunta..Hindu tasha kuka ta godewa Allah.
        Ta gama hada abincin makarantar Ahmad sannan ta hada masa abincin safe da zai ci kafin ya tafi,ya gama yana Mama sai na dawo,tace Allah Ya kiyaye Ya kuma bada sa'a,Abbansa ya wuce da shi makaranta saboda makarantar da dan nisa,itama zabin Hindu ce,ba yanda Farouq ya iya da mitar ta,haka ya cen zawa dan nashi makaranta daga wacce yake a kusa.Suna fita Hindu taci gaba da girka musu abinda za suci idan Farouq ya dawo,wani lokacin kuwa suna fita take darewa gado tayi baccin minti 40,gidanta babbane amma bata da mai aiki saboda mai gidan baya so 😏..Tun kafin a kawo ta 'yan jere suke ta fadin "wannan sai da me aiki,gida kato toilet 5,daki 3,palo 2,dining area,kitchen,store da kuma extra daya ke kamar office ko library ne oho", haka akai ta haya niyar.Lokacin da aka kawota tana level one,ga aikin gida ga school amma Farouq yace bashi da kudin daukar mai aiki,in zata tafi makaranta tare suke tafiya saboda shi kansa yana level 3,ya dauki naira dari ya bata yace taci wani abu 😂.......idan ta tuna da wannan yanzu abun sai yayi ta bata mamaki 🤔,ya bata dari taci abincin zaman yini guda a makaranta,shi kuma su shiga restaurant shida abokansa yayi balantiya kowa yaci abunda yake so,shi yasa kawo iyanzu take yawan tambayar kanta wai shin Farouq yana son ta kuwa???

  
*i'm not perfect*

    *Please help raise a sister by commenting,sharing and pressing that ⭐**

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now