chapter Nine

572 30 12
                                    

*********
Azaune suke suna hada katinan biki,Hajiya Zulai wato hajiyan Farouq tana fada ma su Fatima sunaye suna rubutawa.......Hajiya Bintu(mama) ta shigo dakin hajiyan da sallamar ta.

"Hajiya kinji Asabe mahaifiyarta ta rasu ko"

"İnna lillahi wa inna'illaihir rajiun,yaushe"? Ta tambaya muryarta nayin kasa

"yanzu nan ta kirani,ko kaita ba'ayi ba,wlh abin tausayi don ta kasayimin magana sosai sai kuka"Mama ta fada da alhinin abin da tausayi kwance a fuskarta.

"Jinya ta kare,Allah ya gafarta mata".. Fiddausi ce tayi zumbur kamar an tsikare ta tace

"shike nan wannan bikin ba waina me dadi,don wlh in ba Asabe ce tayi ba akwai matsala"

Wata harara hajiya ta watsa mata,rai a bace

"Kijimin aikin banza,ana mahaifiyarta ta rasu kina maganar waina dan rashin hankali?" ta juya gurin Mama "ko zaki sanar wa da sauran,bari naje na sanar wa Alhaji sai mu shirya muje"

mama ta juya ta fita,ita kuma hajiya ta dauki hijabinta tana mitar rashin hankalin su Fiddausi.....tana fita wayarta da ta bari a daki ta fara ringing,Fatima ce ta duba"lah aunty Hindu ce"

Dauka tayi suka fara hira kamar ya da kanwa kafin Hindu ta tambayeta shirye-shiryen biki.Duk da bikin jikar  hajiyan za'ayi,Hindu tasan bikin kamar a gidan za'ayi,don ma Alhaji baya bari ayi masa taron biki ko suna,da anga bidia....shigowar Hajiya ce ta dakatar da hirar Fatima da Hindu,Hajiyan ta karba suka gaisa,suka danyi hira kafin Hindu ta ajiye wayar

"Ya naga kin dawo Hajiya"?

"Alhajine yace su suje ni na zauna,kar abar gidan ba kowa,sai ku"ta karashe tana dan hararar Fiddausi da tayi mata tambayar,wanda yake nuni da 'har yanzu laifin dazu yana nan', İtako Fiddausi dariya kawai tayi,tasan halin Hajiya,yau kila duk dan gidansu da yazo sai yaji labari

"Ku rubuta katin gidansu Hindu,ki hada mata da naman kaurin Amira,tun jiya hajiya Bintu ta bayar,ki hadasu guri daya idan mijinta yazo anjima sai a bashi,ki dan bude ledar naman"

Leda Fiddausi ta dauko ta hada komai aciki tana "Allah Yasa yazo don jiya naga be shigo ba"

"Ameen" hajiya ta fada tana tunani,shi Farouq wato tsarin iyali suke,ga kannansa nan daga mai 'ya'ya biyu sai me uku,sa'annin aurensu kuwa hadda masu hudu,shi kuwa tunda matar aka cire mata 'yar nan babu rai shiru kake ji,ze ko zo ya sameta,inma roba suka sa to lallai suje acire....

********
Hindu na gama waya da Hajiya ta ci gaba da 'yan ayyukanta na gida,wayarta ta bude ta kunna app dinta na Qur'ani ta zabi surah ta kunna,tana aikinta tana bin karatun har ta gama hada abincin rana..karfe daya da rabi su Ahmad suke tashi daga makaranta,kafin suzo gida wani lokacin sai biyu da ashirin ko ma da rabi..ta kintsa kitchen din ta koma daki..'Allah dae Yasa Farouq ya dawo gida da wuri yau' ta fada a zuciyarta,don yau kwanan ta kusan hudu tana so tayi masa maganar maganin nan da ta gani..nisa wa tayi,ta mika hannu ta dauki carbinta da ke gefen gado,istigfari ta fara kamar yadda take yawan yi yanzu.Dole ta nemi yafiyar Ubangiji,ko batayi butulci ba,ko bata raina kyautar Allah ba,anaso bawa ya kasance mai yawan tuba balle ita da takeji kamar zunubinta ya danneta,kullum ji take kamar yana mata kararrawa aka, don kullum sai ta tuna da wannan zunubin.....

Takardunta dake kan bedside drawer ta kalla,wayarta ta dauka ta bude yahoo mail dinta ta turawa 'Ya Ali da 'Ya Umar c.v dinta,gobe kuma zata je wata makarantar kudi dake kusa dasu ta bada wanda ta bugo a cafe,don kuwa yanzu makarantar gwamnati sai dan sarki.....

İstigfarinta ta ci gaba dayi har ta fara gyangyadi,nan bacci ya dauke ta

Kwankwasa kofar da ta jiyo ne ya tashe ta,ta dauki wayarta ta duba lokaci,biyu da minti goma sha biyar ta gani,tana mikewa carbin ya fado,wai daga kwanciya har tayi baccin minti goma,da sauri ta fice daga dakin don bude kofar,tana budewa kuwa Ahmad ya shigo da sallamarsa cikin farin ciki da jin dadin ganin ta

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 29, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Tsarin AllahWhere stories live. Discover now