Prologue

37.7K 2.3K 132
                                    

To my daughter Haleema, May you forever be blessed.

Bismillahir Rahmanir Rahim

Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannan rubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubuta sharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikon karantawa.

Littafin DIYAM kyauta ne, ina fatan ya zamanto min sadakatujjariya har bayan raina. Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana, na fili dana boye.

Diyam is a total work of fiction, in yayi dai dai da labarin ki/ka to coincidence ne ba wai da niyya ba ne.

Diyam littafi na ne, mallaka ta ce, duk wanda ya juya min littafi ko ya siyar min ba tare da sani na ba shi da Allah.

Just follow my pen for I assure you, you are going to fall in love with DIYAM.

Episode One

Madaidaicin dakin karatun mai dauke da dalibai 36 yayi shiru bakajin motsin komai sai na takardu, sai kuma very clear voice din lecturer da take gabatar da lecture ga dalibai masu karantar ilimin law a makarantar Blavatnik school a cikin Oxford University. Darasi ne suke yi akan marital laws, inda malamar take yi musu bayani dalla dalla game da dokokin da suka shafi auratayya. Saboda kasancewa daliban sunzo ne daga mabanbanta kasashe, wannan yasa malamar take daukan kasashe daya bayan daya take musu bitar dokokin kasashen da niyyar in sun gama sai su hadu suyi comparing aga wadanne ne sukafi kyau kuma wadanne chanji ya kamata a samar.

A yau ne kuma malamar tashigo kasashen nahiyar Afrika. Ta fara da Nigeria, the giant of Africa. A nutse ta fara karanto wa daliban dokokin da kasar Nijeriya take dasu wadanda suka shafi auratayya. Suna tsaka da daukar darasin ne suka ji snicker, malamar ta dakatar da karatun da take yi ta dago kanta a tare da duk sauran daliban suka kalli sashen da dariyar ta fito.

A extreme end of the class room, sitting alone like an abandoned island, wata kyakkyawar budurwa ce wadda kallon farko in kayi mata daga nesa zaka ce kyakykyawa ce, in ka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi yadda kake tunani kyau, as kana cigaba da kallon ta kyawunta yana cigaba da bayyana a gare ka.

Da yawa a makarantar ana yi mata kallon balarabiyya amma Nigerians suna ganin ta suke fahimtar cewa tasu ce, kabilar fulani ce, kabila mai dangantaka da larabawa. Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa tayi dariyar ba. Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa ana kallonta ya saka ta dago kanta da sauri, dara daran idanuwanta a bude kuma ta saka su a cikin na malamar da take tsaye a gaban desk dinta.

Suka tsaya suna kallon kallo sannan malamar tace mata "why do you laughed? Are you finding this funny?" Ta girgiza kanta da murmushi a gefen kumatunta. Malamar ta koma kusa da podium ta tsaya tana kallonta sannan tace "where are you from?" Still kanta a kasa tace "Nigeria" malamar tace cikin harshen turanci "menene ra'ayinki game da wadannan dokoki na auratayya a Nigeria. Kina ganin sunyi dai dai ko kina da gyara?"

Shiru ta sake yi na wani lokaci, sannan tayi karamar dariya tana girgiza kanta, fuskarta na nuna cewa akwai abinda yake damunta, suddenly kuma sai tayi magana "bani da gyara ma'am. Saboda all those laws da kike lissafawa a rubuce kawai suke, maybe for the sake of the likes of you da zasu nema for educational purposes, amma ba wai amfani ake yi dasu ba" malamar looked interested, tace "so, can you tell us the situation of marriage in Nigeria?"

Nan take murmushin fuskar budurwar ya dauke, ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana kallon rubutun da yake gabanta. "You have a very beautiful handwriting kanwata" taji muryarsa a kunnenta as clear as if yanzu yake gaya mata.

Ta dago kanta tace "in Nigeria ma'am, northern Nigeria to be precise, marriage is just like a form of legal slavery" gabadaya hankalin yan ajin ya koma kanta, har wadanda ada suke yin rubutun su yanzu sun juyo suna kallonta. Ta cigaba cikin yaren turanci mai dauke da Nigerian accent "tabbas kafin aure akwai kalmomin I love You a wasu lokutan, amma yawanci ko da an ambata din a baki suke tsayawa basa karasawa zuciya, daga zarar anyi aure miji will have a feeling similar to feeling din da master yake ji a lokacin daya sayi slave. Like since I pay your dawry it means I own you, you belong to me. Sai ya manta da cewa shi da matar belong to each other. Wadansu mazan ko first year ba zata wuce ba zasu juye su zamarwa matar like total stranger, like bata taba sanin sa ba a rayuwarta.

"Na sani cewa kusan more than 80% na mutanen mu na arewa musulmai ne, kuma na sani cewa a Alqur'ani ance 'arrijalu qawwamuna alan nisa'i' miji shine sama akan mace, amma kuma da ubangiji yayi gaba kadan a Alqur'ani sai yace ya sakawa maza wannan qawwamar ne saboda su ya dorawa nauyin ci da sha da sutura da muhalli. Amma a halin yanzu more than rabin mazan mu basa iya daukan wannan nauyin da Allah ya dora musu. Mata da yawa su suke ciyar su shayar su kuma tufatar da kansu da yayansu wani lokacin ma harda mazajen na su. Mace zata fita ta je office neman kudi ko kuma ta fita saro kayan sana'arta sannan ta dawo ta girka abincin data siyo da kudinta ta, tayi shara da wanke wanke da wankin kayanta dana yaranta da na mijin, kayan kuma da ita ta siya da kudinta, ta taya yaranta yin homework din da aka basu a makarantar da ita take biya musu kudin makaranta, sannan kuma mijin yayi expecting zata kai masa ruwan wanka tayi masa ta shirya shi tayi masa tausa sannan ta biya masa bukatarsa a shimfidar auren su".

"Mace ce zata yi ciki, ta haihu, wata ma hatta ragon suna da kayan fitar suna ita zata siya, ta shayar da dan ta ciyar dashi da komai amma idan rabuwar aure tazo sai mijin yace 'ajjiye min yayana'. Tana ji tana gani, tana kuka yayanta suna kuka, haka za'a raba su mijin ya dauka ko daya ba za'a bata ba, kuma a karshe shi din daya dauka sai yaje ya kaiwa matarsa ita kuma ta azabtar dasu ta bautar dasu saboda ba ita ta haife su ba. Yara da yawa sun rasa ransu saboda irin haka, wadansu sun salwanta, wadansu sun koma almajirai, wadansu yan daba saboda babu tarbiyya, babu soyayyar iyaye". Ta goge hawayen da ya taru a idonta ta cigaba.

"To wadannan wadanda suka ci sa'a kenan, suka auri wadanda suka yi musu karyar I love you din, ga wadansu kuma iyaye ne kan zaba musu mijin su aura musu ko suna so ko ba sa so sannan kuma suyi tsammanin zasu yi masa ladabi da biyayya su bishi sau da kafa ko da kuwa yana dukan su kullum, ko da kuwa ya kasance sanadiyyar rasa komai nasu, ko da kuwa kullum in suka kalle shi zasuyi fatan inama dai in ya fita ba zai dawo ba. I Nigeria ne da yake girma ya lalace yafi karfin iyayensa, sai a samu karamar yarinya a raba ta da wanda take so a tilasta mata auren sa sannan a dora mata nauyin gyaran tarbiyyar sa. In ta kasa kuma a tozartata a aibatata, in ta nemi rabuwa da shi kuma ace ta kashe aurenta ta kasa karbar kaddararta. Kaddarar da aka ƙaƙaba mata ta karfi ba tare da son ranta ba"

"That's why I am here in Oxford, that's why I chose to study law. Saboda in tabbatar da cewa babu wata mace a Nigeria da zata sake shan wahala a hannun namiji"

"Ohh shut up please"

Duk class din suka juya suna kallon wanda yayi magana. Ta san shi, tana ganin sa a ajin amma basu taba magana ba dan haka ko sunansa bata sani ba kuma bata da interest din sani. Ya juyo yana kallonta yace "just because kin zauna a kusa da wadanda basu ji dadin aure ba bai kamata ki zauna a nan kina fadin maganganu marasa dadi akan kasar mu ba" ta daga gira daya sama tana kallonsa tace "wacce kasa kenan?" Yace "wacce kike magana akanta" tace "you don't look like Nigerian, and definitely not a northerner" yace "ohh but I am" tace "which part?" Yace "Abuja" ta tabe baki tace "Sorry but I don't consider Abuja as part of Northern Nigeria, so you shut up".

Ya kara bata rai musamman ganin dariya a fuskar daukacin yan ajin. Shi dai yasan duk da tashin da yayi a Abuja hakan bai hana shi kishin arewa cin Nigeria ba, ba zai bari a zauna a yaga arewa har haka ba, for his mother is from the north, his only sister now lives in the north, his uncle too, dan haka ya san hakkinsa ne a yanzu ya gayawa mutane cewa karyace kawai yarinyar ta shirya musu, maybe dan tayi suna.

Yace "What you consider and don't doesn't count here, muna magana ne akan what count and what doesn't. Ni nasan yadda aure yake a arewa for my mother was born in Jigawa State, kuma...." Tace "was she born, raised and married in Jigawa?" Dan shiru din da yayi yasa ta fahimci no ce amsar sa, ta daga kafada tace "then as far as I am concern she too is not a northerner" da sauri yace "her father was" ta sake cewa "born and raised?" Ya mike tsaye, frustrated, yace "what does it matter?" Tace "everything. In kana son sanin halin da al'umma suke ciki you need to live with and study them". Ya sake yunkurowa da niyyar sake kokarin kare mutuncin kasarsa kamar yadda yake tunani amma sai ya zamanto period din ta kare. Yayi kwafa sanda malamar take bayanin cewa zasu dakata anan sai next class zasu cigaba.

DIYAM..........writing

In anyi comments da votes da yawa zanji dadi, kuma zan fahimci ana son in cigaba.

DIYAMWhere stories live. Discover now