Red Handed

10.1K 941 26
                                    

Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo bakina na durkusa a gabansa nace "gani Alhaji" ya nuna hanyar gate "waye wancan da na gan ku tare?" Nayi shiru kaina a kasa "ya sunkuyo yace "ba'a koya miki in manya suna magana ba'a yin shiru a rabu dasu ba?" Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace "waye wancan nace miki" cikin azaba nace "Sadauki ne" ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba Audu ya taho da gudu ya durkusa a gabansa yace masa "wanene yace kake barin ƴaƴan iska suna shigo min gida?" Dattijon ya kalle ni sannan yace "bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne" Alhaji Babba yace "babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta" yayi saurin gyada kai "na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji".

Alhaji Babba ya juyo kaina yace "ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da sanin ta kike shigo min da kattin banza cikin gida" na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki "ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru".

Ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace "kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?" Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati "Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnen ki yake bi yana wucewa ko?"

Yace "mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?" Inna tace "Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za'a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam".

Yace "au kice min tafi ƙarfin ki kenan bata jin maganar ki" ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace "ni in nayi magana ba'a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki" ya sake ni ya juya yana cewa "shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan".

Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace "ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi" ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace "zo inga kunnen" na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.

Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furucin da yayi akan Sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amma gwara hakan akan abinda za'ayi masa in yazo din.

Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata "ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za'a saka mu a islamiyya ni da Asma'u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida" Inna tace "Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za'a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in Hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in Saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku" nace "Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su Fati in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka" ta danyi tunani tace "shikenan, ki bisu din". Ai kuwa na samu chance.

DIYAMWhere stories live. Discover now