Subay'a

10.7K 1K 108
                                    

Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace "Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa'a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu" yayi dariya ya zauna akan kujera ya ɗora kafa daya akan daya yace "maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu".

Na zauna nima ina mamakin bragging irin na Saghir, nace "komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa....." Ya daga min hannu "don't spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa" nayi ajjiyar zuciya na tashi.

Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi "to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi" yace "wanne irin aiki kuma?" Nace "rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?" Yayi tsaki yace "fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zai ke handling duk aiyuka" nace "so? Kai menene naka aikin?" Yace "who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan".

Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance "gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali".

Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana wata bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da Uwani kuma kullum waya ta tana kusa dani dan I was not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan.

Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace "am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za'a yi miki cs ne" duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace "ta taba haihuwa fa doctor, twins ma" Doctor ya dauko takardar scan din yace "tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka'ida in aka tashi haihuwa ɗa ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za'ayi sai dai ayi delivering through cs"

Na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za'ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace "kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi".

Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu'a, na kuma gayawa su Inna suma suka tayani da addu'a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa.

Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just one more time amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kamar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu'a a haka aka shiga dani.

DIYAMWhere stories live. Discover now