The Gamer

12.8K 1.2K 48
                                    

Tabbas maganar da Diyam ta fada wa Bassam bashi kadai ta taba ba, har ita. Tana fita daga ajin taji kanta yana wani irin juyawa kamar zata fadi, duk reality din rayuwar ta yana dawo mata. Tun da tazo UK take living in a dream yanzu kuma ta farka, gobe kuma zata kara farkawa tunda gobe zai zo bata san kuma da wacce zai zo ba.

As far as he is concerned yayi winning over her dan haka zata bi abinda yace kenan. Ta samu jikin wata bishiya ta jingina tana mayar da numfashi, a nan taji karar shigowar text wayarta, ta dauko a jaka ta bude taga wanda take tunanin ne ya aiko mata da message

"Tell him I say hi, kafin inzo mu gaisa gobe"

Ta sake karantawa, ta nanata amma ta kasa making sense of it. "Him?" who is him? Wata karamar murya a can kasan zuciyarta tace "Bassam" ta zame ta durkushe a gurin, so he knows about Bassam? Abinda take take gudu kenan shi yasa tayi cutting ties da Bassam amma gashi nan bata yi escaping ba. Amma ta yaya yasan labarin Bassam? "Fatima" muryar ta sake fada mata.

Ta mike and for the first time ta tari cab saboda yadda take ji ba zata iya tafiya a kafa ba. A motar ma dunkule wa tayi dan ba zata iya zama straight ba saboda wannan abin daya dunkule mata a ciki har yanzu bai saki ba, sai da drivern yayi mata magana sannan ta san sunzo, ta bashi kudinsa ta shiga ciki. Tana bude kofa idonta ya sauka akan Fatima a zaune tana facing kofa, suna hada ido Diyam tayi realising gaskiya, ba Fatima ce ta gaya masa ba.

Fatima ta mike tana twisting hannunta tace "Diyam, yaya yasan kuna tare da wannan yaron" Diyam ta bita da kallo bata ce komai ba, Ta cigaba "wallahi bani na gaya masa ba, I wanted to tell you tun jiya ya kira ni ya tambaye ni wai waye kuke yawo tare dashi a school nace masa ni bansan kina yawo da kowa ba, he said in ban gaya masa ba in yazo sai na sani. To dazu kuma ya kira yace min nayi masa karya kuma sai na gane kure na" still Diyam bata ce komai ba, kallonta take kawai tana lura da yadda tsoro ya fito baro baro a kyakykyawar fuskarta.

Ta taho ta zagaye ta zata shiga corridor Fatima ta mike ta rike hannunta tace "Diyam am sorry akan maganar shekaran jiya, wallahi bansan betting kuka yi a kan wani abu ba, ni kawai cewa yayi min zamuyi playing game, yana so in nuna miki da gaske yake zai kori Judith, please Diyam kiyi hakuri bana son alakar mu ta baci a saboda wannan" ba tare da Diyam tace komai ba ta zare hannunta daga na Fatima ta shige dakinta ta rufe kofa.

Direct toilet ta shiga, ta cire kayanta gaba-daya ta shiga shower ta kunnawa kanta ruwan dumi. Ta lumshe idonta tana jin dadin yadda ruwan yake sauka a kanta, tana jin duminsa yana narkar da daskararriyar zuciyarta, tana jin jijiyoyinta suna warewa suna aikawa da sakonni kwakwalwarta. Ta tuno abinda Fatima tace "a game" of course it is all a game, shi komai a gurin sa ai game ne. Ta tuno wata magana daya taba fada mata shekaru da dama da suka wuce

"Diyam, life is like a game of chess, the secret to winning is to observe the movements of your opponent, think deeply and make your move"

Amma abinda ya kasa ganewa shine a yanzu bashi da opponent din, shi kadai yake buga games dinsa kowa ya saki ya bar masa, kuma ya kasa realizing cewa a haka zai zo yayi hurting others, innocent mutane kamar Bassam. Ya kasa realizing cewa duk abinda take yi tana yi ne for him not against him. Shi kawai burinsa yayi winning, no matter the cost. Ita kuma burinta shine ya ajiye wannan game din ya duba reality, ita bata son wannan game din nasa mai ban tsoro, dan last game din da ya buga didn't end well, it ended with someone in jail for life, someone very important to her.

Ta kashe shower din ta fito ta daura dogon towel sannan ta dauki karami tana goge fuskarta da dogon gashinta dashi, a ranta tana kokarin placing kanta in his place daga nan sai taga menene next move dinsa. Amma duk iya kokarinta ta kasa guessing menene zaiyi a next move dinsa. Ta fito ta dauki wayarta data ajiye tana dubawa, sai a lokacin tayi realising cewa for the first time tun zuwan ta kasar yau ne rana ta farko da bai kira ta ba, hakan yana nufin yayi fushi da ita, fushi kuwa mai tsanani.

DIYAMWhere stories live. Discover now