Her Love

13.5K 1K 20
                                    

Tana saka kaya Fatima ta shigo dakin, daga ganin fuskarta Diyam tasan akwai problem, ta ajiye skirt din hannunta tana bawa Fatima da ta zauna a kan gado dukkan attention dinta. Ta ɗaga gira daya sama tace "me yace kuma?" Fatima tace "he asked me about Judith" Diyam ta hade rai tace "what about her?" Fatima tace "he asked wai bata kawo mana maza gida? Na gaya masa bata kawo wa but he didn't sound convinced." Ta sunkuyar da kanta kasa tace "am afraid he is going to send her away".

Diyam ta dafe kanta tana zagaye dakin da bacin rai a fuskarta sannan tace "tell him nace Judith is my friend, if he want to get to her he will have to go through me. Ni na kawo ta gidan nan, in yana son ya kore ta sai ya fara kora ta tukunna" Fatima ta saka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tace "ba dani ba, bani Fatiman ba. Uwata ta daina haihuwa ballantana ta sake haifo ni"

Judith ta bude dakin ta leko kanta tace "hey girls, food is ready" sai kuma ta tsaya tana kallon yadda suke kokarin kirkiro murmushi.

A bayan lecture hall dinsu ta hango Sadiq. Shi kadai kamar kullum, da sigari a hannunsa kamar kullum, tayi saurin dauke kanta ganin yana kokarin juyowa. Amma sai ta tsaya a kofar hall din bata shiga ba tana so taga yau zai shiga ko yau ma zamansa zaiyi a waje. Sai da aka kusan fara lecture din sannan ya taho, a gabanta a jefar da sigarin hannunsa ya saka kafa ya murje ta, zai wuce Diyam tace "you know smokers tend to die young ko?"

Ya kalleta for some seconds, ya busa mata hayakin bakinsa yace cikin husky voice "says who? I don't believe malama kamar ki ta yarda da wannan saying din. Kin manta kaddara? Ina islamiyyar taki ta tafi?" Ta sa hannu ta kaɗe hayakin da ya huro mata tace "maybe ni da kai munyi understanding kaddara differently. Tell me, why do we pray? Why do we struggle? Me yasa muke neman duniya kuma muke neman lahira in dai har an riga an rubuta komai, me yasa ba zamu yi kwanciyar mu ba mu jira abinda aka rubuta mana yazo ya same mu. Yes kaddara rubuyacciya ce, major abubuwan da zasu faru a rayuwar mu a rubuce suke but what is in between depend on choices din da muke making. Wannan shine fahimtata. And even the majors can be changed with prayer, prayer and hard-working suna chanja kaddara. Yes, kamar yadda ka fada shekarun da aka rubuta maka ba zasu chanza ba amma how you are going to spend them depend on you, ko dai kayi spending dinsu healthy and happy in ka daina shan sigari ko kuma kayi spending dinsu with lung cancer in ka cigaba da smoking" ya kalle ta daga sama har kasa yace "go to hell, both you and your preaching" ya shige class din ya barta a tsaye. Taji zafin maganar sa amma sai ta hadiye ta bishi a baya.

Suna shiga class din wani guy ya kalli Sadiq yace "the Nigerian guy. Why do you skip madam Sally's class yesterday, don't you want to depend your country anymore?" Sadiq yayi banza dashi ya shige ya samu guri ya zauna. A lokacin Madam Sally ta shigo, ana nutsuwa ta kalli Diyam da Sadiq tace "will you like to continue with the argument?"

Gabaki daya yan ajin suka juyo suna kallon su, Diyam ta yi gyaran murya tace cikin harshen turanci "abinda na fada rannan gaskiya ne, gaskiya ne based on sani na. Shima kuma musa min din da yayi gaskiya ne based on sanin sa. We may have come from the same country but we live in different worlds. Muna zama cikin different mutane, muna kallon rayuwa from different perspectives. My being right doesn't make him wrong. You as potential lawyers should know that" duk yan ajin suka gyada kai cike da gamsuwa.

Madam ta juya gurin Sadiq tace "what about you, are you satisfied as well?" ya gyada kai yace "am okay ma'am. We now understand each other" sai ya juya a hankali ya kalli Diyam, itama ta dago kai suka hada ido and she smiled at him, a take ya fahimci cewa she had the brightest smile he had ever seen.

Bayan sun gama dukkan lectures dinsu, ta fito tana tsaye tana jiran Fatima sai gashi ya taho, ya tsaya dan nesa da ita kadan yace "waiting for a friend?" Ta daga murya tace "yeah" sai kuma taga ya zo zai wuce ta, tace "my name is Haleema. Haleema Usman Kollere. But people call me Diyam" ya gyada kai yace "I am Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq. Most people call me Bassam. You can call me that as well".

DIYAMWhere stories live. Discover now