My Savior 2

10.1K 968 66
                                    

Bansani ba ko bacci nayi ko kuma suma nayi, amma cikin either baccin ko suman ne nayi mafarki ina tsaye a cikin cincirindon mutane hannayena biyu a rike da babies dina, hawaye yana fita a idona ina kwalla kiran neman taimako amma kowa yana ta harkokin gabansa babu wanda yako kallo inda nake, can sai ga Sadauki yana kutso kai ta cikin mutanen yana tahowa inda nake amma yawan mutanen da suke gurin ya saka yakasa karasowa sai ya tsaya daga nesa yana miko min hannu, kawai sai na zubar da babies din hannuna na kama hannunsa amma ina kamawa sai ya bace ya barni ni kadai a tsakiyar mutane. Na kwalla masa kira "Sadauki! Sadauki!! Sadauki!!!" Amma bai dawo ba.

Ji nayi ana rirrike ni ana ƙoƙarin kwantar dani yayinda ni kuma nake ta yunkuri ina kiran Sadauki. Na bude idona naga nurses suna tura ni akan gadon marasa lafiya, ga Inna tana biye dasu a baya zani a hannu har suka tura ni wani daki suka rufe kofa, sai kuma naji shigar allura a hannu na, daga nan na koma baccin ko suman ne ban sani ba.

Sanda na kuma farkawa I was feeling much better, dan a hankali na bude idona na sauke su akan ledar ruwan da take sakale a jikin karfe sannan nabi tube din da ya taho daga kasanta da kallo har zuwa inda ruwan yake shiga jikina. Na fara karewa dakin kallo ina kokarin recalling abinda ya kawo ni nan. Idona ya sauka akan Inna da take zaune rashe rashe a dandaryar kasa duk kuwa da cewa akwai kujera a dakin. Kuka take da iyakacin karfinta, sai na tambayi kaina "kukan me take yi?". Abinda na fara tunawa shine kyakykyawar fuskar jarirai na, sai naji wani relief yazo min cewa ban mutu ba at least zan sake ganin su, zan dauko su in rungume su a jikina. Sai naji cewa yanzu na samu wani source of happiness din bayan Sadauki.

Nace "Inna" sai naga ta juyo da sauri gurina tana share hawayenta da gyalenta, tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna wanda babu ruwan a jiki "sannu Diyam" na gyada mata kai kawai, zuciyata tana so ta tambayeta ina jarirai na amma sai baki na ya kasa furtawa. Ta tambaye ni "menene yake miki ciwo yanzu?" Na rasa me zance mata saboda duk ilahirin jikina ciwo yake yi tun daga kaina har yan yatsun kafata. Na tuna irin wahalar da nasha dan ko a mafarki ban taba tsammanin haka haihuwa take da azaba ba, na tuna mafarki na, sai naji ina jin haushin Sadauki me yasa ya rabu dani in the first place, mai yasa duk sanda nake bukatar sa nake samun bayanan?

Inna ta tashi da sauri ta fita, sai gasu sun dawo tare da wata nurse da tazo tana yi min sannu sannan ta auna bp na ta duba idona da hannuna tace da Inna "har yanzu mijin nata bai dawo ba? Yarinyar nan fa in ba'a kara mata jini ba za'a iya rasata, gashi har ta fara kumbura. It is a miracle ma da take a raye wallahi" Inna ta karkata kai "nayi ta kiransa wayar bata shiga wallahi, nayi ta kiran mahaifiyarsa ita ma bata dauka ba, yanzu babu wani abu da za'a iya yi mata kafin kanwata tazo? Tayi tafiya zuwa Abuja ne amma tace min yanzu zasu taho ita da mijinta" nurse din ta girgiza kai tace "gaskiya babu wani abu da zan iya yi mata ni dai, jinin nan dai shi za'a kara mata kamar leda uku first sannan kuma muga yadda za'ayi" Inna ta gyara mayafinta tace "bara in fita in je gidan da kaina" har ta kai bakin kofa kuma sai ta juyo "babu komai idan na tafi na barta ita kadai?"

Nurse din tace "babu komai, allurar baccin ma zan sake yi mata. Amma kiyi sauri, in babu kudin ma ki samo maza wadanda za'a iya dauka a jikin su" Inna ta sake kallo na sannan ta fita da sauri. Nurse din tazo kaina tana zuko allura tace "ki godewa Allah yarinya, you are very lucky" tana yi min allurar na tambayeta "ina babies din dana haifa?" Ta girgiza kai tace "ban sani ba gaskiya, ke kadai aka kawo ki nan tun cikin daren jiya" daga nan bacci ya dauke ni ina wandering ina babies dina?.

Sanda ma kuma farkawa Inna na gani tana waya tana kuka "wallahi Hafsa babu ko dari a hannuna a yanzu, gashi suna ta tsorata ni da yana yin jikin nata. Naje gidan babu wanda ma na samu duk sun tafi asibiti gurin Alhaji" naji kamar kaina ya kara nauyi, nayi kokarin daga hannuna naji shi kamar ba a jikina yake ba, eyelids dina ma kansu sunyi nauyi. Na sake cewa "Inna" ta ajiye wayar da take yi ta taho gurina da sauri ta rike hannuna "sannu Diyam, Allah zai dube mu kinji? Allah zai dubi maraicinki ya bamu yadda zamuyi".

Kamar amsa maganar ta sai ga wani doctor sun shigo shida nurse, hannunta dauke da ledojin jini guda biyu tazo da sauri ta fara kokarin daura min. Inna ta mike "jini? A ina aka samu jini" kana jin muryar ta zaka fahimci wani relief a ciki. Doctor ya juyo yana kallonta yace "ba ke kika kirawo wani dan uwanku ba?" Tayi saurin girgiza kai, "ni ban kira kowa ba, ban samu kowa ba da naje gidan" doctor yace "but baki dade da fita ba wani yazo yace dan uwanku ne, mun dauka ke kika turo shi, yace a debi jininsa, kuma muna aunawa muka ga yayi matching, shi leda ukun ma yaso bayarwa mu muka ce kar ya zama affected shi kuma. Ya biya dukkan bills din ku na gado da kudin magunguna duk mun rubuta masa ya biya har da ƙari wai ko wani abin zai taso".

Inna ta koma ta zauna akan kujera baki bude "to waye wannan kuwa?"
Nurse din tace "Halima Usman Kollere dai yace yana nema. Ya shigo nan ma ya tarar tana bacci sai ya fita". Inna ta rasa bakin magana.

Nurse ta gama daura min jinin ta juya suka gama rubuce rubuce ita da doctor sannan suka fita yayin da Inna ta zauna tana ta jera addu'a zuwa ga savior dina. "Allah ya bashi abinda yake so duniya da lahira. Yadda ya bude mu Allah ka bude shi shida zuri'arsa, Allah ya biya shi da gidan aljanna" na gyara kwanciya ta ina kallon window, dare ne, meaning na kwana na wuni kenan da haihuwa. Ina 'ya'ya na?

Washegari sanda na farka naji muryar Mama suna magana da Inna, sai kuma hayaniyar su Asma'u da Muhsina. Na bude ido ina kwallon su, they looked like twins, ina twins dina? A tare suka taho gurina suna rige rigen rike hannuna, nayi musu murmushi ina shafa kawunansu, Mama ta taso itama "sannu Diyam, ya jikin naki?" Nayi gyaran murya nace "da sauki Mama" tayi murmushi tace "naji dadin yadda na ganki, da duk hankali na ya tashi, ai mun auna arziki sosai" Inna tace "gashi kinga har ta fara saɓewa, amma jiyan nan duk a kunbure take. Wannan mutumin Allah ya biya shi da aljanna".

Mama tace "ni nafi tunanin irin masu bin asibitin nan ne suna taimaka wa mutane, maybe ya tarar ana zancenta shine ya nuna kamar dan uwane, tunda dai kinga yanuwan duk mun tambaya sunce basu bane ba". Ni dai ina jinsu ina jiran inji sunyi hirar jarirai na amma shiru. Tare suka kamani suka tashe ni tsaye, na tashi da kyar ina cije lebe, sannan Mama ta hada min ruwan zafi sosai ta kaini toilet da kanta ta gasa min jikina ta kuma saka na shiga ciki. Muna fitowa take ce da Inna "ashe bata karu ba" inna tace "eh fa, haka nurse tace min. To ai yaran ne baki gansu ba yan kanana dasu, ni ko a bakwaini ban taba ganin masu kankantar wadannan ba" Mama tace "Allah sarki. Allah yasa masu ceton ta ne" gabana ya fadi, na juya ina kallon Mama sai naga duk jikinta yayi sanyi, na saki cup din tean data miko min na rufe fuskata da hannayena.

Tayi sauri tazo ta rungume ni a jikinta tana jijjiga ni kamar yarinya "kiyi hakuri Diyam, Allahn da ya baki su shi zai baki wadansu. Kuma yayi alƙawarin aljanna ga duk iyayen da ya karbi ran yayansu suka yi hakuri" na kifa kaina a kafadarta nayi ta kuka, sai naji duk ciwon jikin da naje ji ya barni dan wanda nake ji a raina yafi na jikin ciwo. Sai naji muryar da naji jiya ta cewa ban mutu ba ta koma, naji tamkar rayuwa bata da amfani a gare ni. Na rufe idona ina tuno their cute little faces.

Sai da suka samu na tsagaita da kukan sannan suka saka ni a gaba na basu duk labarin abinda ya faru. Gabaki daya suka dauki salati. Inna tace "amma dai Saghir ya cika makaryaci, cewa fa yayi ita ce ta shiga daki ta rufe kofa sai daya ji shiru ya balla kofar ya shiga ya same ta a haka".

Na matso hawayen idona nace "wallahi karya yake yi. Shi ya kashe min yara na. Ta sanadiyyar shaye shayensa suka rasa rayuwarsu, bazan taba yafe masa ba wallahi". Mama tace "duniya ce Diyam, ki barshi da duniya ta ishe shi darasi shi da iyayen nasa dukka. Tun yanzu ba gashi nan sun fara gani ba" Nace "me ya faru?" Mama tace "ai daya gama mayen nasa ya farka ya ganku, babies din already babu rai, shine ya dauko ku babies din ko cibiya ba'a yanke ba ya taho daku gida a gigice, a nan aka jere wa Alhaji Babba su a gabansa innarki kuma Saghir din ya dauko ta tare dake ya kawo ku nan, dan wulakanci kuma babu wanda yayi kara ya biyo ku su ta yayan da suka riga suka mutu suke yi. Sai gashi Saghir yana kawo ku nan aka kira shi wai kuma gobara ta tashi a kantin kwari, shagunan Alhaji Babba gabaki daya sun kone kurmus babu abinda aka fitar, yanzu dai Alhaji ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ya tashi, har yanzu yana asibiti unconscious".

Na karbi tean da Inna ta sake haɗo min na kurba ina jin zafinsa yana kona min bakina. A raina sai nayi wani tunanin irin hikimar ubangiji da take cikin haihuwar wadannan yaran, sannan kuma na saka a raina cewa mutuwar su tamkar wata sabuwar jarabawa ce a gareni, kuma nayi niyyar yin iyakacin kokarina wajen cinta. Twins dina sun zo sun tafi, ko picture dinsu bani dashi sai wanda nayi saving a memory na, kuma bazan taba mantawa dasu ba har in tafi inda suka tafi.

Kwana na biyar a asibitin na warware sai abinda ba'a rasa ba. Ina zaune ina cin abincin da Inna ta zuba min ina tunanin yadda rayuwata take, kaddara upon kaddara haka take samu na and I wondered wacce kaddarar ce kuma next.

DIYAMWhere stories live. Discover now