The Two Corpses

10.7K 956 85
                                    

Tunda muka koma school nake lissafin kwanaki ina jiran zuwan Sadauki dan nasan wata daya yake yi yazo ya ganni, kuma nasan bashi da karya alkawari sam. Lissafi na yana cika kuwa na fara saka ran ganinsa. Ina zaune kuwa a class sai ga baba mai kiran alkhairi yazo kirana. Na tashi na bishi da sauri Jidda tana tsokana ta dan tasan lissafin zuwan wanda nakeyi. Muna fita daga class din na tsaya na kara gyara fuskata ta glass din window, ina lura da yadda sabon kitson da na saka akayi min jiya ya kara fitowa wa da kyawun fuskata.

A gefen staffroom na hango shi a kasan bishiyoyi kamar kullum in yazo. Sai dai amma dama matsa kusa sai naga kamar ba shiba, kamar Sadauki na bai kai wannan girma da iya daukar wanka ba. Sai na tsaya daga dan nesa nayi sallama. Ya juyo kyakykyawar fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, na rufe baki ina dariyar murnar ganinsa nace "ashe da gaske kaine, sai naga kamar ba kai ba" ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace "lallai Diyam girma yazo, yau ke ce da yi min sallama bayan da tahowa kike da gudu ki wuce kirjina?" Na dan jawo hijab dina na rufe fuskata ina jin kunyarsa, ya saka hannu ya bude fuskar yace "yanzu in taho gari ya gari dan inga fuskarki kuma sai kiyi min rowarta ki rufe? Kinyi min adalci kenan?" Na danyi murmushin jin kunya sannan na kalle shi daga sama zuwa kasa. Ya zama cikakken saurayi sosai, hatta sajen sa ma ya zama complete kuma yayi masa kyau sosai. Gani nake duk samarin duniya babu wanda ya kaishi kyau a lokacin.

Sai kuma na rike baki nace "wai! Zabgi!! Sadauki ina zaka kai girma ne? Sai wani jin karfi kake kamar zaka dauki duniya" cikin ji da kansa yace "ya kika ji sunan? Aliyu fa aka ce miki. Kin manta shi asalin mai sunan duniya kaf ta shaida karfinsa da jarumtakarsa? Sannan kuma akayi min lakani da Sadauki, kin san kuwa ko a cikin mayaƙa to duk wanda aka kira da Sadauki ana nufin jarumi ne shi a cikin jarumai. Ingarman namiji kenan" nayi dariya ina rufe baki, yace "what's funny?" Nace "wai ingarma, sai kace wani doki" shima sai ya tayani dariyar.

Sai da mukayi dariyar mu sosai sannan mukayi shiru na wani lokaci, na sunkuyar da kaina kasa ina jin idanuwansa akan fuskata, na dago kai na muka hada ido, na turo baki na buga kafa a kasa nace "ni ka daina kallona haka" yace "fada min menene shirrin, sai wani kara kyau kike yi kullum" na bata rai nace "bayan bana girma. Kuma wallahi ina cin abinci sosai" yayi dariya yace "girman zaizo ne Diyam. You won't know sanda zaki girma kawai sai dai ki ganki kin zama katuwa" nace "ni tsoro nake ji?" Ya bata rai yace "tsoron me? Nace "kai gashi nan ka zama katoto, gashi kuma zaka tafi jami'a, kar kaje kaga manyan yammata kace ka fasa dani" ya jingina da jikin bishiya yana kallona, yace "Diyam" na dago muka ido yace "you have no idea how much I love you, do you? Ke din fa zuciyata ce, son ki kuma jinin da zuciyata take bugawa ne yana zagaye ilahirin jikina. Ta yaya mutum zai iya rayuwa babu zuciyarsa? Idan kinga Sadauki ya daina sonki to numfashin sa ne ya bar jikinsa. Idan kinga na rabu dake Diyam to kirjina aka tsaga aka cire zuciyata daga ciki. Nine ya kamata in kasance cikin tsoron watarana zaki rabu dani, ina tsoron idan innarki ta ki amincewa dani Baffa zai hanani aurenki, ina tsoron in kin girma zaki samu wani wanda ya fini kudi wanda ya fini asali kice kin fasa dani"

Na girgiza kai na da sauri ina jin the mare thinking of rabuwa da Sadauki yana kokarin tsayar da numfashi na nace "never, ba dai Diyam ba, Diyam ai kai take so tun kafin ta san menene so, da kai ta saba da kai kuma za tayi rayuwa insha Allah. Rayuwa babu kai will not be only unbearable but also unimaginable. I can't imagine Diyam without Sadauki" sai ido na ya kawo kwalla, yace "zaki fara kukan ko? I am here and I am going no where"

Muka zauna akan bench ya fara bani labarin gida, anan yake gaya min Baffa ya siya masa fili kato, yace "filin fa babba ne sosai, wai ashe for years yana tara min kudin aikin da nakeyi masa a garage shine yakara akai yasiya min. Yace duk sanda natashi yi mana ginin gidan mu sai inyi akai. Sannan kuma ya fara bani salary a garage kamar sauran ma'aikata" nayi murmushi nace "inye, kaga masu albashi" ya daga gira yace "ya kika gani?" Nace "Baffa ya kyauta. Allah ya saka mishi" yace "ameen. Problem din da nake fuskanta daga Ummah ne, tun ba yau ba kinsan nake fama da ita akan ta kaini dangin babana taki, ni kuma yanzu ina ganin kamar har da rashin su a tare dani ne yake kara kiyayyata a zuciyar Inna, ina so su shiga rayuwata Inna ta gansu tun yanzu amma kullum Ummah tana ce min wai ba yanzu ba, wai lokaci bai yi ba. I just hope ba zai zama too late ba" nace "it won't be, ni nasan Ummah kuma na tabbatar tana da dalilinta".

DIYAMWhere stories live. Discover now