A Day To Remember

10.2K 999 31
                                    

Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gani ta budo kofa a zuciye tana kallona "ba kiranki ake yi ba?" Na taho a hankali ko wacce gaɓa ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta tunkuda keyata na durkushe a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace "Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?"

Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace "idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki amsa ba?" na fara rera kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba".

Na dago kai muka hada ido da Inna da ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan baƙin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?"

Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kai ki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe Sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.

Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.

A palo bayan na tashi Inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ya gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi? Diyam din yanzu har ta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren".

Inna tayi ƙoƙarin kare ni "ya shanye ta ne fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta".

Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba ya samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kallon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta.

DIYAMWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu