Fauziyya

11.3K 1.1K 132
                                    

Fati tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba'a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace "wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda na cewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai".

Na jinjina maganar nace "amma biki fa? Gara fa?" Tace "wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi" nayi dariya nace "kai Fati, har da sharri kuma?" Tace "wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara".

Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala'i. Zagi ta uwa ta uba daga ni da banyi komai ba har sadaukin. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace "ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba'a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba" ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.

Bayan kwana biyu kuma duk sai naji ya chanja, babu zagin sai kuma wani lallaba ni yake yi a waya kamar saurayin da yake kokarin tsara budurwa, ni dai sai dai in saki baki ina jinsa da mamaki ko kuma in kashe wayar in bar ta yayi ta kira har ya gaji. Ana gobe zai dawo ya kira yagaya min "ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tanade ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo" sai naji ma abin ya bani dariya nace "duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?" Bai musa ba yace "naki special ne. Har yanzu Diyam ban taba jin mace irin ki ba. Da gaske nayi missing dinki fa" sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo?

Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemon kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa Kabir ya kaimu airport ni da Subay'a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay'a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado.

Ina jinsu suka zo, kawai daga jin muryarsa naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay'a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota" nace "kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining" ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya ƙara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace "shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?" Nace "na dafa maka abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?" Ya saki hannun Subay'a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na sauka na fita na bar musu dakin.

Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma kasa muka zuba ni da Fati muna ci tace "ke ba zaki tafi gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin ke kina wulakanta naki?" "Humm" kawai nace mata sai ga kira kuwa Subay'a tana yi min inzo inji Daddy.

Yana zaune a kujera ya hade rai "ki zo ki zuba min abincin tunda ba zakiyi min wankan ba" bance komai ba na zuba masa na kawo table gabansa na ajiye masa. Yace "wai ke ciwon rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina mayar min yafi dadi" nace "ba ciwon rashin magana bane ba, ƴata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta" yayi dariya yana kallon Subay'a data zauna ta zuba mana ido. Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace "kai! Matar nan wani duwawu naga kina yi fa" nayi saurin kallon Subay'a naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.

DIYAMTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang