_*HASKE A DUHU*_
_*Book one*_
_*DAGA ALK'ALAMI*_
_*Aisha M Mahmud*_
_meeesherh lurv__*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*
*Page 5*
Ta dad'e wajen siyar da Koko sannan ta siyar da shi cikin wani yanayi yau take domin dai Kokon yau batayi kud'in da Iyah take so ta kaimata, yau cikin tashin hankali take domin dama kokon kad'an ta zuba Mata gashi kud'in sai sun Kai dubu Kuma Koko duka yawan shi baya wuce d'ari shida tuni hankalinta ya tashi duk yadda take zubashi Amma kud'in sunk'i sukai yadda Iyah take so haka har Rana ta fito Bata koma gida ba ganin zaman ba zaimata ba yasa ta tattara robobin kokon sannan tayi mik'e domin tafiya gida d'aukar bokitin kokon tayi tafara tafiya kamar kazar da kwai ya fashe Mata a ciki tashin hankali kwance fuskar ta ga yunwa tanaji ga tunanin halin da zata Shiga indan ta koma gida tasan ba abinda zai Hana Iyah ta nad'a Mata na jaki, Amma ya ta iya Dole ta tafi gidan ko tak'i ko taso, cikin tafiyar ta had'u da Mairo cikin gudu tayi wajenta domin Mairo Allah ya hore tsalle tsalle tsaki Sultanah tayi ganin Mairo na gudu cikin Bata rai tace "Wai ke Mairo sai yaushe zakiyi hankalin ne? Kullum ke Baki tafiya da nutsuwa sai da gudu kamar ba mace ba, kinsan fa nayi muguwar tsanar wannan halin naki ko." Dariya Mairo tayi ta dafa ta tace "Wallahi dad'i ne ya isheni zumud'i yayi min yawa shiyasa nagaza nutsuwa har sai nazo na fad'a maki." Murmushi kawai Sultanah tayi domin tasan halin Mairo kullum tayi Mata magana da abinda zata fad'a Mata Dan ta kare kanta dashi dariya tayi sannan tace "Fad'amin to miyafaru Wanda har zai saki gudu Ina saurarenki." Murmushi tayi sannan ta juya kanta gefe wai tanajin kunya sannan tace "Wallahi yanzu Ali yazo yake fad'amin ya Gama karatunsa a binni ya dawo gida gobe insha Allah zai turo a kawo kud'in aure gidanmu." Tana kaiwa Nan tayi wani tsalle sannan ta rugume Sultanah cikin farin ciki da murna tace "Wallahi Sultanah ba k'aramin dad'i nikeji ba burina zai cika Zan auri masoyina Ali kinga shikenan Kullum Sai in dinga yimana duk abinda mukeso nida ke sai kirik'a wanka da kwalliya a gidana ko." Wani irin sanyi jikin Sultanah yayi jin zata rabu da Aminiyarta ta Mai share mata kuka wajenta kad'an take samun sassauci gashi zata Yi Mata nisa yazatayi Amma Dan kartaga yanayi ta ya canza cikin sauri ta maze Dan Kar ta d'aga Mata hankali tasan idan har ta nuna tashin hankalinta duk yadda Mairo takeson auren masoyinta zata iya fasawa saboda ita cikin farin ciki da nishad'i tace "Wayyo Allah dad'i Amma kuwa nayi Miki murna kinji dad'i da nikeji Nima tab'a yin babbar k'awa domin kisan banta ba Yi ba." Tuni ita ta rugumeta Nan suka ta murna a titi sannan Mairo taja hannun Sultanah sukayi gidansu Dan cin d'umamen tuwo da Inno tayi musu suna tafe suna Hira da tsara yadda yanayin bikin zai kassace domin Ali d'an makaranta ne yaje birni ya waye duk k'auyen ba d'an boko irin sa.
Su jima gidan su Mairo suna Hira sannan Inno tayi musu nasiha sosai mussama Sultanah tace ta cigaba da hak'uri da halin rayuwar da take ciki wata Rana sai labari insha Allah sai anyi alfahari da ita sosai taji dad'i nasihar da Inno tayi Mata tuni taji fargabar da take ciki kaso hamsin cikin d'ari ya ragu daga zuciyarta ganin Rana tayi sosai yasa tayi ma Inno sallama sannan ta tafi gida Mairo tayi Mata rakiya inda tasaba rakata domin batason zuwa gidansu saboda da bala'in Iyah.
Cikin farin ciki ta Shiga gidan da sallamarta Amma ba Wanda ya ansa Mata Iyah na k'ofar d'aki da 'yan majalissar ta suna ta Hira da gulmace gulmace mutane sunajinta sukayi banza da ita domin duk gidan suk'i jininta ko kad'an Basu k'aunarta.
K'ofar d'akin Iyah tayi inda suke zaune duk'awa tayi sannan cikin ladabi da mik'awa Iyah kud'in wani mugun kallo ta wurga Mata sannan ta anshi kud'in kirgawa tayi taga d'ari shida cikin mugun zafi da bala'i dake cinta ta d'ago ta dubi Sultanah sannan tace "Ni Jummai na Shiga Uku wannan yarinya kasheni kike so kiyi kullum na d'ora Miki talla sai ki wulak'anta min Kaya ki banzatar min da su Kuma idan nayi magana ance min na takura Miki na tsaneki ansa Ido Dan bani na haifeki ba yanzu da Allah karime dubamin Nan kokon yafi na dubu d'aya Amma d'ari shida kawai ta kawomin."
YOU ARE READING
HASKE A DUHU
Hành độngIta Duniya juyi juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar wahainiya k'addara na fad'awa mutum Mai kyau ko akasin haka, sai dai anason fatan samu cin jarabawar da ubanjiki yayi maka. Rayuwa ta na tafiya k'an tafark'in k'addara tun bansan miye duniya ke...