10

408 16 0
                                    

_*HASKE A DUHU*_

      _*Book one*_


_*DAGA ALK'ALAMI*_
          _*Aisha M Mahmud*_
        _Meeesherh lurv_

_*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_


*Page 10*

_*ABUJA*_

Cikin sauri ta k'arasa parlourn tana sababi duk ganin su tayi sun hallara suna cin abinci cikin sassarfa ta nufi wajen dinning d'in kallon Abba tayi sannan tace "Lalle Usman kenan ni yunwa ta kashe Ni ko? Duk kun had'u wajen cin abinci Amma Babu shegen da ya tuna dani balle ya kirani in Banda Allah ya fito Dani da Haka yunwa zatayi ta cina daga k'arshe Kuma cikin baccin danike Ubangiji ya d'au Raina Kai Amma kedai Kaltume akwai Yar iska." Shiru kowa yayi ba Wanda ya tanka Kaltume tuni bak'in ciki ya kamata domin duk duniya yanzu Hajjah ce kawai matsalarta Amma yazatayi maganinta domin duk abinda tayi taga tana fitowa tana fara bala'i Abba ya tsorota kenan har yanzu Yana shakkar uwarsu Bari ajima zata je wajen dodonta duk zai Yi Mata maganin komai saurin shanye baccin ranta tayi sannan ta kalli Safnah tace "Ashe bakije kin kirata ba danace ki Kirasu ita da sultan? Dan Allah Hajjah kiyi hak'uri Wallahi Safnah na tura ta kiraki bansa bataje ba insha Allah Haka bazai sake faruwa ba" Amma cikin zuciyarta in Banda tsinuwa ba abinda take aika Mata.

Turo Baki Safnah tayi sannan tace "Nifa Mom banji ba kawai ji nayi kince na Kira Sultan" wani mugun kallo ta watsa musu ita da uwartata sannan ta mere Baki tace "Hmmm munafukai banza da wofi yoni duk cikin ku Naga d'an iskan da zaiyimin kissa duk nasan salon ku yaza'ayi kiji ance Ni kina zumud'i kije kiga jikana to Wallahi kwalelenki munafuka." Saurin yin magana Abba yayi domin yasan Halin Hajjah duk abinda tayi niyar fad'a ba Wanda ya Isa ya hanata fad'a shiyasa yace "Hajjah Dan Allah kizo ki zauna kice nasan munyi k'uskure Amma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba kiji." Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace "Shikenan naji na hak'ura Amma Kar a sake kaji ko" cikin sauri Abba yace "insha Allah Hajjah ta" dariya tayi sannan ta tsaya tana kallon yadda suke zaune ganin tayi Safnah tana kusa da Sultan zaune sai wani k'ara matsawa take kusa da shi gashi tunda suka fara magana yanaji Amma yayi banza dasu yayi kunnen Uwar shegu da ita kamar ba ya wajen.....

Murmusawa ta d'an Yi sannan tace zanyi maganinka d'an banza nida Kai ne kafin ta Sami zarafin magana taji Abba na cewa "Hajjah Dan Allah ki zauna ko har yanzu Baki huce ba."

"Uhm kaidai Bari d'annan tuni na huce kawai Ina tunanin inda Zan zauna yauwa nama samu ke tashi ki koma kusa da uwarki kibani wajen na zauna Nima naji d'imin jikina."

Wani mugun abun taji ya tok'areta jin abinda Hajjah ta fad'a ji tayi kamar ta d'auketa da Mari Amma ba halin hakan.

Jin tayi shiru Hajjah tace "Yoni wannan kallon da kike min kamar Zaki rufeni da duka ko baza ki tashi bane."

Cikin sauri Mom ta tari numfashinta tace "Wai Safnah bakiji anayi Miki magana baza ki tashi ba kinsanni fa Sarai bansan ta Ido ki tashi."

Sannan ta dubi Hajjah tace "d'an Allah Hajjah kiyi hak'uri hakan baza ta sake faruwa ba kinji."

Lokacin da Mom kewa Hajjah magana Safnah ta mik'e tana gunguni Hajjah tazo ta zauna tana fad'in "Hmmm kunji da shi duk wani salon munafuncinku nasani Dan Haka ba wani tasiri zaiyi ba wajena a canza shek'e zama Kuma kusa da jikana ba ubanda ya Isa ya hanani ehe."

Duk abinda suke ya jinsu yak'i magana sai yanzu ya d'ago ya kalli Hajjah sannan yace "Hajjah Wai miye Haka kikeyi tunda Kika fito kin ishi mutane da jaraba da fad'a."

Cikin sauri ta tari numfashin shi sannan tace "rufemin Baki tsohon d'an iska nayi masifar duk abinda Nike da Ubanka saboda da Kai Nike gata nikeyi ma Amma kak'i ka fahimta banso ko kad'an a cutar min da Kai Amma Kai gani kake na takura ma cutarka akeso ayi."

HASKE A DUHUWhere stories live. Discover now