_*HASKE A DUHU*_
_*Book one*_
_*DAGA ALK'ALAMI*_
_*Aisha M Mahmud*_
_meeesherh lurv__*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_
*Page 7*
_*K'AUYEN KALGO*_
Lok'aci k'ank'ane soyayyah Mai k'arfi ta Shiga tsakanin Sultanah da Nura duk da ba wani mugun so take Yi Masa Dan ita har yanzu batasan Mai take ji game dashi ba.
Duk had'uwar da suke Bata Bari su had'u gidansu duk ranar da zaizo to k'ofar gidan Mairo suke had'uwa har wajen siyar da abincinta take zuwa kiranta Nan zasu had'u.
Wata shak'uwa ce ta Shiga tsakaninsu Wanda Bata tab'a tunanin Haka zai faru tsakaninta da wani ba shi kanshi Nura tausayinta yafi yawa a cikin zuciyarshi tausayinta yafi k'aunarta yawa.
Duk lokacin da zaizo ko abinci Bai k'areba shike siye abinci Nan zasu dawo k'ofar gidansu Mairo su zauna tare da Ali da shi ganin kwai jahilci sosai Kan Sultanah ko kad'an baza ka had'asu da Mairo ba saboda Mairo tana zuwa makarantar Allo tasan wasu abubuwa sabanin Sultanah da batasan komai a ciki ba bangaren addininta.
Cikin hikima da dubara yake koyar dasu ita da Mairo harda na boko ya had'a masu da yake suna buk'atar ilimin bokon saboda garin nasu babu makarantar boko sai makwabtan garin nasu wasu daga cikin garin suna Shiga makwbtan garin nasu tuni suka fara sanin abubuwa sosai takejin dad'in kasancewar ta da Nura Dan ya haskaka rayuwarta sosai.
Da Kansa yaje shagon d'an ladi ya bashi kud'i yace ya ya d'inga Bata Omo da sabulu Dan ta dinga wanki sannan ya siyamata sabon tak'almin dank'o Dan shine Wanda zai jima Mata sosai taji dad'i ba kad'an ba.
Amma Kuma da suka rabu hankalinta ya tashi da tunanin ya zataje gida shi ganin yadda hankalinta ya tashi yasa Mairo ta ansa tace "Sultanah maza kije gida Ni nasan yadda zanyi Iyah ta barki kiyi amfani da takalmin kinji." Shiru tayi kamar bazata yarda ba Amma Haka ta tafi cikin da tsoron abinda mairon zatayi Haka ta Shiga gidan da sallamarta.
Amma su Kuluwa na k'ofar d'akin Iyah ita da Iyah suna cin tsire da saurayinta ya kawo Mata sukayi shiru Sultanah ta Saba da Haka shiyasa kawai ta share.
Wajen Iyah ta nufa ta mik'a Mata kud'in goro da gyad'ar da ta fita da su da yamma Nura ya siyar ya rabawa tsaffin daddalin da majalissar su ke wajen, Amma da ba Dan Nura ba yau tasan da ta daku.
Kud'i ta ansa ciki da masifa Dan ganin take kamar Sultanah idon ta zuba musu ciki da zalama yasa cikin bala'i tace "To mayya kin zura min wannan k'wala k'walan idanun naki to Wallahi kurwata tafi k'arfinki Kuma wannan abinda da kike gani sai dai ki had'iye mugun yawu domin bacinshi zakiyi ba Dan ke sai gani da Ido gid'awa da Kai Wallahi ko Zaki mutu baza ki ci ba maza ki tashi ki bani waje ga sauran tuwon da Ilah yaci ki d'auka ki ci domin bazan Yi asara ba."
Tashi tayi tana girgiza Kai sannan ta wuce inda ta nuna Mata ita ko kad'an ma Bata d'ora ranta Kan k'ayan iya da Kuluwa saboda ko tana so ita tasan sauran ba Mai Bata "Allah k'yauta" abinda ta fad'a kenan fakar idon Iyah tayi ta waje tayi d'akin Baba ta tafi domin duba jikinsa kwana biyu Yana kwance bayajin dad'i.
Tana Shiga kwance ta Tara da shi Yana ta lumfashi dagani Yana jin jiki ba kad'an ba sannu ta fara yimasa sannan tace "Baba Dan Allah ka tashi ka d'an ci wani Abu nasan tun Karin safe ba abinda kasa cikin cikinka."
Cikin zafin ciwo yace "Sultanah kiyi hak'uri ki k'yaleni banajin dad'i sosai Wallahi bazan iya cin abincin Nan ba cikin Nan ya matsamin sosai da sosai."
Jin Haka da sauri ta fad'a cikin gida lek'awa ta farayi ganin ba kowa duk sun shige d'aki yasa tayi saurin Shiga sannan tayi inda kwanukan iya suke ta d'auki k'ofi a hankali sannan ta d'an d'ebi ruwa ciki d'an abinda ta koya wajen Nura na addu'a ta tofa Masa cikin ruwan sannan ta tayar dashi zaune duk da da k'yar ta d'agashi saboda ba wani girma take da shi ba kusan girman 'yan matan k'auye duka Bata shekara 14 ba kawai huruwa ce da aiki yasa take da juriya domin tun tana k'arama ta Saba da wahalar wajen Iyah tun Bata Iya ba har tazo ta Iyah tana d'agashi ta jinginashi da jikin bangon d'akin ruwan addu'ar ta bashi yasha da k'yar jiginar da shi tayi tana tayi Masa sannu.
YOU ARE READING
HASKE A DUHU
ActionIta Duniya juyi juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar wahainiya k'addara na fad'awa mutum Mai kyau ko akasin haka, sai dai anason fatan samu cin jarabawar da ubanjiki yayi maka. Rayuwa ta na tafiya k'an tafark'in k'addara tun bansan miye duniya ke...