_*HASKE A DUHU*_
_*Book one*_
_*DAGA ALK'ALAMI*_
_*Aisha M Mahmud*_
_meeesherh lurv__*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_
_*Follow me on Wattpad please*_@meeshalurv
*Page 17*
_*K'AUYEN KALGO*_
Biki su nagani na fad'a irin na k'auye komai Mai cike da Al'ada Mairo da kanta ta kuncewa Sultanah kitson kanta da yayi wata muguwar tsufa har ba'a gani tsagar ga d'auda ya d'ank'are sosai, da k'yar ta kunce shi ga gashi nata Mai k'yau da santsi Amma ba gyara shiyasa duk ya wulak'ance, yod'o tasa ta wanke Mata yayi fes da shi yayi k'yau ga tsawo kannata gareshi shiyasa ta k'ara k'yau sai walk'iya yakeyi gidan Mai kitso suka tafi aka yarfa musu k'ananan kitson....
Wanda yayi k'yau sosai tuni Sultanah ta fito da cas da ita fuskarta ta fito tayi k'yau sosai k'yauta ya fito, ga ta sa d'aya daga cikin k'ayan da aka d'inka Mata harda sabon gyale da silifas d'inta Mai d'ango tasa Tasha kwalliyarta irin ta k'auye da d'ige-digenta sosai take farin ciki dajin dad'i ganin yau gashi ta fito cas da ita, ga kunshi Tasha yadda kasan ita ce amaryar sai washe Baki take abin ba sabonba,
Sosai suka Sha shagalin biki da da al'adunsu na mutane k'auye lokacin bikin, gad'a kuwa sun shata sosai ranar talata aka d'aura auren Mairo da angonta Ali tuni jikin Mairo da Sultanah yayi sanyi ganin zasu rabu saboda irin shak'uwar da sukayi yau gashi Aure zai rabasu duk wuni ranar suku-suku suke yawo, lokacin kuwa da sukajiyo wak'ar d'aukar amarya tuni suka fashe da kuka suka ruk'unk'ume juna suna wani irin kuka na tashi hankali, tuni suka ba kowa tausayi saboda duk sun San hands suka shak'u da juna Kuma suke k'aunar junansu Dole suyi kuka dak'yar aka lallashesu tayi shiru suka tafi gidan amarya....Tunda aka fara bikin ganin yadda Iyah ta share da ita ita abin dad'i yayi Mata, saboda tasamu sake tuni ta mance da gidan Dan tunda aka fara bikin ta koma gidan su Mairo da kwana ganin Iyah ta share Bata nemeta ba yasa tayi kwanciyarta tak'i ta koma gidan tace sai baya biki duk abinda zatayi Mata dai ai sun Gama bikin....
Su Kuluwa kuwa da suka zo wajen bikin ita da Altine da Jamile wani mugun bak'in ciki sukaji ya rufe su ganin yadda Sultanah ta fito tayi k'yau duk tafi su sharp da k'yau tare da shigarta ma tafi tasu k'yau ji tayi Ina wuta su saka ta saboda Hassada da bak'in ciki sosai suka fita da abin waje suka ta watsa Mata magana tanajinsu Amma ta k'yalesu......
Koda suka koma gida Kuluwa Nan ta fad'awa Iyah k'arya da gaskiya Wai Sultanah Dan taganta da sabon d'inki shine harda zagin su harda kuka sannan tace idan ta dawo gida duk kayan su amshe min su domin Dani ya dace ba da ita ba...
Kwantar Mata da hankali tayi tare da Alk'awarin idan ta dawo zata anshe Mata su, tayi hak'uri...
Tunawa tayi da hud'ubar Asabe akan Sultanah tare da na boka shiru tayi batason bacin Rai Kuluwa gashi tana son kud'i Dole Kuluwa tayi hak'uri tunda idan aka samu kud'in ita kuluwar zai amfana shiyasa tasa a ranta idan ta dawo baza ta ansar Mata ba zata ba Kuluwa hak'uri dayi Mata albishir d'in abinda take k'ullawa Akan Sultanah tasan da tasani Dole tayi murna tabar zance kayan.......
Yanzu Nura ya zama rak'umi da akala sai yadda sukayi dashi komai ya Samo to kan Kuluwa yake k'arewa da Iyah Kuma duk iskancin da takeyi Bata fasa ba ita da jabiru shiko kullum jabiru cikin kawo su kud'i da nama saboda ubanshi Yana da Hali cikin k'auye shine Mai gari, Kuma ba Wanda ya Isa ya tari Nura ya fad'a Masa ya yarda ranar sai kaci uwarka wajen shi....
Kwana biyu sukayi gidan amarya kamar yadda al'adar k'auyen ke faruwa idan aka Kai amarya k'awayen amarya zasuyi kwana biyu, suyi kwana d'aga Basu bacci sai Hira da zance aure cikin Wanda suka kusa son aure ranar da suka cika kwana na biyu akazo akayi Mata gyara da komai sai dare suka shirya zasu tafi sun Sha kuka sosai Sultanah da Mairo kin sakin Sultanah Mairo tayi sai da k'yar sai da tayi Mata alk'awarin gobe zata dawo gidan sannan Ali da k'yar yajanye Mairo daga jikin Sultanah yayi d'aki da ita sannan Sultanah ta samu damar tafiya cikin kuka dajin zafin rabuwa da Aminiyarta ga tunanin zuciya gidan....
YOU ARE READING
HASKE A DUHU
ActionIta Duniya juyi juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar wahainiya k'addara na fad'awa mutum Mai kyau ko akasin haka, sai dai anason fatan samu cin jarabawar da ubanjiki yayi maka. Rayuwa ta na tafiya k'an tafark'in k'addara tun bansan miye duniya ke...