11

369 17 0
                                    

_*HASKE A DUHU*_

     _*Book one*_

_*DAGA ALK'ALAMI*_
        _*Aisha M Mahmud*_
           _Meeesherh lurv_


_*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_


_*Tofa masoyan HASKE A DUHU free page ya k'usa k'arewa duk Mai buk'atar siya yayi magana idan duka shida kake so idan daya ko biyu ko uku ko hud'u kukeso sai ku tuntub'i wannan number 07067364721 sai najiku masoyana a duk inda kuke*_

*Page 11*

_*K'AUYEN KALGO*_

Cikin kwana uku jikin Sultanah yayi sauk'i sosai har lokacin iya Bata ce Mata komai ba zata Shiga gidan tayi duk abinda take buk'ata ta dawo d'akin Baba sannan Mairo ke zuwa ta kawo Mata abinci safe rana dare say biyu a boye Nura da Ali suka zo duba ta tare da Yi Mata Yan siyayya Yan kayan kwalama na birni Dan k'auyen su Nura yafi na Sultanah birni sosai sosai baba ya yaba da nutsuwar Nura tare da halaiyarsa yayi na'am dashi sannan yayi Masa alk'awari indai bashi yace ba yaso ba to ya bashi Sultanah halak malak ba k'aramin dad'i Sultanah taji ba dajin batun Baba shiyasa yanzu ya fara zuwa k'ofar gidan su Sha firarsu gashi yanzu ko aiki zata d'auka zatayi Iyah hanata takeyi tuni taba banza ajiyarta wannan Kuma ba hud'ubar kowa bane sai ta k'awarta Asabe saboda idan sun tashin yin kullin Kar agane sune shiyasa tace ko tallah ta daina dora Mata ganin yanxu Bata zuwa k'o'ina yasa Nura yasa su Shiga makarantar Allo ko sun k'ara sanin addininsu bak'aramin dad'i Sultanah taji Dan ba k'aramin son karatu addini Dana boko saidai Iyah ta hanata Amma yanzu ga dama ta samu tafiya sukeyi ita da Aminiyarta Mairo suje da safe sannan suje da yamma dinki Nura yayi Mata kala uku na atamfa roba tare da hijab d'aya sai takalmin d'ango da kayan kwalliya Hoda fankeke da Jan Baki Kan tawaye sai gazar da Mai shafawa Mai gurguwa ba k'aramin dad'i Sultanah taji ba ganin kayan Mairo ma taji dad'i Dan yanzu Sultanah zata fara fitowa gari cikin gida tazo ta nunawa Baba sawa yayi ta Kira Nura yayi Masa godiya sannan yace duk sanda ya shirya ya turo domin yasan zai iya rik'e Masa Sultanah da mutunci hankalin shi Kuma zaifi kwanciya idan yaga ya aurar da ita shikenan matsalarshi ta Kau, cikin jin kunya ya ansa sannan yayi Masa sallama ya fita Yana Yaba kirkin Baban.....

Ganin kayan kwalliyar da d'inki da akayi Mata da sauran siyayyar da yayi Mata tuni Kuluwa ta d'aga hankalinta, ta tusa iya gaba da kuka itafa tasan yadda zatayi ta sa Nura ya dawo wajenta domin duk k'auyen Nan ba Wanda yake da saurayi irin na Sultanah, sannan gashi d'an birni Dan k'auye su kuwa duk k'auyen Nan ba Wanda yayi karatun boko sai Ali kad'ai duk mazan garin ba Wanda yayi daga kiwo sai noma gashi da k'yau kuka take wiwi kamar zata mutu, tuni hankalin Iyah yak'ara tashi ita kanta bak'in cikine fal zuciyarta....

Gashi Asabe tace Kar tayi magana komai zata gani idan tana son aikinsu ya tafi yadda suke so, ita kuwa ta fara gajiya d'an ba k'aramin d'aureya takeyi ba akan hakan....

Sai taji kamar ta kama Sultanah tayi ta dukanta Amma ba halin tana tsoron kwabarta tayi ruwa shiyasa take d'aurewa, Amma fa abin yayi yawa Dan tayi mugun samu sake ita da ubanta sai abinda suka ga dama sukeyi tofa abin yazo k'arshe Dole yau duk abinda ake ciki ta tafi gidan Asabe idon gari yau su tafi inda za'a kawo musu k'arshen matsalar tayi maganin Sultanah da ubanta sai sunyi da nasanin duk abinda suka aikata Mata domin gani take kamar da gayya sukeyi.....

Cikin kwantar da murya ta fara lallashinta da k'yar da ban Baki ta shawo kanta tare da Yi Mata alk'awarin zuwa gidan Asabe yau su tafi gidan bokansu Dan anyi maganin Sultanah......

Ganin hankalin ta ya kwanta yasa cikin sauri ta zari gyalenta Wanda yaji duniya ta tafi gidan Asabe domin aikata aika aikarsu akan Sultanah.......

Ko sallama Babu ta fad'a gidan Asabe "Asabe! Asabe! Kina inane fito yau muyi ta tak'are Wallahi nagaji da wannan shawarar da Kika bani zuciyata tana gab da bugawa."

HASKE A DUHUWhere stories live. Discover now