_*HASKE A DUHU*_
_*Book one*_
_*DAGA ALK'ALAMI*_
_*Aisha M Mahmud*_
_Meeesherh lurv__*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*_
_*Follow me on Wattpad please*_@meeshalurv
*Page 19*
_*K'AUYEN KALGO*_
Bak'aramin tashin hankali Iyah ta Shiga ba ganin shikar ciki wajen Kuluwa kuka kuwa ta Sha shi gashi Bata so ta d'aga hankalinta kada mutane gidan su fahimci halin da ake ciki Dole sai a cikin d'aki take d'aga hankalinta gudu kada a fahimceni halin da suke ciki.
Kuluwa ma fa tashiga tashin hankali tare da fargaba lokacin da Iyah ta fahimtar da ita shigar cikin dake jikinta sai a lokacin ta fahimci watan ta biyu rabon da taga al'adarta ganin dama sau d'aya ta tab'a Yi shiyasa Bata d'aga hankalinta ba Ashe masifa ce d'an k'are a jikinta....
Gaza d'aurewa Iyah tayi ta k'ira Kuluwa gefe d'aya cikin tashin hankali take tambayar ta ubanda yayi Mata ciki cikin kuka Kuluwa ta fara fad'a Mata abinda ya faru....
"Dama Iyah jabiru ne shike bani kud'i tare da nama idan yagama yin amfanin da ni kullum sai mu had'u Wallahi shi kad'ai muke tarayya da shi Kuma shi yayi cikin Nan tunda bani kula kowa sai shi."
Tana Gama fad'a ta fashe da wani irin kuka itama Iyah kukan tasa da Jin tashin hankali cikin zuciyarta yazatayi da ranta gashi d'an masu gari ne Kai bama zata tab'a yarda wannan maganar ta fito idan har ta Bari ta fito ba Mai iya aureta cikin garin har shi jabiru tana da masaniyar yaran da ya lalata da yawa cikin k'auyen Nan idan sukai k'ara yace k'arya ne ubanshi ya d'aure Masa gindin sai abinda ya ga dama yakeyi.....
Gargad'i tayiwa Kuluwa tace tayi shiru karta Bari wani yaji wannan zance domin Wallahi ita zata Shiga tashin hankali ko Sultanah Kar ta fad'awa gyalenta ta Zara sai gidan Asabe...
Yau sallama ma batayi ba ta fad'a gidan d'akin ta fad'a cikin tashin hankali ta fasa kuka da bala'i Asabe ta d'ago tayi Mata ganin ta shigo gidan nata ta firgitata sai kawai ganinta tayi Amma ganin Jummai na kuka yasa hankalinta ya tashi cikin tsantsan tsoron tayo kanta ta rik'o hannuta zaunar da ita tayi tsakar d'akin tace.
"Kiyi hak'uri Dan Allah kidaina kuka duk da bansa miyafaru dake ba kiyi hak'uri ki fad'a miyafaru Dan musan inda gizo ke sak'ar ba Wai kizo kinayi min kuka ba alhali nikuma bansan Mike faruwa ba."
Gefen gyalenta tasa ta face hancita tare da goge ruwan hawayen da ya zubo sannan tace "Asabe ya zanyi da Rai na wannan yarinya ta janyo min masifa Kuluwa ta cuceni ki duba kiga sai da biki ya taho shine zata janyo min abin kunya cikin garin Nan Wai ta d'aukomin cikin" wani kukan ta kara saki sannan tace "Yanzu Asabe yazanyi idan wannan yaron ya gane Kuluwa na da cikin mutanen gari suka gane yazanyi."
Kame Baki Asabe tayi itama ta tsorata tajin abinda ya faru tuna wata shawara tayi yin saurin cewa tayi "kwantar da hankalinki Iyah na samu mafita yanzu abinda zai faru duk yadda za'ayi ace Nura cikin satinnan ya fito ayi auren Kuma gobe mu Kuma wajen boka ya kwantar da cikin tare da rufe bakin duk Wanda zai gane yayi magana Haka kawai zamuyi mu rufe bakin kowane d'an iska kin kwantar da hankalinki baza mu tab'a kunyata ba."
Tuni taji hankalinta ya kwanta ba k'aramin jin dad'i shawarar tayi ba tana sosai godiya tayi Mata tare da Alk'awarin zata zo d'in gobe da safe su tafi Amma Dan Allah ta rik'e Mata Amana..
Bata Rai Asabe tayi saboda Jin abinda Iyah ta fad'a Nan ta fara fad'a ita da ita alk'awari ne ta tab'a Jin abinda duk suke aikatawa ya fito...
Ganin ranta ya baci yasa ta Bata hak'uri da k'yar ta hak'ura tayi shiru sannan ta tafi gida duk abinda suka shawarta shi ta fad'awa Kuluwa idan Nura ya Zo ta fad'a Masa ayi bikin cikin satin taji dad'in abin da Iyah ta yanke domin dama itama Bata so asirinta ya tonu ko a fahimci halin da take ciki....
Nura na zuwa ta fito Bata Rai tayi hankalinsa ya tashi duk ya rud'e Yana tambayarta abinda ke faruwa cikin cin magani da hura hanci ta fara yi Masa magana...
"Idan har k'aunar da kake min gaskiya ce inason cikin satinnan a d'aura Mana aure saboda nagaji da Jin zance da ake a gari Wai ba aure zakayi ba yaudarata zakayi shiyasa aka saka bikin da yawa."
Tuni ya rud'e jin abinda take fad'a cikin tashin hankali yace "Ki fad'amin duk ubanda ya fad'i zance Nan yau zanyi maganinsa Kuma Ni Nura Zan nunawa duk Yan k'auye Nan son da Nike Miki son gaskiya ne Zan aureki cikin satinnan nayi alk'awari."
"Nifa bawai ka cika min ciki ba da surutu da tambayar wa ya fad'amin ba kawai ka aikata abinda nace idan na gani kayimin magana Karka Kara zuwa wajena idan har bakayi abinda nace."
Tana Gama fad'a ta shige cikin gida ta barshi tsaye Nan cikin tashin hankali da cizon yatsa tafiya yayi gida da kud'irin cikin kwana biyu Nan za'a daura musu aure da ita saboda ba k'aramin tashin hankali ya Shiga ba ganin yadda Kuluwa ta juya mishi baya tuni...
Tana shiga gidan cikin farin ciki ta fad'awa Iyah yadda sukayi da yadda hankalinsa ya tashi bak'aramin murna Iyah tayi ba duk abinda suke Sultanah tana jinsu ta Kuma sani saboda zata Shiga d'aki taji Iyah tana fad'a wa Kuluwa kada ta Bari ko ita taji tana da ciki hankalinta ya tashi tanajin haka ta koma d'akin Baba da kwana sai idan safiya tayi ta dawo tayi kuka kamar ba gobe ta d'aga hankalinta ganin halin da Yar uwarta ta Shiga bak'adan ba...
Cikin kwana biyu taga shirye shiryen ya tashi cikin gidan nasu domin har ankawo kayan auren Kuluwa da komai na al'adar bikin irin ta tadar k'auye tuni gidan Iyah ya fara ciki da Yan biki domin bikin Kuluwa fa ya tashi Nura ya d'aga hankalinsa sai a d'aura Masa aure da Kuluwa tuni innarshi taji tsanar Kuluwa da kud'iri Mai yawa a tare da ita yadda ta mallake Mata d'a ta d'au alwashin sai taga bayan wannan auren sannan sai ta hana Kuluwa zaman lafiya shiyasa tace cikin gida d'aya zasu zauna....
Kuluwa hidima ta kankama domin washegari d'aurin aure kowa sai mamakin auren yake yadda akayi saurin matso sa kamar Wanda ake gudun wani Abu tuni Asabe da Iyah suka rufe bakin kowa sannan ta kwantar da cikin dake jikin kuluwar sai tayi wata biyu zasu koma a tayar da shi yadda ba Wanda zai gane....
Duk wani shagali sunyi shi su Jamile da Altine sune Yan hidima ita kuwa Sultanah gidan Mairo take tafiyarta ganin yadda suke hantararta yasa ta daina Shiga cikin su Nan tayi tafiyarta gidan Mairo ta wanke Mata kanta ta yarfa Mata kitso tare da kunshi sosai tayi k'yau abinta....
Ranar juma'a aka d'aura auren Kuluwa da Nura Kuma ranar aka Kai amarya gidan angonta Iyah sai tink'aho take 'yarta tayi aure ta samu mijin k'ere sa'a sai shewa take ita da k'awayenta cikin d'akin cikin daren da akai Kuluwa suna d'aki zaune Asabe ta janyo Iyah waje Dan sunyi magana Bata son kowa yaji Bayan Rumbun gidan sukayi inda Asabe take fad'awa Iyah ta had'a kayan Sultanah ranar litinin za ta tafi Abuja kuma tare da ita zasu tafi Bata kowa yaji dad'i taji sosai jin tafiya ta matso tuni ta fara jin har ta hangonta cikin garin makka Mai albarka ta zama Hajiya Iyah wata dariya tayi tare da Alk'awarin zata had'a kayan nata saurin dawowa sukayi gudun Kar a fahimcesu....
_*Manage pls*_
_*Wallahi banji dad'i yau zazzabi nakeji d'aurewa kawai nayi nayi muku typing Dan karkujini shiru kuyimin uxuri pls*_
_*Sauran shafi d'aya insha Allah book one ya k'are ku hanzarta Dan siyen naku domin jin yadda fitattu shida zasu kasance karku Bari abaku labari kuyi k'ok'arin mallakar naku.*_
_*FITATTU 6 NA SIYARWA NE, IDAN KUNA BUK'ATAR D'AYA DAGA CIKI, KO KUMA DUKKANINSU, KU TUNTUB'EMU TA WANNA LAYIN:,07067364721*_
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abudul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA DAYA*
Asisi B Aliyu
YOU ARE READING
HASKE A DUHU
ActionIta Duniya juyi juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar wahainiya k'addara na fad'awa mutum Mai kyau ko akasin haka, sai dai anason fatan samu cin jarabawar da ubanjiki yayi maka. Rayuwa ta na tafiya k'an tafark'in k'addara tun bansan miye duniya ke...